← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 120

Sashe 109

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin katse shi Zaiyan ya yi ya ce "Doctor cikin da ke jikinta fa?"

Saurin kallon shi Abdul ya yi baki buɗe har zai yi magana sai kuma ya fasa, Hashim ya yi murmushi ya ce "Ka kwantar da hankalinka cikin yana nan bai fita ba, amma dai kaɗan ya rage ya salwanta saboda an daki cikin nata ne, dan kune ma ya sa na yi shuru ban sanar da 'yan sanda ba saboda na ga kuna da babban ɗan sanda a gida, yanzu dai nan da kwana uku za a iya sallamar ku, ga wannan ku amsa a sayo magani shi za a ba ta gobe da jibi dan ta warware. " Ya miƙa musu takardar Abdul ya amsa ya miƙa wa Zaiyan tare da ciro kuɗi ya ba shi, kallon kuɗin ya yi Abdul ya girgiza kai ya ce "Ka amsa ka sayo maganin."

Miƙewa ya yi ba tare da ya amshi kuɗin ba ya juya ya wuce, har ya je bakin kofa ya juye ya ce "Ka yi hakuri ba sai na amshi kuɗinka ba, ina da kuɗi a jikina zan je na sayo da shi." Yana gama faɗin haka ya buɗe ƙofar ya fita.

Da kallo suka bi shi sai da suka ji ya rufe ƙofar sannan Doctor Hashim ya yi gyaran murya ya ce "Wai wannan ba Zaiyan ba ne? Sannan kuma ba shi ba ne ka ce min an aura wa Baby?"

Jinjina kai Abdul ya yi yana murmushi ya ce "Shi ne fa ai ya warke ras dan yau ma suka diro garin É—azun nan."

Murna ya taya su yana faɗin "Ikon Allah! Ga shi kuma har da tsarabar Baby ta zo muku da shi dan ma ku ƙara tabbatar da cewa ya samu lafiya."

Hira suka ɗan taɓa sannan Abdul ya fito, a hanya suka haɗu da Zaiyan yana miƙa wa norse maganin da ya sayo yana tambayarta zai iya ganin matar tasa kuwa? Nan take sanar da shi za su iya shiga amma ban da hayaniya sosai. A tare suka wuce inda suka sanar da su Ammi ai ciki ne a jikin Abir Allah ya sa bai ɓare ba, sosai suka yi murna da jin wannan daddaɗan labarin suka shiga ɗaya bayan ɗaya suna duba ta, ita kuma tana kwance tana baccin wahala...

Sai Yamma lis duk suka koma gida Ammi ta ce za ta tsaya ta kula da ita, amma Zaiyan ya ce kar su damu zai kula da ita su tafi da safe sai su zo, ganin ya nace sai Ammi ta hakura tana faÉ—in "Kai jama'a yaran zamani gabaÉ—aya ba ku kunya."

Murmushi ya yi yana shafa kwantaccan sajansa wanda ya ƙara ƙawata fuskar, su kuma suka tafi amma Abdul duk ya kasa nutsuwa gani yake kamar da sun tafi za su kuma guduwa, ganin hakan ya sa Zaiyan yin wani kalar murmushi ya shige ɗakin...

Misalin karfe 1:am na dare yana akan dadduma ya kai sujjada yana ta kwararo wa matarsa Addu'ar samun lafiya da addu'ar Allah ya haɗa shi da mamansa, sai da ya gama sannan ya shafa fatiha ya ɗago ya kallo gefen gadon da take kwance. Idanu ya zuba mata ganin tana ƙoƙarin farkawa, ya tashi da hanzari ya isa bakin ya hau ya ɗago da ita ya rungume tare da shafa bayanta yana jero mata sannu, a hankali ta buɗe idanuwanta ta gan ta a Asibiti nan abin da ya faru ya dawo mata tiryan-tiryan, hannu ta sa ta goge hawaye da suka zubo mata ta ɗago daga jikinsa suka zuba wa juna idanu..

Hannu ya kai ya goge mata hawayen yana girgiza mata kai ya ce "Baby ki yi shuru kin ji Allah ya ba ki lafiya, in sha Allah sai na bi miki haƙƙinki." Ya faɗa yana shafa gashinta mai santsi.

Hannu ta É—aura akan cikin ta sa masa kuka marar sauti ya yi saurin kwato da ita jikinsa yana rarrashin ta, da kyar ya shayo kanta ta daina kukan tana daga jikinsa ta ce "Nury yanzu shi kenan Umma ta yi sanadin zubewar cikina? Na kwallafa rai akan cikin nan me ya sa Umma ta tsane ni har haka?"

"Babynmu yana nan maƙale a mararki bai fita ba, in sha Allah kuma sai kin haifa min shi mu ga girmansa."

Saurin kallon shi ta yi ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa, hamdala ta yi ta raba jikinta da nasa ta koma ta kwanta tare da masa nuni da ya kwanta, babu muso ya kwanta ya janyo ta jikinsa kamar wata uwa da É—anta ta dinga shafa kansa tana faÉ—in "Ka yi bacci nasan duk ka gaji."

Murmushi ya sakar mata ya É—ago ya manna mata kiss a kumatu sannan ya koma ya kwanta, ta jima tana kallon shi kafin bacci ya yi awon gaba da shi, ajiyar zuciya ta sauke tana bin shi da kallo har ya É—an rame daga fuska..

Ɗan hasken ɗakin ne ya dauke ta yi shuru tana ƙara rungume Zaiyan, tuna matar nan sai ta kamu da tsananin farin ciki tana jiran ta bayyana. Bayan kamar minti biyar sai ga ta ta bayyana fuskarta dauke da murmushi tare da cewa "Assalam alaikum Hauwa'u."

Itama murmushin ta yi ta ce "Wa alaikum salam Mama, sannu da zuwa."

Matsowa ta yi kusa da gadon ta dubi Zaiyan ta ce "Alhamdu Lillah yarona ya warke, kuma abin daÉ—in ma ya kusa zama Baba."

Sunkuyar da kai Abir ta yi tana wasa da yan yatsunta, sai da ta jima a haka sannan ta kalli Abir ta ce "Yau na zo na cika miki alkawarin da na É—aukar miki tun farkon haduwar mu, yau za ki san waye Zaiyan, su waye iyayensa, duk zan sanar da ke."

Cike da zaƙuwa Abir ta ce "Mama na jima ina jiran wannan ranar ki sanar da ni."

Jinjina kai ta yi sannan ta ce "Dama na sanar da ke ni ba mutum ba ce kamar ke, wannan suffar da kike gani ina baiyanan miki da ita ta wadda ta raini Zaiyan ce."

Saurin katse ta Abir ta yi ta ce "To Mama ina ita wadda ta raine shi take ? Kuma su waye asalin iyayensa?"

"Duk za ki ji su ke dai ki nutsu da kyau."

Jinjina kai Abir ta yi ita kuma ta É—an yi shuru na sakanni sannan ta soma ba ya labarin.

"Asabe ta kasance ƴar aiki ce a gidan wani attajirin mai kuɗi mai suna Alhaji Abdu matarsa kuma Hajiya Husna, tun Husna na amarya Asabe da mijinta wanda yake musu gadi suke zaune a wannan gida suna musu aiki, mijinta Maigadi ita kuma tana musu aikin gida da girki har Allah ya azurta Husna da samun ciki. Haka suka yi ta tattalinsa wannan cikin Alhaji Abdu yana ƙara shagwaɓa Husna duk abin da ta ce tana so shi zai yi mata. Alhaji Abdu ɗan kasuwa ne wanda yake zaune a J. R. A. Unguwar masu kuɗi a Kano, haka suke zaman su lafiya lau dan Husna ta ɗauki Asabe tamkar uwar da ta haife ta. Cikin Husna ya girma dan har ya shiga watan haihuwa Alhaji Abdu ya shirya musu komai na tafiya ƙasar waje ya ce a can za ta haihu, ana ya gobe za su tafi suka fiddo kayan tafiya aka aje a palo duk abin da za su buƙata sun fito da shi, nan kowa ya tafi ya kwanta..

Misalin karfe 2:30pm na dare Alhaji Abdu ya fito palo cikin sauri ya ɗaga wata ƙofa tare da duba agogon da ke tsintsiyar hannun sa ya ga dai lokaci daidai nuna masa biyu da rabi ce ta dare. ƙarar da ya ji ne ya sa shi saurin yin baya yana zaro idanu fuskarsa na nuna tsoron davke cikin zuciyarsa, cikin sanɗa ya koma ta ƙofar da ya fito.

Bai tsaya yin komai ba ya nufi kan gadon tare da faÉ—in, "Husna! Husna!"

A razane Husna ta buɗe idanuwanta jin yadda kiran ya karaɗe majiyarta, ƙaton cikin da ke jikinta ya kasa ba ta damar yin motsi mai kwari. Kamo hannunta ya yi cikin azama ya zaunar da ita yana kallon ƙofar shigowa, ita ɗin ma ƙofar take kallo kuma daidai lokacin jaririn da ke cikinta ya yi wani irin juyawa.

"Inna lillahi! Maigida zan mutu." Ta yi maganar tana ciza lips ɗinta na ƙasa.

Sakin ta ya yi ya kunna hasken É—akin nan-da-nan haske ya gauraye É—akin ya dawo kusa da ita tare da É—ago fuskar ta, Kama ta ya yi ya saukar da ita cikin rawar baki ya ce "Hu..Husna akwai matsala fa."

"Wacce irin matsala Maigida?" Ta yi saurin tarar numfahinsa da tambaya.

"Maza tashi 'yan fashi ne suka shigo mana gida ki bi ƙofar baya ki gudu, kuma komin runtsi ki daure ki tseratar da rayuwarki da abin da yake cikinki ni zan tsaya." Ya faɗa yana saka mata hijabi tare da damƙa mata wata ƙaramar akwati.

Baki ta buɗe da niyar yin kuka ya yi saurin rufe mata bakin cikin azama tare da girgiza mata kai. "Kada ki ɗaga murya Husna ina son ki bar gidan nan yanzun nan, zan ba su duk abin da suke so, idan na rayu zan neme ki ga wayata da taki nan a cikin jakar nan karki damu muje." Ya faɗa tare da kama hannunta ya ja ta suka fito zuwa palo, hakan ya sa suka ji karar buga get ɗin gidan Husna ta yi saurin ƙanƙame mijinta sakamakon ciwon naƙudar da ya taso mata.

Ganin haka ya sa ya dauke ta ya bi ta kitchen ya fitar da ita , saurin sakin ta ya yi murya a raunace ya ce "Don girman Allah Husna ki tafi da na rasaki gara ace nine na mutu, idan kuma kuÉ—i suke so zan ba su duk abin da na mallaka gabaÉ—aya indai ba za su cutar da mu ba."

Fashe wa da kuka ta yi ta ƙara riƙe hannunsa ta ce "A a gaskiya ka zo mu gudu tare ba zan iya tafiya na barka ba, ko ka kira 'yan sanda." Ta yi maganar tana jan hannunsa.
Chapter 109 · 0% Book details