Sashe 28
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune su Alhaji suke su huɗu a cikin wata rumfa irin ta hamshakan masu, kowannen su ya yi shiga ta alfarma sai dariya suke, Jarmai ya cire glass ɗin fuskarsa ya ce "Gaskiya ina yinka Alhaji, komai yana tafiya cikin tsari." Ya faɗa sana tafawa da Alhaji da ya yi shirmama a zaune da uban tumbi sai jin kansa yake na ƙara girma, gyara zama ya yi ya ce "Yo mu ɗin na wasa ne? Yanzu ba mun yi maganin matsalar mu ba mun huta." Ya faɗa yana murmishi.
"Gaskiya ne Alhaji ni in da so samu ne ma, ina so mu san yadda za mu kwashe komai na Alhaji Ibrahim Abdullahi Maitama da Manager." ÆŠayan ya faÉ—a yana sakin murmushi.
"Wow kai amma fa kai kanka yana ja PA, yanzu mu tsara komai ta yadda in mun kai sheda ba za ayi wani kokwanto a kai ba, zan kuma je wajan Nadumbuza ya mana aiki mai ƙarfi. Sannan wannan ajiyar da ke hannun ƴarsa lalle a dage a amso ta daga wajan ta, in ta ta yi gardama a aika ta inda muka aika ubanta." Ya faɗa cike da jin haushin Abir yana hura hanci. Jarmai ya shaƙe da dariya ya ce "Ka kwantar da hankalinka Alhaji ai PA zai ji da komai, ko ka manta muna da masu yi mana aiki a cikin gidan nasu?" Sai a lokacin ya saki fuska ya ce "Haka ne fa kuma, to yanzu mu koma kan maganar ɗaya bayan mu gama sai mu ji da wannan yaran masu taurin kai, shi Ɗansandan nan har wani gani-gani yake yi wa mutane dan yana jin kansa shi wani ne, to in na ga dama sai na ce a tsige shi daga aikin kuma a lalata masa takardunsa sai mu ga ta yadda zai yi jin kan."
Da Sauri Jarmai ya ce "No Alhaji in muka yi haka ai mun ɓata komai, kai dai mu yi abin da muka tsara ka rabu da yaron nan, abin da nake so mu samu a amso wannan ma'adanar bayanan da take wajan su, idan fa muka tsaya muna gani wankin hula zai kaimu dari.."
Da haka dai suka gama tattaunawa kowa na kawo tashi shawarar har suka gama kowa ya nufi inda zai nufa..
Tafiya suka yi mai nisa sosai sun kusa isa wata Unguwar talakawa direba ya tsallaka bakin hanya ya yi packing, da mamaki Abir ta kalle shi ta ce "Ya dai ka tsaya a nan?"
Gyara zaman rigarshi ya yi ya ce "Oga ya ce a sauke ki a nan sai mu ƙarasa da ke a ƙafa."
GyaÉ—a kai ta yi tana sakin murmushi ta buÉ—e ta fito, suma fitowa suka yi sai da suka wawwaiga ko'ina suka ga ba mai kallon su sannan biyu suka shiga gaba, bayan su ta bi wasu biyun suka bi bayan ta. Kowannen su akwai eapis a kunnensa, suna cikin tafiya lokaci É—aya duk suka É—aura hannu a kunne É—aya daga cikin su ya ce "Hello Oga kana kan layi?"
Abdul da ke duba wasu takardu ya gyara zama ya ce "Ku kula da kyau Ali, kar ku bari wani ya ga inda kuke bi."
Ali ya gyara kai cikin girmamawa ya ce "Ok Oga za mu kula."
"OK thank you guys, good bye." Ya katse kiran sakamakon nocking da ake, izinin shigowa ya ba da aka turo ƙofar. Kyakyawar budurwa ce doguwa fara wadda ba ta wuce 27years ba, sanye take da ɗinkin atamfa riga da siket ɗinkin ya matse ta da ƙyar take juyawa a cikin kayan, glass ɗin da ke manne a idanuwanta ta cire tare da ƙarasowa tana wani yauki da yanga ta yi saƙare da jakar hannunta ta ce " Oga can I be?"
Cike da mamaki ya nuna mata kujera ya ce " sit down." Zama ta yi tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana taunar cimgam, nan-da-nan Abdul ya fusata amma ya ɗaure ya danne ɓacin ranta dan ya ji da me ta zo masa, fuska ba annori ya ce "What's going on with you? and who are you?"
Sauke ƙafarta ta yi cikin nuna jan hankali ta yi baya da gashin dokin da ke kanta, surar jikinta ta bayyana gabaɗaya ƙirjinta rabi a waje suke, siket ɗin kan shi an masa wata fataha daga kasa har kusan mazaunanta.
Ƙara ɗaure fuska ya yi ya maimaita mata maganar, sai a sannan ta ce "Ranka ya daɗe ni na jima ina son ka ba tun yau ba, to na gaji ne da cutar kaina na ce bari na zo na faɗa ma abin da ke cikin zuciyata ko zan samu salama. Don Allah Abdul ka taimaka ka so ni ko da rabin wanda nake ma ne." Ta ƙarashe maganar tana yin fuskar tausayi...
Tuni Abdul ya hargitse sakamakon ganin surar jikinta da ya yi, nan-da-nan hankalinsa tashi ainun ya rufe idanunsa yana karanto Addu'o'in neman tsari ga wannan makirar mata, wani irin murɗawa mararshi ta yi ya ƙara runtse idanu yana sauke ajiyar zuciya..
Ita kuwa ganin yanayinsa ya canja ta yi wani shu'umin murmushi ta yi saurin mayar da turaren da ta fesa a ɓoye, gyaran murya ta yi ta ce "Yallabai lafiya dai?"
Idanuwansa a lumshe ya ce "Ki tafi zan yi tunani."
Wani irin daɗi ne ya ziyarce ta kamar ta kurma ihu dan daɗi ta tashi daga inda take ta dawo kusa da kujerar shi ta tsaya tana ƙara kallon shi, shi kuwa tuni ya ji wannan ƙamshin turaren ya ƙara kusanto shi sai ya yi saurin buɗe idanu ya gan ta a tsaye a kan shi, sake rufe idanunsa ya yi ya ce "Ki tafi please bana son damuwa zan neme ki."
Marairaicewa ta yi kamar za ta yi kuka ta durƙusa a gaban shi ta ɗaura hannayenta a kan cinyarsa tana shafawa ta ce "my love, are you okay?"
Girgiza mata kai kawai ya yi dan ji ya yi gabaɗaya ba zai iya motsa ko fa yatsarsa ba ce, wani irin fitinannan abu yake ji na fusgar shi zuciyarsa na ba shi umarni amma kwakwalwarsa ta hana hakan, da ƙyar ya iya faɗin " A'o'uzu billahi minan shaɗani rajim! La'ilaha illa antas subhanaka inni kuntu minan zalimin." Sai da ya maimaita sau uku sannan ya ji kuzarinsa na ɗan dawowa, ya buɗe idanu ya ce "Ki fita na ce miki."
Ganin ɗan ɓacin rai a kan fuskarsa yasa ta yi saurin miƙewa ta ce "My name is Ayush, ga kuma number wayata nan in ka gama yanke shawara ka kirani." Tana gama faɗin haka ta juya cikin jan hankali ta dinga taku tana kararraya har ta fita a office ɗin. Gabaɗaya Abdul ji ya yi ya kasa yin komai bacci ya rufe masa idanu, cikin wata iriyar kasala ya miƙe ya haɗa kan komai ya bar office ɗin. Yaran sa da mamaki suke kallon shi ganin yau ya tashi ba lokacin da ya saba tashi ba, sannan ko sallamar da yake musu bai yi ba sai kiran direbansa ya yi ya zo ya ɗauke shi...
Suna isa bakin wani madaidaicin gida suka buga ƙofar, wani matashin saurayi ya zo ya buɗe musu suka shigo yana musu barka da zuwa. Har cikin palon gidan suka kaita sannan Ali ya ce "Madam mu za mu tafi akwai masu tsaron ki suna waje da kin shirya ki kira na zo na ɗauke ki."
Murmushi ta yi ta ce "Ina yake to?"
Ali ya bi wata zigaga ta mara masa baya sai ga su a cikin wani palon inda ta ga Baba da matarsa sai Zaiyan da ke zaune ya juya mu su baya, cike da tsananin mamaki ta ce...
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[10/25, 4:05 Yamma] My Addatyna: ~A HAKA NAKE SON SHI~
Arewabooks.com: Saratalkasum1897
WhatsApp number: +966577675904
Shafi na (16)
Cike da mamaki ta ce "Baba! Me kuma ya kawo ka nan?" Ta faɗa tana isowa gaban su ta durƙusa. Murmishi Baba ya yi ya ce "Labarin mai tsayi ne ƴar nan, ki zauna a gaisa tukun." Ya faɗa yana nuna mata kan kujera, ita kuma ta yi kim kamar ba za ta zauna ba sai kuma ta zauna tana. Murmushi ta yi ta leƙa Zaiyan ta ga yana ta naɗe hannayensa da ɗankwalinta da ta bar masa. Ajiyar zuciya ta sauke cikin nutsuwa ta ce "Baba ina yinin ku? Ya kwana biyu kuma? Na sha kiran wayarka ba a ɗauka hankalina ya tashi na ce da Yaya ya kaini unguwarku na gani ko wani abu ne ya faru da kai, sai ya ce na bari ba yanzu ba ashe dai kuna nan abin ku."
Gyara zama matar Baba ta yi ta ce "Yarinya ai rana ɗaya aka kawo mu da Zaiyan, na yi matuƙar farin ciki da ya kubuto daga hannun mutanen nan."
Lumshe idanu ta yi ta kuma buɗe su a kan shi, ganin bai ma san ta zo ba sai ta tashi ta zagayo gaban shi ta tsugunna, hannu ta miƙa ta kama ɗankwalin tana murmushi ta ce "Zain!" Turo baki ya yi bai ɗago ya kalle ta ba, naɗe hannun da yake dai ya dakatar, mamaki ne ya kama ta ganin yaƙi ɗagowa bare ya san ita ce. Baba ya ce "Wannan fa wai fushi ne ya yi da mu, yana tambayar ina kike mun ce za ki zo shi ne ya ga ba ki zo ba ya juya mana baya."
Shuru ta yi tana kallon lips ɗinsa da yake saɓa su yana ɗan ciza su kamar mai jin zafi, ƙura mana idanu ta yi inda ta soma ganin baiwar kyan da Allah ya masa. Zararan gashin idanunsa da ya sa musu wani farin abu kamar gari ta ƙura wa idanu, murmushin da yake dimple ɗinsa na bayyana ta lumshe idanu cikin wani kalar yanayi mai wuyar fassarawa a baki ta buɗe su a kan shi ta ga dai bai kula ta ba, hannu ta kuma miƙawa ta ɗan shafo fuskarsa da yi fayau..