Sashe 84
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Æata rai ta yi ta ce "Haka kake faÉ—i, kuma na yi ta fama ka faÉ—i min su waye su amma sai ka ce wai sun fi ni rashin imani."
Murmushi Malam ya yi ya soma jan Carbi idanuwansa a rufe, bayan kusan kamar minti biyar ya aje ya ce ta zaɓi ɗaya ta dauka ta miƙa masa, sai da suka yi haka sau uku sannan ya ce mata ta je zai yi aiki a satin nan komai zai kammala.
Tana isowa gida ta yi packing ta fito cikin takun ta na izza da taƙama ta nufo part ɗin ta. Kiciɓus suka yi da Laraba kula riƙe a hannunta za ta fito daga part ɗin, kallon banza ta watsa mata ita kuma Laraba wani kalar shu'umin murmushi ta yi wa Umma ta jinjina kai tana kawar da kai gefe.
"Iyye! Ke uban wa ya ba ki izinin shigar min part ba tare da ni na sani ba?" Ta faɗa kamar za ta kai mata duka. Wani irin duhu ne ya mamaye zuciyar Laraba jin zagin da ta mata, ji ta yi da ba dan tana tuna kar ta ɓata musu aiki ba da ta shaƙi Umma ta zabga mata mari, saboda yawan zagin ta da take kamar wata uwarta, matsawa ta yi ta ce. "Haba don Allah, kuma yanzu sai kin zageni dan kawai kin ganni part ɗin ki? To Allah ya ba ki haƙuri kar ki sauke gajiyar yawon ki a kaina." Tana faɗin haka ta yi saurin wucewa fuu saboda matuƙar kufula da ta yi, idan har ta ce za ta sake daƙiƙa a wajan babu abin da zai hana ta fito mata a asalin ita ko wace ce, ita kuma ba za ta so hakan ba..
Da zagi Umma ta raka ta ta shige part É—in ta..
_NIGER_
Iman na zaune ta rafka tagumi gabaɗaya lamarin masarautar ya fitar mata a kai, ga ta kira Abir ta faɗa mata damuwarta amma sam wayar ba ta shiga a kashe, hakan ya sa ta kira Umma yau take tambayar ta ina Abir take in ta kira ba ta shiga, a nan ta sanar mata auren da ta yi, hankalinta ya yi mugun tashi da jin wannan labarin hakan ya sa ta kulle kan ta a ɗaki ta dinga rusar kuka tana tuhumar su Abba da Suhal ne silar komai da yake faruwa da ƴar'uwarta, da Suhal bai ce ya fasa auren ta ba suma su Abba ba su goya masa baya ba yanzu da tana cikin farin ciki a gidan mijinta. Dafata ta ji an yi ta yi saurin juyowa, sanye yake da shigar kayan gado wato tufafin gidan sarauta black colour ya daura hula yellow kalar zaren da aka yi wa rigar ado da shi, ƙafafuwansa cikin wasu tsadaddun takalma na fata suma launin kayan, murmushi ne shinfiɗe samar fuskarsa ya miƙa mata hannunsa alamar ta zo..
Maƙale kafaɗa ta yi tana turo baki, indai ta gan shi da wannan shiga to tabbas tasan garin zai bari, ita kuma tsoron kowa na masarautar take Ikilima da Mamma kaɗai ta yarda da su, lumshe idanu ya yi yana buɗe su a kanta kamar mai jin bacci, takowa ya yi ya iso gaban ta ya durƙusa ya ɗaura hannayensa a kan cinyarta, ɗayan hannun ya sa ya ɗago fuskarta yana girgiza mata kai.
Kwacewa ta yi tana ja da baya ta koma ƙuryar kujera ta haɗe kai da gwiwa ta shiga rera masa kuka kamar marainiya, dafe kai ya yi yana kallon agogo ganin lokaci na tafiya, ba yadda ya iya ya cire takalmansa ya zauna a gefen ta ya zuba mata ido. Ɗagowa ta yi jin shuru bai mata magana karaf suka haɗa idanu sai ta kuma fashewa da kuka ta ce "Ni ka tafi ka ba ni guri tun da dama ba tausayina kake ba."
Dariya ta ba shi sai ya yi murmushi ya dauke ta cak daga kan kujerar ya nufi É—aki da ita, duka ta dinga kai masa tana faÉ—in ya sauke ta har ya dire ta a kan gado, cire rigar ta sama ya yi ya cire hular ya hayo gadon ya dauko ta ya rungume.
Shuru ta yi tana sauke ajiyar zuciya har sai da ya ji ta ɗan samu sauki ya ɗago da ita ya zaunar, goge mata hawayen ya yi ya ce "My Iman waye ya taɓa min ke a gidan nan?"
Jin abin da ya faÉ—a ta turo baki ta kawar da kai gefe ta ce "Anty Baby ce." Ta faÉ—a tana sake sakin wani kukan.
Runtse idanu ya yi ya ce. "Me ta yi ita Princess É—in?"
Daina kukan ta yi ta ba shi labarin auren da ta yi, alamar mamaki shi ma ya nuna ya ce "Ni ma fa na kira ba ta dauka Allah ya sa dai lafiya."
Rigima ta sa masa tana kuka har da tirje-tirje take ta ce ba zai tafi ba sai ya kira mata ita sun yi magana, babu yadda ya iya ya ciro wayarsa ya lalibo number ta ya danna mata kira, har ta katse ba a dauka ba ta ce ya sake kira, sake kira ya yi ya miƙa mata wayar ta zaƙu ta ji an dauka, sai da ta kusa katsewa sannan ta ji an daga tare da yin sallama. Muryar da ta ji an yi sallamar ce ta ba ta mamaki ta ce "Hello ina me wayar take.?
Daga can ɓangaren aka ce yanzu za a kai mata, Iman tana jin Abir na cewa "Hajiya waye ya kirani?"
Ta Sakkwato ta miƙa mata wayar tana ce mata in ta amsa sai ta ga ko waye, amsa ta yi ganin sunan Suhal ɓaro-ɓaro akan screen ɗin wayar ta riƙe kai tunawa da Iman.
"Assalam alaikum, Ango mijin Bloodyna ya kwana biyu."
Kukan Iman ne ya iso majiyarta ta miƙe tsaye ta shige ɗaki, zama ta yi a gefen Zaiyan da yake bacci ta ce "Haba Iman ke wai sai shegen sakalci kika sa a gaba, me ya faru?"
Goge hawaye Iman ta yi ta kalli Suhal da shi ma ita yake kallo ta ce "Haba Anty Baby wannan wacce irin rayuwa ce haka kika daukar wa kanki? Ki yi aure ba tare da kowa ya rakaki gidan miji ba saboda zubar wa da kai daraja, kuma ki rasa ma wa zaki aura sai mai larurar ƙwaƙwalwa? An ce ma wai kin bar garin ke da shi Anty Baby in za ki je da kika bar asalinki inda danginki suke kika koma cikin mutanen da ba su san ki ba?"
Haɗiye kukan da ya zo mata ta yi tana huci zuciyarta na mata wani kalar azabbaben ciwo wanda ba zai musaltu a baki ba, nisawa ta yi ta ce "Ƴar'uwata ki daina zubar da hawaye akan abin da na aikata, nasan Allah na tare da ni, bakin da ya yi kuka wata rana shi zai yi dariya, ba zan sare ba kuma ban yi nadamar auren da na yi ba dan shi kaɗai ne samun kwanciyar hankali a gareni, duk abubuwan da suka dinga min ba su faɗa miki ba sai auren da na yi ne suka sanar da ke dan ki ga lefin abin da na aikata? Tabbas ban san yaushe na kafe sai na aure shi ba sai yanzu na gane shi ɗin a zaman mijina yake. Yanzu so kike na rabu da shi ya shiga duniya ya faɗa mugun hannu ni kuma na koma gida su ci gaba da ƙunsa min baƙin ciki har ya yi ajalina? To ba zan taɓa komawa Yobe ba zan ci gaba da zama a duk inda Allah ya kaini na kuma zauna da Zaiyan a matsayin mijina na har abada, ke ko da a haka a Zaiyan zai zauna bai warke ba ba zan taɓa barin sa ba saboda tun farkon haɗuwa da shi na kamu san shi. A HAKA NAKE SON SHI a matsayin mijina, A HAKA NAKE SON SHI ko da kuwa mutanen duniya za su nuna rashin dacewar hakan, A HAKA NAKE SON SHI duk rantsi duk wahala ba zan taɓa gudun shi ba, A HAKA NAKE SON SHI ko da tsirara yake yawo, A HAKA NAKE SON SHI zan faɗa ko a gaban waye. Ya kike so na yi da rayuwata Iman? Yaya Abdul yana min barazanar zai kashe ni har ma da Zaiyan? Yana tambaya ta abin da ban san da shi ba shi ya sa na yanke shawarar barin musu garin na koma wani yankin, na san dai kari da yawa maye ba zai ci kansa ba, kuma idan su sun ƙini wanda na tarar a nan suna so na muna zaune lafiya, in sha Allah kamar yadda na ƙudurta zan ci gaba da nema masa magani ko da kuwa kuɗin account ɗina za su ƙare. "Ta ƙarashe maganar tana share hawayen da suke ta sunturi kan kuncinta.
Sai da ta gama bayanin ta kaf daga Iman har Suhal ba wanda ya katse ta, Iman ta ƙara jin tausayi ƴar'uwarta ta, gyara zama ta yi tare da nisawa ta ce "Ki yi haƙuri Anty Baby in sha Allah komai zai zo daidai."
"Yaushe? Sai yaushe zan yi farin ciki Iman? Kin san kuwa tsananin raÉ—aÉ—i da ciwon da nake ji a gangar jiki da ruhina?"
Saurin katse ta Iman ta yi ta ce "Haba Anty Baby ke fa musulma ce ka da ki yi saɓo mana, ai duk tsanani yana tare da sauƙi, ki ci gaba da addu'a ni ma ina tayaki da Yaya Suhal Allah ya ba wa Zaiyan lafiya, amma ki faɗa min abin da Yaya Abdul ɗin ya miki."
Murmushi mai ciwon ta yi ta gyara zama tana yamutsa sumar kan Zaiyan zuciyarta na ƙara karaya na hali da suke ciki, nisawa ta yi ta ba ta labarin komai da ya faru har tafowar su Kano da yan fashin da suka so yi mata faɗe da yadda Ta Sakkwato ke yi mata kirki a gidan nasu na haya..