Sashe 65
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata daga cikin su ta ɗaka wa Hafsat duka a mazaunai ta ce "ƴar iska marar mutumci, to ki bi dai a hankali Wallahi in dai wannan ɗan zafin kan ne sai ya gasa miki aya a hannunki, mu za ki nunawa kin yi aure? Kai ku zo mu tafi gobe ma rana ce ai." Ta faɗa tana yin gaba. Dariya Hafsat ta yi tana maƙale kafaɗa irin ko a jikinta, sauran sallama suka mata suna jinjina tsaurin idanu irin na Hafsat. Ko lokacin da aka ɗaura aure Mom ɗin ta ta ce sai washegari za a kaita, ai kuwa ta yi tsalle ta dire ta ce Wallahi yau za a kai ta gidanta ba za ta sake kwana a gida ba. Saboda mamaki Mom ɗinta kasa magana ta yi ba ta taɓa tunanin rashin kunyar Hafsat ya kai har haka ba, ganin abin ya yi yawa aka kira Daddynta ya zo ta sake maimaita maganar a gaban shi ya kuwa ce kawai a kaita kar su ga lefin ta so ne. Sai da Mom ɗinta ta kira ta dan ayi mata nasiha ta kafe ta ce ita fa ta san yadda ake zaman aure haƙuri da biyayya ne dan haka ba sai an mata wata nasiha ba. Mommy ba ta tsinke da lamarin Hafsat ba sai da ta ga Hafsat ta shiga ta yi wanka tana cewa kwalliyar ma in ba za a mata ba sai ta yi da kanta, haka dai aka shirya ta suka tarkata ta aka kawo ta gidanta..
Zama ta yi ta kira kira Abdul yana ɗauka ta sa kuka, a ruɗe Abdul ya miƙe tsaye yana faɗin "My love lafiya kike kuka?"
Turo baki ta yi ta ce "To ba kai ba ne kaƙi zuwa sai jiran ka nake, ni fa so nake na gan ka kusa da ni." Ta faɗa tana yin baya ta kwanta tare lumshe idanu..
Da sauri ya ce "Am so sorry my love gani nan zuwa yanzu, please ki daina kuka." Ya faÉ—a yana katse kiran, kallon shi Hashim ya yi cike da mamaki ganin yadda ya ruÉ—e ya ce "Malam ba za ka tsaya su zo ba mu raka ka?" Ko ci kanka Abdul bai ce mishi ba ya dauki wayoyinsa y yi gaba, baki sake Hashim ke kallon Abdul har ya fita..
Yana packing ta leƙo daga window tana kallon shi, wani irin so da ƙaunar sa na ratsa ta ta yi saurin komawa kan gadon ta kwanta ta soma kukan ƙarya. Tun daga palo yake jin sautin kukan ya yi saurin shiga ɗakin duk ya riɗe kamar ba Abdul ba, da sauri ya hayo kan gadon ya ɗago da ita ya ce "My love yi shuru gani na zo."
Hannu ta sa tana murza idanu ta faɗa jikinsa ta dinga masa shagwaɓar wai ta gaji shi zai mata wanka, babu muso ya dauke ta cak ya nufi toilet da ita yana rarrashin ita kuma tana ƙara narke masa. Bayan sun gama wanka ko Sallah ba ta bari su yi ba ta manne masa da ya motsa za ta ce bayan ta ciwo, shi kuwa duk abin da ta ce masa biye mata yake yana shafa bayanta yana jero mata sannu ya ja musu bargo suka..
_NIGER_
Suna isa Niger cikin garin Niamey motoci daga gidan sarauta suka zo ɗaukan amaryar Yarima Suhal, wata irin faduwar gaba Iman ta ji ta kawo mata ziyara ta dafe ƙirji tana tunanin yadda dangin Suhal za su karɓe ta a matsayin suruka, sai da Mom Nabila ta dafa ta tare da cewa "Ka da ki sare Iman ki zama mai ƙarfafawa kanki gwiwa ba mai sakar da ita ba, ki yi Bismillah mu fita ga masu jiran mu nan a tsaye." Jinjina kai ta yi ta tuna maganganun Abir nan-da-nan ta ji kwarin gwiwa ya zo mata ta tashi Mom Nabila ta riƙo hannunta suka fito..
A hankali take taka matakalar jirgin har suka sauko dukkan su, da sauri masu hidimar gidan sarauta suka shinfiÉ—a wani jan carpet mai tsayi har bakin motar da amarya za ta shiga, a kan carpet É—in an sanya sunan *YARIMA SUHAL* da manyan harufa. Haka Mom Nabila ta saki hannun Iman ta ce ta nutsu ta bi kan carpet É—in ta dinga tafiya tana yin addu'a har ta shiga motar, da to ta amsa ta soma takawa a hankali da ta zo kusa da hidimai sai sun dan rusuna sun ce "Barka da sauka Gimbiya." Ita kuwa sai ta ji wani bambarakai wai namiji da suna Hajara! Haka ta dinga takawa cikin nutsuwa inda wasu ke cewa ai amaryar nan Æ´ar Gayu ce sosai ga izza da haka dai har ta shige Motar..
Saida aka dauke carpet É—in sannan Mom Nabila ta iso bakin motar ta kalli Iman ta ce "Sun ce wannan motar ke da Ango ne dan haka mu za mu shiga sauran, ki nutse kin ji." Ta faÉ—a a hankali ta yadda ba mai jin abin da take fada. Jinjina kai ta yi ita kuma duk suka nufi sauran motocin suka shiga aka nufi Masarauta..
Sai da suka yi nisa sosai daga airport ɗin ta ji an tsaya, ba ta ɗago ta ga ko a ina suke ba ta ƙara lulluɓe fuska tana jin wani sanyi na mamaye mata kamar mai jin zazzaɓi, motar aka buɗe masa cikin shigar sa irin kalar kayan jikinta ya shigo aka rufe sannan suka ja motar.. Wani kalar ƙamshi Iman ta shaƙa wanda tun da take jin ƙamshin turaruka ba ta taɓa jin ƙamshi mai daɗin wannan turaren da ta ji ba, a hankali ta ɗago kai dan ta ji ƙamshi sai ƙara mamaye motar yake. Waro idanu ta yi ganin Suhal zaune a daf da ita ya sha kyau kamar ba gobe, wani irin fitinannan kyau ta ga ya ƙara yi mata akan wanda ta san yana da shi ta lumshe idanunwanta ganin ba ma ita yake kallo ba hankalinshi a can yana kallon gefe, tunani ta dinga yi dama ya riga su zuwa ne? Girgiza kai ta yi ta soma wasa da yan yatsunta dan taji daɗi da bai mata magana ba..
"My Iman."
Ta ji ya kira sunan ta murya can ƙasa, ɗago kai ta yi ta kalle shi sai ta ga ya juyo sun haɗa idanu ta yi saurin sunkuyar da kai, sai da ya sake kiran ta sannan ta ɗan turo baki gaba ta ce "Ka ga Malam karka sake kiraye min suna." Ta faɗa tana murguɗa baki.
Murmushin gefen baki ya yi ya matso sosai daf da ita ya miƙa hannu ya janyo ta jikinsa ya rungume ta, zazzaro idanu Iman ta yi ta soma mutsu-mutsun kwacewa sai kuma ta ga hakan bai dace ba tun da akwai direba ga kuma dogari, ba dan ta so ba ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke ajiyar zuciya. Kumatunta ya shafa yana jin kamar ya mayar da ita cikinsa saboda yadda yake jin son ta na ratsa shi, a hankali ya sunkuyo ya manne mata kiss à kunci ya ce "Wannan bakin rashin kunyar taki sai na murɗe shi." Ya faɗa da wani kalar salo. Ji ta yi haushi ya kama ta kai da ba a son ka meye na wani zaƙewa? Turo baki ta kuma yi ba ta ce masa komai ba har suka iso masarautar..
A harabar masarautar suka samu su Mom Yasira tsaye suna jiran zuwan su, a hankali ya ɗago da ita kamar wanda ya ɗauki kwai,, ita kuwa duk haushi ya cika mata ciki ganin yadda yake mata ta yi kwafa tana aiko masa harara, duk kuma yana ganin abin da take ya share ya buɗe motar dogarai suka kewaye shi suna fadin "Gyara kimtsi da kyau! Allah ya taimaki Yarima ango." Fuskar nan a haɗe ya fito daga motar ya sunkuya ya kamo hannun Iman ya fito da ita ya tsayar da ita a gefen shi tare da jingina ta da jikinsa ya saƙalo hannunsa a ƙugunta. Guɗa matan suka ɗauka ana faɗin amaryar Yarima ta sauka lafiya, sai da aka kuma shinfiɗa musu carpet green color suka soma takawa, a hankali suke tafiya sai ya saki fuskar shi amma bai yi murmushi ba haka suka taka har zuwa babban palon Maimartaba suka zauna, a nan suka tarar da Mamma da Sarauniya Bilkisu da kuma Kilishi sun kakimce a kan kujera kowaccen su ta sha ado na ban mamaki kamar za su je gasar kyau, kasancewar su farare sai suka ƙara haska wajan duk da Kilishi baƙa ce amma ita ɗin ma ta yi kyau sosai..
Mom Yasira ta kama Iman ta zaunar da ita a gaban su Kilishi su kuma suka samu waje suka zauna.. A wulaƙance Sarauniya Bilkisu ta ce "Sannu da zuwa."
Amsawa suka yi da yawwa itama Kilishi ta musu sannu da zuwa inda Mamma kuma ke yi musu murmushi, Ammi ta riƙe baki ganin Mamma ba ta ce komai ba sai ma gani ta yi ta ɗago da Iman ta rungume ta tana ci gaba da murmushi. Iman da yake ta san labarin Mamma a wajan Abir sai ta ƙara shigewa jikinta, a hankali ta ɗago daga jikinta tana murmushi ta ce "Mamma."
Jinjina mata kai ta yi idanunwanta suka cika da hawaye ta yi saurin hana su zubowa, zama ta yi itama Iman ta zauna ta gaishe da su Kilishi suna mata wani irin kallo suka amsa.. Bayan sun gama aka ce duk su fita Maimartaba zai shigo a bar mace ɗaya a tare da Iman sai matan Sarki da Ango, Mom Yasira ta ce ita za ta tsaya su su tafi masauki, da farko Ammi ta so ta tsaya amma dan kar ta bayar da su ta haƙura suka fita...