← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 120

Sashe 74

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shi dai Baba komai aka ce to kawai yake faɗa ya ciro kuɗi a aljihunsa ya lissafa su dubu 30k ne ya miƙa wa Abba ya ce "Ga sadakin Hauwa'u ina nema wa Zaiyan auren ta."

Murmushi Abba ya yi ya amsa ya miƙa wa Daddy ya ce "Mun amsa kuma mun ba ka Mamana."

Baba gani yake kamar wasa kowa ya sheda sadaki a palon suka yi addu'a suka É—aura wa Abir da Zaiyan aure lokacin ita kuma ta gudu ta shige É—aki tana jin kanta kamar sabuwar halitta...

Bayan sun gama Salim ya yi jugum yana kallon ikon Allah, wai Abir ce aka É—aura wa aure a palo ba tare da an tara mutane dayawa ba? Tashi ya yi ya nufi É—akin ta jin Abba ya ce ya je ya sanar da ita ta haÉ—a komai nata su tafi, kwafa ya yi ya nufi É—akinta..

A gaban wardrobe ɗin ta ya same ta janyo ƙatuwar akwatunta tana zuba kaya, riƙe baki ya yi ya ce "Baby yanzu wai da gaske har kin zama matar aure.?"

Kallon banza ta watsa masa ta ce "Ga zahiri ka gani malam."

Gyaɗa kai ya yi kamar wani ƙadangare, yana tsaye ta kwashe kayanta bakiɗaya duk wani abin da tasan tana so sai da ta kwashe abin ta har da zannuwan gadonta duk ta kwashe, ganin ba za ta gama ba ya ce mata Baba na jiran ta ta ce to ya je tana zuwa ya fita..

Takardun da Mom ta ba ta ta dauko ta janyo ɗayar akwatin ta sa su a ƙasa duk wani abu da tasan mai amfani ne ta dauke kayanta ta cusa a akwati, ATM card ɗin ta ta saka a handbag ta kwashe kuɗaɗanta da ke cikin loka wani kuɗin ma tun Abie na da rai yake ba ta in za ta yo shopping duk take Tara su.. Bayan ta gama ta janyo akwatuna uku ta fito ta sa key ya kulle dakin ta nufo palo inda iya Baba kawai ta samu ta kalle shi tana murmushi ta ce "Baba muje."

Shi dai Baba jinjina lamarin nan yake na auren su, tashi ya yi ya amsar mata akwati É—aya suka fito zuwa harabar gidan inda ta bude motarta ta saka kayan, Baba ya shiga itama ta shiga za ta mata key sai ga Umma da sauri tana gyara zaman hijabi ta tsayar da ita..

"Abir ya za ki tafi ke É—aya ba za ki bari mu raka ki ba ne?".

Ɓata rai Abir ta yi ta ce "A'a Umma ai ba sai kun rakani ba da Baba za mu wuce." Ta faɗa tana kunna motar.

Dariya Umma ta yi tana tafa hannu wannan lamari ya mata daidai, ja baya ta yi ta ce "To matar Mahaukaci a gaishe da gida." Ta faÉ—a tana kuma yin wata dariyar.

Hannu kawai Abir ta daga mata Allah-Allah take ta bar gidan, hon ta yi Maigadi da ya cika da mamaki ya buɗe musu get yana bin Abir da kallo, kasa haƙura ya yi ya ce "Oh ikon Allah! Aure da mahaukaci mai babban suna? To Allah ya ba da zaman lafiya."

Cikin hauƙi take taƙi hankali kwance kamar bawan da ya samu 'yanci. Suna isa ta yi packing a harabar gidan ta kalli Baba ta ce "Baba kaima ba ka son auren nan namu ko?" Ta faɗa tana yin fuskar tausayi.

Saurin girgiza kai Baba ya yi ya ce. "Ina Hauwa'u, ai na ma fi kowa farin ciki da wannan aure naku, Allah ya biyaki da gidan aljanna akan abin da kike mana na alkhairi."

Amin ta ce suka fita daga motar ta buɗe ta ɗauko akwatunan suka ja ita da Baba suka nufi ciki. A hargitse suka samu palon an yi ɗaiɗai da kujerun palon hatta dining table ɗin palon an kakkarya kujerun, gefe ɗaya kuma an farfasa kayan wani show glass babba da ke gefen kujerun palon an amsa raga-raga. Kwalalo idanu Baba ya yi jikinsa ya ɗauki rawa nan-da-nan zufa ta shiga yanko masa ta ko'ina, kallon ko'ina na palon Abir take ganin ba kowa, kamar daga sama suka ji ƙaran fashewar wani abu a kitchen ta saki akwatin hannunta suka nufi kitchen ita da Baba. A hankali suke takawa har suka isa bakin kofar, a ruɗe ta kalli Zaiyan da ya dauko wani cup ya ɗaga zai dankwaza shi da ƙasa ta taƙarƙare ta ce "A'a Zaiyann..!!"

Cak ya dakata da fasa cup É—in ya É—ago kai ya kalli bakin kofar, ganin ita ce ya nufo ta da saurin yana sakin kuka ya faÉ—a jikinta tare da cewa "Antyy....!"

_Maman Nusaiba ce_

[11/15, 10:59 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~

Shafi na (36)

Da sauri ta sa hannu ta rungumo shi ganin yadda jikinsa yake rawa kamar mazari, nan-da-nan hankalin Baba ya tashi ganin idanuwan Zaiyan sun soma juyewa baƙin na yin sama. Ɗago da shi ta da kyar saboda nauyin da ya mata ta ga idanuwansa suna farfari ta juyo ta kalli Baba a ruɗe, hannu Baba ya sa ya amshi Zaiyan suka taka a hankali suka fito daga kitchen ɗin ko'ina ya zubar da kaya ya kashe. A hankali suka dinga jan shi ƙafafuwansa na jan ƙasa saboda ya musu nauyi, suka bi ta gefen da ba komai suka nufi ɗakinsa da shi. Ruwa Baba ya dauko da sauri ya dinga tofa addu'o'i a cikin sannan ya dinga shafa masa a fuska, miƙa ya dinga yi yana ƙara riƙe Abir da ta soma zubar da hawaye tana shafa kansa bakinta dauke da Addu'a. Zafi rau jikinsa ya ɗauka hakan ya sa Baba ya ɗauko bargo daga kan gadonsa ya lulluɓa masa yana fadin "Allah ya ba ka lafiya, bari naje na kira Ɗanladi mu kwashe kayan palon ke ki zauna a nan karki fito." Ya faɗa cikin jimami tare wucewa ya rufe musu ɗakin..

Shuru ta yi tana sauke ajiyar zuciya tana kallon fuskarsa, kyakkyawar girarsa da ta kwanta baƙa ta kai hannu ta taɓa ya ɗan motsa, saurin da

ɗauke hannu ta yi sai kuma ta ga ya ƙara shigewa jikinta yana jan numfashi. Buɗe idanu ya fara yi hakan ya sa ta soma kiran sunan shi, "Zaiyan buɗe idanuwanka ka ganni."

Hannu ya sa yana mitsitsika idanu jin muryarta ya buɗe idanu a kan kyakkyawar fuskarta tana sakar masa murmushi, saurin tashi ya yi daga jikinta yana zaro idanu ya daga baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya zura mata na mujiya. Murmushi ta yi tana gyara zama ta buɗe masa hanayenta ta ce "Zo nan ka kwanta ka ga ba ka da lafiya." Ta faɗa tana nuna masa cinyarta. Ɓata fuska ya yi yana riƙe kansa ya matso ya kwanta a cinyarta tare da zagaye ƙugunta da hannu ya lumshe idanu, ta goge hawayen da suka soma silalo mata tana shafa kansa a hankali tana ƙissima abubuwa daban-daban..

Baba na fita ya kira ÆŠanladi suka kwashe komai na palon, har kitchen suka kwashe wanda ya farfasa ÆŠanladi ya share ko'ina tas suka dauke carpet É—in palon suka fitar da shi waje suka zazzage tas tare da sharewa, dawo da shi suka yi suka shinfida ya yi wa ÆŠanladi godiya sannan ya fita shi kuma ya nufi É—akinsu dan ya watsa ruwa..

Ana kiran Sallar magariba Inna ta dawo daga wajan bikin da ta je, ko da ta shigo palon ta ga wayam babu kujeru sai akwatuna 3 da ta gani a palon, sosai ta cika da mamaki ta wuce ɗaki. A bakin ƙofa suka ci karo da Baba yana shirin tafiya Masallaci, ɗan murmushi ya yi ya ce "har kin dawo? To sannu da zuwa." Ya faɗa yana tsayawa a gaban ta. Itama murmushin ta mayar masa tana cire hijabin jikinta ta ce. "E na dawo Malam, amma ya na ga an dauke kujerun palon nan ko sabo za ka canja mana ne? Na ga kuma har da akwatuna." Ta faɗa tana kallon Baba. Girgiza mata kai ya yi ya ce "Ki bari in na dawo zan sanar da ke komai, ɗiyarki na nan tana ɗakin Zaiyan ki shigar mata da akwatunanta cikin ɗakin in dawo zan miki bayani." Ya faɗa yana wucewa. Cike mamaki Inna ke nanata Kalmar akwatuna, ganin dai ba mai ba ta amsa ta isa ta aje Jakarta ta shige bandaki..

Abir jin an kira Sallar magariba sai ta lallaɓa ta daga kan Zaiyan da nufin ta kwantar da shi, a hankali ta janye cinyarta ta kwantar da shi a kar carpet ta yunƙura za ta tashi ta ji an ruko ta, waro idanu ta yi ganin ya buɗe idanuwansa a kanta ya turo baki ya ce "Anty kar ki tafi ki bar ni." Ya faɗa yana tashi shi ma ya riƙe hannunta. Ba yadda ta iya haka ta buɗe wardrobe ɗin sa ta dauko masa wasu kayan yana rike da rigarta ta nufi toilet, a bakin ƙofar ta tsaya tare da kama hannunsa wanda ya riƙe mata gefen riga ta ce "To ka tsaya a nan na yo alwala sai na canja ma kayan." Ta faɗa tana zare hannunsa. Maƙale kafaɗa ya yi ya dawo bayanta ya kwanto kansa bisa kafaɗarta yana fadin "Dan ki gudu ne."
Chapter 74 · 0% Book details