Sashe 73
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya nisa ya ce "Mamana ki bar maganar Zaiyan kin ga ba shi da hankali, ki haƙura ki auri Salim ɗan'uwanki zai kula da ke."
Daddy da ya fusata ya ce. "Sulaiman ka daina ma rarrashin ta, ko ta ɗauka mu ma ba mu da hankalin ne irin ta za mu yarda a aura mata mahaukaci? To Wallahi ki ma canja zaɓi in ba haka ba ni da kaina zan ɗaura miki aure da Aruf ya dawo ayi bikin ku ya dauke ki ku tafi can ku ƙarata." Ya faɗa yana nuna ta hannu.
A zabure Abir ta ɗago tana nanata maganar Daddy, Uncle Aruf za a haɗa ta da shi bayan ta ce ga zaɓin ta? Tab ai kuwa ba zai yiyuba dole ne ta tsaya ƙyam akan ƙafafunta wajan ganin an ba ta wanda take so. Goge hawaye ta yi cikin tashin hankali ta ce. "Wallahi ni dai Abba ba na son Uncle Aruf ya fiya kula 'yan mata duk wadda ya gani sai ya ce yana son ta, Kuma ma ai ni ga wanda nake so in karya nake ku kira shi nan ku tambaye shi zai ce muku yana so na." Ta faɗa tana fashewa da kuka..
Abdul da ya kawo wuya ya zaburo ya zabga mata mari ji kake tas!Tas! Yana huci ya kama kunnenta cikin tsananin ɓacin rai ya ce "Su Abban ne suna faɗa ki na faɗa saboda ba ki da kunya? Wallahi na sake jin bakinki a wajan nan har a gama sai na kakkarya ki fitinanniya kawai, an ce ba za ki aure shi ba ƙanen banki ne shi?" Ya faɗa yana sake kai mata wani dukan Salim ya yi saurin riƙe hannunsa ganin yadda shatin yatsunsa suka baiyana ruɗu-ruɗu a kumatunta.
Rai ɓace Salim ya kalli su Abba da suka zuba musu idanu ya ce "Yanzu Abba kuna gani yake dukan ta kamar wata jaka ba za ku hana shi ba? Wannan wani irin zalinci ne? Ban taɓa tunanin irin wannan ranar za ta zo ba Yaya Abdul ya sa hannu ya daki Baby, ina ruwan ka da zaɓinta tun da kai dama yanzu ka tsane ta? Wallahi in ka sake dukan ta sai na rama mata baiwar gidanka ce ita da za kake dukan ta?" Ya faɗa kamar zai kai wa Abdul duka; nan da nan ran maza ya ɓaci sai huci yake yana kallon Abdul da shi ma a samar yake, bai taɓa tunanin akwai ranar da Abdul zai yi wa Abir haka ba saboda tsananin so da ƙaunar da ke tsakanin su..
Ganin abin ya kacame Umma ta miƙe tsaye tana murmushi tare da takowa ta iso gaban Abir ta miƙar da ita tsaye, share mata hawayen ta yi ta kalli su Daddy tana ɗan hade rai ta ce "Ku aura mata wanda take so mana meye a ciki? Ba dai yana da iyaye ba sai su yi zaman su, ni a matsayina ba ƙanwar mahaifinta kuma uwa a gareta ba zan taɓa bari ku aura mata wanda ba Zaiyan ba. Ba dai aure kuka so ta yi ba? To tun da ta kawo wanda take so ai sai ku bar ta ta aure shi in ba neman tashin hankali kuke yi ba a gidan nan, kun takura mata dayawa marainiyar Allah dan kun ga ba ta uwa ba ta da uba sai ita kaɗai, wanda take sa ran zai zame mata dangin uwa shi ma yanzu dukan ta yake ya kuke so ta yi ne? " Ta faɗa irin ga uwar tar nan na magana cike da gadara..
"Haba Baraka ya za ki ce mu bari ta auri mahaukaci? Anya kema ki na haiyacinki kuwa?" Abba ne ya faÉ—a cikin jimamin wannan lamari..
Ƙanƙance idanu Umma ta yi tana kada kai ta ce. "To uban iyayi ba fa zan bari ka aura mata wanda ba ta so ba, yadda kake tunƙaho Abir jininka ce ni ma jinjina ce, kun yi munafuncin ku kun raba ta da wanda take so kuka aura wa ƴar'uwarta, ba dan ba ma tana son Iman me kuke tunanin zai faru tsakanin su?" Ta faɗa tana hararar Ammi da ta saki baki da hanci tana kallon ta.
"Ihumm iko sai Lillahi ni Farida, au Allah ko Baraka ? To ke ki aura mata shi mu gani Æ´ar iya uwar shisshigi, ai duk kusancin ki da Abir su sun fi dan haka ki iya bakinki mu shayo kan matsalar nan." Ta faÉ—a tana kawar da kai.
Daddy ya dubi Abir ya ce "Shi dai kike so ko? Kuma za ki zauna da shi a matsayin miji?"
Gyada kai ta yi ta ce "Ni A HAKA NAKE SON SHI."
"To wa zai ciyar da ke yake tufatar da ke? Wa zai ba ku gida ku zauna?"
Turo baki ta yi ta ce "Ni zan saya mana gida sai nake kasuwanci." Ta faÉ—a tana hararar Abdul..
Ganin wannan magana ba mai ƙarewa ba ce Abba ya ce su tashi su tafi zai neme su gobe in kowa ya dawo daga aiki, haka kowa ya fita yana ta jinjina maganar Abir..
Abdul kuwa da mugun ɓacin rai ya bar gidan saboda maganganun da Salim ya yaɓa masa ya ji ya ƙara tsanar Abir, shi kuwa Salim wani irin tausayin Abir ne ya mamaye shi yana tunanin ta ya marar hankali zai auri mai hankali kamar gari ba manya? Haka dai ya shiga motarsa ya mata key ya wuce.
Ita kuwa Ammi kasa zama ta yi sam ba ta so Abba ya ce Salim zai aura wa Abir, dan ita ba ta son a haɗa yaronta da jinin matsiyata su Mom gara ta zaɓo masa a ɗiyan Aminanta yaran masu kudi su aura..
Su kuwa su Abba fita suka yi da nufin yin shawara.
Ita ko Abir tana shiga ɗaki kan gado ta faɗa ta fashe da kuka, wannan wacce irin jarrabawa ce haka? Kowa yanzu bai damu da ita ba, tashi ta yi zaune tana share hawaye ta soma magana cikin kuka. "Ya Allah ka fitar da ni daga wannan halin da nake ciki, kowa ba ya so na dan an ga mahaifiyata ta rasu Abie na ma ya rasu ba wanda ke min kallon so, da suna raye nasan ko da kowa ya gujeni su za su ƙaunace ni." Kai da gwiwa ta haɗe ta ci gaba da rero kuka, kamar daga sama ta ji saukar wani abu a gefen ta ta buɗe idanuwanta da sauri. Duhu ne ya mamaye ɗakin sai kawai ta ji wani sanyi ya ziyarci zuciyarta, a hankali ta sake duban gefen ta yi arba da shi ya yi tsaye yana kallon ta. Da sauri ta zabura ta miƙe tsaye baki na rawa ta ce "Z. Za.. Zaiyan." Ta faɗa a ruɗe.
Zama ya yi a bakin gadon yana sakar mata murmushi sai kawai ta ga ya soma canja halitta zuwa matar nan, dogon numfashi ta ja ganin ba shi É—in ba ne.
"Maijidda kukan ya isa haka." Ta faÉ—a tana dafa kafaÉ—arta.
Sabon kuka Abir ta sa cikin rashin sanin inda za ta sa ranta ta ji sanyi, cikin raunanniyar ta ce "Mama to ya zan yi?"
Shafa bayanta ta yi ta ce "Kar ki ce komai ki kwanta ki yi bacci, komai zai wuce amma auren ki da Zaiyan ba fashi ko me za su yi." Tana maganar tana shafa kan ta kwantar da ita tare da ja mata bargo. Nan da nan bacci ya yi awon gaba da ita, murmushi ta yi ta ɓace a ɗakin..
A fusace Alhaji ya kira Alhaji Mustapha sai safa da marwa yake, ganin ya daga ya soma sababi.
"Wai Mustapha me ka dauke mu ne? Ya za mu ji shuru kuma an yi aure watanni fiye da shida amma ba labarin wani abu da muka samu."
Daga can ɓangaren Alhaji Mustapha ya gyara zama ya ce "Kai fa daɗi na da kai Alhaji gaggawa, yanzu haka na kira Abdul akan cewa muna neman shi a gidana za mu tattauna akan wasu batutuwa kuma ya ce ko yanzu nake son ganin sa zai zo, ka kwantar da hankalinka ni ai nasan me nake yi." Ya faɗa yana kaɗa ƙafa.
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke ya ce "Ni yanzu ba wannan ba ma, wai yarinyar nan ta rasa wa za ta ce tana so sai mahaukacin nan da muka taɓa kamawa? Amma kai ya kake gani mu bari auren ya yiyu ko kuma mu sanar da Boka na kan dutse ya yi mana maganin ƴar banza?"
Ƴar dariya Alhaji Mustapha ya yi ya ce "Kai fa Alhaji wani lokacin ƙwaƙwalwarka manta lissafi take, ta ya ma za mu yarda a ƙi yin wannan auren? Ai wata dama ce ta zo mana in aka yi auren, da zarar an gama komai muna gano inda aka kai ta zance ya gama." Ya faɗa yana dariya. Shi ma dariyar Alhaji ya yi yana dukan kansa da hannu ya ce "Ka yi gaskiya Mustapha dan haka mu yi yadda za mu yi ayi a gama.."
Da haka dai suka gama tattaunawa kowa na kawo tashi shawarar..
Sai bayan kwana biyu aka sake yin taro inda dukkan su ba wanda ya sake muso akan zabin Abir, sosai ta yi mamaki ganin duk sun goya mata baya har da shi kan shi Abdul da yake dukan ta akan maganar, haka suka sa Abdul ya kira Baba a waya ya zo gidan da Yamma..
ABBA ya dubi Baba ya ce "Mamana ta ce ita Zaiyan take son aura."
A ruÉ—e Baba ya kalli Abir da ta yi kicin-kicin da fuska dan kar ma wani ya mata magana, Baba ji kawai ya yi wannan haÉ—in ya masa dan haka ya ce "Kwarai kuwa ai zan fi kowa farin ciki in hakan ta faru, in ma yanzu kuke son a É—aura na zo da sadaki."
DaÉ—i ne ya mamaye zuciyar Abir ta saki murmushi, Abdul ya ce "To Baba kawo ai ko iya mu mun isa mu É—aura mata aure kawai ta bika ku tafi ba sai an tsaya ana wani tara mutane ba."