Sashe 15
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin pink abaya ta shirya tana zuba ƙamshi kai ka ce sabuwar amarya ce, duk da ba wani jiki gare ta ba amma abayar ta yi mata kyau matuƙa, ta fito ta zauna a palo tana jiran Abdul ya sa a kaita..
Zaiyan na tsaye Baba Dattijo ya ce "Zaiyan yau Anty za ta zo." Waro idanu ya yi sai ya fashe da dariya ya ɗaga rabin taɓaryar dake hannunsa ya ce "Hahaha! Anty amma dai za ta kawo min abinci ko?" Ya faɗa yana ɓata fuska. Murmushi Baba Dattijo ya yi yana gyaɗa masa kai, miƙa masa awarar dake cikin leda ya yi ya ce "To ka ci kafin ta zo." Amsa ya yi ya buɗe ledar sai ya lumshe idanu tare da buɗewa ya dubi Baba ya ce "Ni fa Sarki ko?"
"Kwarai ma kuwa kai Sarki ne." Baba ya faɗa zuciyarsa na ƙara tausaya masa.
Dariya ya yi ya É—aga awarar sama yana wurga ledar awarar, Baba ya yi saurin ce masa "Ka daina yin haka mana ci za ka yi abinci ne."
Soke sandarsa ya yi a ƙasa ya buɗe ya soma ci, ganin haka ya sa Baba ya juya ya nufi gidansa...
Kiiii! Ya ji ƙaran mota ya yi saurin juyowa dan shi a tunanin shi hatsari ne aka yi, amma sai kawai ya ga wata ɓakar mota doguwa mai kama da ambulance ta tsaya a kusa da zaiyan, saurin nufo su ya yi sai dai kafin ya iso tuni sun ci zambar Zaiyan sun jefa shi a mota sun ja kiiii sun bar wajan...
Ganin shuru-shuru Abdul bai zo ba abin ya ɓata mata rai ta miƙe ta nufi part ɗin Umma. Da Sallama ta shiga amma ba kowa, hakan yasa ta yi saurin wucewa. Fatima da Yasmin suna zaune Umma ta fito tana tambayar wa ta ji yana Sallama? Yasmim ta ce "Wa za ki ji bayan wannan mai kama da aljannu."
Kwafa ta yi sai kuma ta saki murmushi ta yi saurin zuwa kitchen dan ta san Abdul tuni ya fita daga gidan. Ganin gawayi a kan wuta yasa ta yi maza ta ɗauko kasko ta ɗaura ta janyo wata ɓakar leda ta buɗe, abin da yake ciki ta kwaso ta afka nan-da-nan hayaƙi ya turnuke kitchen ɗin ta ɗauko da sauri ta kawo palo tana gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa duk suka yi saurin barin palon..
Abir ta duba ko'ina ba ta ga Abdul ba hakan yasa ta yi fushi ta fito da nufin zuwa wajan Salim shi ya kai ta. Tana shigowa palon kawai ta ji hayaƙi ya mamaye mata idanu da hancinta, cikin tashin hankali ta soma tari tana riƙe ƙirji. Sosai tari ya sarƙe ta nan-da-nan numfashinta ya soma barazanar rabuwa da gangar jikinta, tun tana tari a tsaye har ta kai ga ta durƙushe tana jan numfashi ɗifak-ɗifak haka ta rarrafa tana nufar ƙofar fita. Da ƙyar ta iya kawowa bakin ƙofa tana ci gaba da tari wannan karon da ƙyar take yi, in ta yi tarin sai huhunta da bayanta sun amsa ga wani irin mugun ciwo da azaba suke mata, ji take kamar ana yankan huhun nata sai daga baki take.
Salim ta gani tana ɗaga masa hannu amma sam bai gan ta ba hakan yasa ta zube a wajen yim! Ta faɗi ƙasa. Kamar an ce ya kalli gefe ya ganta, a guje ya isa tare da ɗago da ita cikin tashin hankali ya shiga jijjiga ta amma ina tuni ta sheƙa, hankali a tashe ya kira sunanta a ƙarfi.
"Babyyyyy!!!!
_*Ko ya za ta kaya? Ku
_*hanzarta ku sayi naku kar ayi babu ku*_
_Taku har kullum Maman Nusaiba ce_
[6/20, 7:37 PM] Ummu Amjad: :37 Yamma] My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_
*Arewabooks.com: Saratalkasum1897*
+966577675904
Shafi na tara (9)
A kiɗime yake jijjiga ta yana kiran sunan ta amma ko motsi bai ga ta yi ba, cikin azama ya ɗauke ta da mugun gudu ya nufi part ɗin Mommy da ita yana faɗin "Baby open eyes please." Gabaɗaya hankalin masu aikin gidan ya karkata kan Salim da yake ɗauke da Abir yana magana hankali a tashe. Da ƙafa ya buga ƙofar palon ta buɗe, Mommy da ta fito da cop a hannunta daga kitchen jin an buga ƙofar ba ta san lokacin da ta saki cop ɗin ba ya faɗi ya tarwatse, ganin Abir a hannun Salim yasa ta yi saurin nufar shi tana tambayar shi "Salim lafiya na ga Mamana a haka? Ko accident ta yi?" Ta faɗa tana tallafo ta gabaɗaya suka zauna a ƙasan capet. Huci yake yana kallon kyakyawar fuskarta da ta yi wani irin haske, hannunshi ya ɗauke daga kan wuyanta ya ce "Ni ma ban sani ba Mommy, na zo giftowa ne na waiga saitin part ɗin Umma na gan ta a bakin ƙofar a zube."
Kwala wa Laraba kira ta yi ta ce ta kawo ruwa mai sanyi sosai, cikin sauri sai ga ta ta kawo ruwan ganin Abir a mimmike kamar gawa ya sa ta ja ta tsaya a gefe tana dafe ƙirji. Ruwan Mommy ta shafa mata murya na rawa ta ce "Mamana ki buɗe idanunki." Ta faɗa zuciyarta cike da tunanin abin da ya same ta.
Da ƙyar ta ja numfashi kaɗan shi ma sai da Mommy ta kara kunne a ƙirjinta sannan ta ji sautin bugun zuciyarta na tafiya a hankali, hakan yasa ta miƙe cikin azama ta nufi ɗakin Abir sai kuma ta kalli jakarta da ke kan kujera, hakan yasa ta yi saurin buɗe jakar ta fito da maganin da take shaƙawa ta buɗe ta shaƙa mata tana zubar da hawayen tausayin ƴarta da ɗaya tilo.
A hankali ta ja numfashi hakan ya taimaka mata wajan shaƙo maganin sai ga numfashinta ya dawo daidai ta shiga sauke ajiyar zuciya.
Salim ya kamo hannunta cikin tausayin ƙanwar tashi ya zuba mata idanu ganin yadda take sauke ajiyar zuciya tana ɗan motsa hannunta, gyara zama ya yi a tausashe ya ce "My Baby buɗe idanunki." Ya kuma ɗago da kanta dake cinyar Mom tana goge mata fuska, saboda zufar da ta tsastsafo mata.
A hankali ta soma buɗe idanunta har ta gama buɗe shiga su a kan fuskar Salim, ta dinga kallon shi kamar ba ta san shi ba, Mommy ta taimaka mata ta tashi zaune suna mata sannu. Salim ya ja numfashi yana hamdala sannan ya ce "Baby me aka miki a part ɗin Umma da har ciwon ki ya tashi? Kuma tashin ma har ya kai matakin ƙarshe?" Ya faɗa yana zuba mata idanu.
Maƙoshinta ne ya bushe ta tattaro yawun da ya rage a bakin ta haɗiye shi ko za ta iya magana, sai ta runtse idanu sannan ta buɗe shi tana motsa bakinta amma maganar ba ta fita, hannu ta ɗaga ta dafe cikinta da har yanzu da sauran ciwon ta kalli ruwan da ke hannun Mom hakan yasa ta kafa mata baki ta shanye shi tas, sai bayan ta sha ne ta ji za ta iya magana.
"Kawai dai na je neman Yaya ne saboda mun yi da shi zai kaini Unguwa ko ya sa yaransa su kaini, to na ji shuru shi ne na je ɗakinsa dan na gani ko bai fito ba. Nan ta ba su labarin fitowar ta da hayaƙin da ya mamaye ta har hakan ta faru da ita. Fashewa da kuka Mommy ta yi ta ce "Ka gani ko Salim, ni ban san wani abu yarinyar nan ta tsare wa matar nan ba take son ganin sai ta kashe min ita, ai ta san sarai ba ta son hayaƙi shi ne dan ta ga ta shiga part ɗinta ta kunna mata hayaƙin. To Wallahi ta yi na farko ta yi na ƙarshe ba zan yarda ba a kashe min 'ya dan ba a son ta, haƙurina ya ƙare a wannan karon na rantsa da girman Ubangiji yau ɗin nan sai na kira an mana tsakani da ita ta daina cutar min da yarinya, ko ta manta shi Abdul ɗin ɗan'uwanta ne shi gaba da baya? Ba ta isa ta raba Abir da Abdul ba saboda su ɗin ta ko'ina sun haɗa jini dan haka dole ne ayi mana tsakani da ita in ba haka ba sai na yi ƙarar ta naji dalilin da yasa take son salwantar min da ran ɗiya." Ta ƙarashe maganar tana huci hawaye na zarya kan kuncinta, tabbas a wannan karon ta ji ba za ta juri cin kashin da ake mata ba dole a yi wa tufkar hanci kafin su ƙarasa mata ɗiyarta, ba ta san wani abu ta yi wa su Umma ba suke ɗaura mata karan tsana yanzu kuma abin ya tashi daga kan ta ya dawo kan ƴarta.. Kwafa ta yi tana kallon Abir gabaɗaya duk ba ta jin daɗin duniyar, da faɗin ɓakar maganar familyn za ta ji ko da rashin sanin inda mijinta yake? Ko kuma da zama cikin firgici da tsoron da take ciki?
Shi kan shi Salim ya jinjina wa haƙurin Mommy yadda Umma da Ammi ke yi mata wasu abubuwan kamar kishiyar su, shi wani lokacin har mamaki yake in ya ji Ammin nasu na faɗin mummunan furuci akan Mom bayan yasan shi a iya sanin shi Mom ba ta shiga harkar kowa. Gyara zama ya yi ya ce "Mommy ba zan hana ki faɗa wa su Abba wannan lamarin ba, saboda kin yi haƙuri na tsayin wannan shekarun ban taɓa gani kin ce komai ba game da abin da suke miki."