← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 120

Sashe 117

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A Abuja aka sauke su daga nan wani jirgin ya ɗauko su ya kawo su Yola, Ali ne ya zo ɗaukan su a babbar mota. Hannun Abir sakale da na Mamma suka sauko daga cikin jirgin suna murmushi, Mamma ta lumshe idanu jin ta a ƙasar da ta taso, Ali da ya hango su daga naisa kwalalo idanu waje ya yi yana kallon Mamma gani yake kamar Mom ce ta yi fatalwa ta riƙe hannun Abir, har suka iso inda yake bai sani ba sai da Abdul ya girgiza shi sannan ya yi saurin ƙamewa yana sara mata tare da cewa "welcome back Sir."

Ya sake kallon Mamma ya ce "Sir wai ni kadai ne nake ganin Mom na min gizo ko kuwa kuma kuna ganin ta?"

Dariya Abir ta yi ta ruko hannun Mamma ta ce "Ba gizo ba ne kuma ba ita ba ce, Æ´ar'uwarta ce." Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi ya gaishe da ita ta amsa tukun ya buÉ—e musu suka shiga ya ja suka bar wajan..

Suna zuwa gida su Abba duk sun tsaya a harabar gidan suna jiran zuwan su, fitowa Ali ya yi ya buÉ—e musu kofa suka fito ita da Abir. Fatima ta waro idanu tana faÉ—in "Wow Abba Wallahi ba dan kun ce min Mom twins ce da za iya rantsewa wannan Mom ce." Murmushi kawai Abba ya yi yana yi wa Mamma barka da zuwa ta amsa cikin fara'a, kallon Daddy ta yi ta ce "Kabir kaine haka ka girma?"

Ƴar dariya Daddy ya yi yana riƙe da hannun Khairat ya ce "Haba dai Usainar matar Yaya shekaru ai sun ja, ke kanki ai ba haka kike ba."

Part É—in su Abir suka nufa suka yada zango a nan, Grandma ta yi kuka na ganin Mamma saboda da tuna Mom. Sabon kuka aka yi Gradma na tambayar mijinta ta ce suna nan zuwa ai, sai da komai ya lafa sannan suka ci abinci aka dawo palo aka ci gaba da hira. Suna tsaka da hira sai ga Hafsat ta faÉ—o palon a firgice, kallon ta duk suka yi ta zube a gaban Abir ta fashe da kuka, Abir ta É—ago da ita tana faÉ—in "Friend lafiya kike kuwa? Me ya faru kika shigo haka a firgice?"

"Don Allah Baby ki taimake ni ki rufa min asiri, Wallahi in na bar gidan Yaya Abdul mutuwa zan yi, ki ba shi haƙuri ya maida ni ɗakina ai ba ni na masa lefin ba, kuma ban taɓa sanin Daddy mutumin banza ba ne sai yau. Don Allah ki sa baki ya mayar da ni Wallahi ina son shi, ko ba dan ni ba ɗan cikinsa da ke jikina ya yi haƙuri ya zauna da ni na haife shi a gidan ubansa, nasan Daddy Mai lefi NE a gare ku amma ni ban yi muku komai ba Wallahi da zuciya ɗaya nake son ku daga ke har shi." Hafsat ke faɗa tana gunjin kuka gwanin ban tausayi.. Mamma ta kalli Abdul tana haɗe rai ta ce "Me ya sa ka yi wannan ɗanyan aikin Abdul? Ka sanar da iyayenka da za ka sake ta?"

Sunkuyar da kai Abdul ya yi yana hararar Hafsat da take kallon shi tana kuka, sai da ta sake magana sannan ya ce "To Mamma ai na ga da mahaifinta aka kashe Abie da Mom, ni ban ga ba amfanin zamana da ita saboda wataran za ta iya cutar da ni, ni ko auren ta da na yi ban san yaushe na ce ita zan aura ba duk cikin tuggun babanta ne, ta wannan hanyar ya yi amfani na dinga yin abubuwan da sai da na tsani kaina bayan na dawo haiyacina, kin ga kuwa ai ba matar zama ba ce tun da ubanta ƙanen Fir'auna ne. "

Dakuwa Mamma ta yi wa Abdul ta ce "Na ci gidanku Abdul, ka taɓa gani lefin wani ya shafi wani? Kai za ka ji daɗi idan Suhal ya sako Iman?"

Daure fuska ya yi ya ce "Allah Mamma ba wani rashin jin daÉ—in da zan yi dan Suhal ya sako Iman ai uwarta ta ja mata."

Faɗa sosai Mamma ta yi masa ta ce ya je ya dawo da matarsa tun kafin ta saba masa, ita ba ta da lefin komai babanta ne mai lefi dan haka kar ya ɗaura wannan lefi akan ta ba ta san hawa ba bare sauka. Sosai Hafsat ta ji daɗi matuƙa ta dinga yi wa Mamma godiya sai cewa take kamar kara aka tsaga ita Mom, murmushi Mamma ta yi ta lallaba Hafsat ta ce ta je gida Abdul zai je ya dawo da ita, cikin farin ciki ta tashi ta tafi....

Su Alhaji Mustapha suna tsaka da cin karansu ba babbaka ciwo ya rufe su su ukun duka, tsutsotsi ne ke fita daga duburarsu abin ya tayar musu da hankali suka garzaya asibiti. Likita ya É—aura su akan magani ta nan ne ma abin ya zo musu da sauki, suka ci gaba da sharholiyarsu ta siyasa. A zaman watannin da Alhaji Mustapha ya yi a kan kujerar mulki ya saci kuÉ—i masu mugun yawa, duk abin da aka ba shi ya raba wa 'yan Jaharsa sai ya raba a kashi goma ya dauki kashi É—aya ya ba su sauran kuma ya danne shi.

Kwatsam sai ga shi yau an aiko musu tsammaci daga kotu Abba yana karansu akan kashe masa ɗan'uwa da suka yi, Abdul yana karansu akan kashe masa yayar mahaifiya da suka yi, Zaiyan yana karansu akan cutarwar da suka mishi har ya zama mahaukaci. Zufa ce ta dinga karyo musu duk sanyin AC da ke palon amma jikin su ya yi sharkaf, Hausawa na cewa marar gaskiya ko a ruwa gumi yake! Hankali a tashi Daddyn Aruf ya wuce gida yana susa duk jikinsu ƙaiƙayi yake musu...

Yau su Zaiyan suka iso kuma yau ne zaman farko na kotu, suna sauka suka ɗan huta tukun suka ɗunguma su duka gidan suka tafi kotu. Suna isa kowa ya zauna sai ga su Alhaji Mustapha sun iso su da maƙarrabansu suka je in ake tsayawa duk suka tsaya sai wani cin magani suke. Jarmai ya ce "Kar ku kuskura ku ba da hanyar da za ta nuna duk abin da muka faɗa ƙarya muka yi." Ya faɗa ƙasa-ƙasar, ɗagowar da zai yi suka haɗa idanu da Mai martaba ya zaro idanu yana daddaɓa kafaɗar Daddyn Aruf ya ƙara Sunkuyar da kai ya ce "Kamar Alhaji Abdu nake gani da kayan sarauta."

Kallon in da yake Daddyn Aruf ya yi ai kuwa ya gan shi, gabaÉ—aya tsoro ya kama su suka Sunkuyar da kai suna addu'ar Allah ya sa ba shi ba ne fatalwarsa ce....

Maman Nusaiba ce....

[12/22, 11:09 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI*

END.

Shafi na 56

Alƙali na isowa bayan ya zauna ya yi a rubuce-rubuce Magatakarda ya tashi tsaye ya soma bayani, "A yau ranar Talata ashirin ga watan Yuni Alhaji Sulaiman yake ƙaran ɗan'uwansa Alhaji Sadisu tare da abokansa Alhaji Mustapha Gwamnan mai ci a yanzu da kuma Jarmai, D. S. P Abdul Kabir shi ma yana ƙaran su a bisa zargin kashe masa yayar mahaifiya.." Haka dai ya gabatar duk ƙaran da aka shigar ya miƙa wa Alƙali takardar ya koma ya zauna. Alƙali ya yi rubuce-rubuce sannan ya ɗago yana gyara zaman glas ɗinsa ya ce "Ko lauyan mai ƙara yana kusa?"

Miƙewa Barrister ya yi ya gyara zaman rigarsa ya tsaya da kyau sannan ya ce "Sunana Barrister Huzaifa Alaramma, ni ne lauyan wanda yake ƙara." Ya koma ya zauna.

Jinjina kai Alƙali ya yi ya kuma cewa, "Ko Lauyan wanɗanda ake ƙara yana kusa?".

Tashi ya yi tare da rusunawa ya ce "Sunana Barrister Shamsuddin ƙaribullah ni ne lauyan wanɗanda ake ƙara." Ya koma ya zauna.

Alƙali ya ba da dama lauyan wanda ya yi ƙara ya fara tambayoyinsa, tashi Barrister Huzaifa ya yi ya isa gaban su Alhaji Mustapha yana murmushi ya dube su sannan ya ce "Shin ko za ku iya bayyana wa kotu sunanyenku?"

Wani mugun takaici ne ya kama Dadyn Aruf ji yake kamar ya shaƙe Barrister Huzaifa, shi ya fara gabatar da kan shi sannan su Alhaji Mustapha. Gyara tsayuwa ya yi ya kalli Daddyn Aruf ya ce "Alhaji Sadisu shin ko za ka iya faɗa mana alaƙarka da Alhaji Ibrahim Maitama?"

Yana wani ciccin magani ya fara magana, "Ibrahim É—an'uwana ne shi da mahaifiyata da mahaifinsa uwa É—aya uba É—aya suke, kuma abokin kasuwanci na ne shi." Ya faÉ—a yana hura hanci.

Girgiza kai Barrister ya yi ya ce "OK to amma me ya haɗa ka da shi har kuka sace shi daga ƙarshe kuka kashe shi."

"Ubjection my lord! Ya kamata barrister ya daina ƙoƙarin rikita wanda yake tambaya." Cewar Barrister Shamsuddin.

"Ƙorafi ya karbu Barrister ka gyara kalamanka."

Ɗan rusunawa Barrister ya yi sannan ya kalli Alƙali ya ce "Ya mai girma mai shari'a ina son kotu ta ba ni dama na gabatar da shaida ta ta farko, ina son kotu ta kira min Baraka."

Mai kira ya ƙara sanarwa in Baraka tana nan ta fito, aka buɗe ƙofar kotun sai ga Umma tare da 'yan sanda duk ta yi baƙi ta rame ga wasu kuraje da suka ɓata mata fatar jiki, ta iso ta tsaya a gefen su tana sunkuyar da kai ganin Iman na kallon ta.

"Baraka muna so ki sanar da kotu gaskiyar abin da ya faru tsakanin ku da Alhaji Ibrahim har aka tsinci gawarsa..

Hawaye suka gangaro kan kuncinta ta jinjina kai tana jin damasa marar iyaka na shiga jikinta, a hankali ta buɗe baki murya na rawa ta ce "Na yi alƙawari zan sanar da kotu gaskiyar abin da ta tambaye ni in dai har na sani."

Jinjina kai Barrister ya yi ya ce "Muna sauranron ki mana bayani yadda ku huÉ—un nan kuka ci amanar Alhaji Ibrahim."

"Ubjection my lord! Ya kamata Barrister Huzaifa ya daina sa mata magana a baki."Cewar Barrister Shamsuddin..

"Ƙorafi bai karbu ba, Barrister za ka iya ci gaba da tambayarka. "

Murmushi ya yi ya dubi Umma ya ce "Malama Baraka ki taimaka ki sanar da kotu gaskiya kar ki wahalar da shari'a."
Chapter 117 · 0% Book details