← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 120

Sashe 105

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da ta dawo ba ta ce musu ga abin da ya faru da ita ba sai kuka kawai take, zazzabi kuma ba ya barin jikinta ba ta iya komai sai kwanciya in ta farka ta dasa kuka tana kiran sunan Zaiyan kamar wata yarinyar goye. Wannan abu ba ƙaramin tsayar wa da Tasakkawato hankali ya yi ba, hakan ya sa ta dauke ta ta kaita wajan Limamin da ke kusan gidansu ta ce ya yi mata addu'a ko ta dawo haiyacinta, haka aka mata Addu'ar suka dawo cikin ikon Allah ta rage yin kukan sai dai ta yi tagumi tana kallon matan gidan. Sai da Tasakkawato ta lallaɓa ta tukun ta sanar da ita Big Boy ne ya kuma sace ta, ta sanar ita komai da ya faru. Salati ta dinga yi ta ce dole ne su kai ƙaran shi wajan 'yan sanda ayi musu tsakani, washe gari ta shirya ta dauke ta suka tafi office ɗin' yan sanda suka shigar da ƙara. Bayan sun gama shigar da ƙaran aka ce su faɗi gidan waye dan a kira shi ayi musu tsakani? Abir ta ce ba ta sunan shi na asali ba ko iyayensa amma dai ana ce masa Big boy, nan wani ɗan sanda ya riƙe baki ya ce tabbas ya san shi su tafi zai sa a kira shi su musu tsakani. Sai bayan sun tafi wannan ɗan sandan ya ce su jaga takardar da aka shigar ƙaran dan za su iya rasa aikin su saboda wannan kes ɗin, sanin waye mahaifin Big boy ya sa suka yaga takardar suka ci gaba da lamarin su..

Zazzaɓi dai yaƙi rabuwa da ita kullum tana kwance sai ƙara ramewa take, hakan ya sa takanas Tasakkawato ta leka gidan maƙociyarsu kasancewar ta likita ta ce ta zo ta duba Abir ɗin..

Bayan ta zo ta mata gwaje-gwaje ta gama, tambayoyi da dinga mata tana ba ta amsa sannan ta mata allura, bayan ta gama mata ta yi rubutu a takarda ta miƙa mata tana murmushi ta ce "Congratulations Allah ya raba lafiya."

Baki sake Abir take kallon Doctor Tasakkawato ta rungume ta tana faÉ—in "Kai Alhamdu Lillah zan yi jika Jiddo ta samu juna biyu."

Dak! Dak! Dak! Haka zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri, sai ta rasa abin da za ta yi kawai ta fashe da kuka tana ƙanƙame Tasakkawato, shafa kanta take ta ƙara riƙe ta aka mata allura wanda hakan ya ƙara wa kukan ta mai. Suna cikin haka suka ji maganar mijin Tasakkawato yana kiran ta, sakin Abir ta yi ta fito tana shirin yin magana ta haɗa idanu da Zaiyan da ke bayan mijinta, waro idanu ta yi sai kuma ta yi dariya ta koma ɗakin da sauri ta kama hannun Abir da ta tsayar da kukan ta ce "Ke tashi mijinki ya dawo."

Kafin ma ta taimaka mata ta tashi ta yi saurin mikewa ta yo waje kanta ko ɗankwali babu, tana fitowa da shi ta fara yin arba ya harɗe hannayensa a ƙirji yana sakar mata da ƙayataccan murmushi irin na masoyan da suka daɗe ba su ga juna ba. Da sauri ta isa gare shi ba ta ji kunyar kowa ba ta faɗa jikinsa tana sakin sabon kuka, shi ma ba kunya ya ƙara rungume abar shi yana shafa bayanta..

Sumar wucin gadi Bashow ya yi ganin Abir a zahiri, sosai ya shagala da kallon su.

Murmushi ya kuma yi ya É—ago da ita daga jikinsa ya sa hannu ya shiga share mata hawayen yana faÉ—in "Yi hakuri Baby ba gani na dawo ba."

Turo baki ta yi tana kallon gefen shi, da alamar tambaya ta dawo da kallon ta kan Zaiyan sai kuma ta ji ashe fa ba ta da ko ɗankwali, da sauri ta matsa za ta koma ɗaki Tasakkawato ta miƙo mata Hijabi, amsa ta yi ta saka tana sunkuyar da kai.

Dariya Maman Amal ta yi ta ce "Ikon Allah sai yanzu kika ji kunyar mu Jiddo?"

Rufe fuska ta yi tana komawa gefen Zaiyan ta tsaya, Tasakkawato ta ba su key É—in É—akinsu Zaiyan ya ce " Mama barka da rana."

Murmushi ta yi ta ce "Kwan lahiyarka É—an nan? Na shiga damuwa da ba ka zo ba har Jiddo ta dawo rashin lafiya ta rufe ta, yanzu dai ku zo muje daga ciki."

Murmushi ya yi yana ƙara jin son Tasakkawato da ta zame musu uwa shi da matarsa, bin bayanta suka yi suka shige ciki, ruwa ta dauko musu suka sha. Takardar ta miƙa masa ta ce" Kalli ka ga. "

Amsa ya yi yana duba takardar inda ya ga an sa Jiddonsa na dauke da ciki har na wata biyu cif, da sauri É—ago yana kallon su baki na rawa ya ce "M.. Ma.. Ma shin da gaske ne Jiddo tana dauke da cikina a jikinta?"

GyaÉ—a masa kai ta yi sai gani ta yi ya sauka daga kan kujera ya yi Sujjada yana faÉ—in "Alhamdu Lillah ya Allah."

Bayan ya dawo ya kalli Abir ji yake kamar ya rungumi abar shi amma ba zai iya ba a gaban Tasakkwato, ganin kallon da suke wa juna Bashow ya miƙe ya ce yana zuwa, Tasakkawato ta cikin ɗakinta tana murmushi, ganin haka ya sa shi miƙar da ita suka fito hannayensu cikin na juna ya bude ɗakin suka shiga.. Janyo ta ya yi ya manna mata kiss a Kuma cikin wani kalar salo ya ce "Miss you Baby."

Narke masa ta yi ya ja ta suka faɗa kan katifa, buɗe cikin ta ya yi ya ƙara kunne akai yana murmushi, ta ture shi tana faɗin "Ya za ka kwanta min a ruwan ciki?" Ta faɗa tana murguda masa baki.

Dariya ya yi ya dawo gefen ta ya haɗa goshinsa na ta ta maƙale masa, lumshe idanu ya yi ya ce "Baby ya kamata mu koma Yola fa."

Saurin tashi ta yi a jikinsa ya sa hannu ya dawo da ita, gyaran murya ya yi suna kallon juna cikin ido ya ce "Akwai abin da nake son yi a can, kuma na ga saƙon ƙanwarki tana cewa hankalin Family a tashe yake na rashin sanin inda kike, so ya kamata mu koma can zai fi dan ni kaina ina son sanin inda Mamana take."

Hannunsa ta riƙe tana tuna familynta sai ta ji ta kwaɗaitu da son ganin su musamman Yayanta, nisawa ta yi sannan ta ce "Ni ma ina son naje gida."

Kwanciya ta yi suka ci gaba da hira..

Tun da aka ce tana da ciki Zaiyan ke tattalin ta, da zarar ya fita zai yi ta kiran ta yana tambayarta me take so ta ci ya zo mata da shi? Idan 'yan rigimar suka zo sai ta samu wani abu mai wiyar samu ta ce shi take so, shi kuma haka zai yi ta nema da kyar ya samu ya kawo mata. Soyayya suke zubawa ta gaban kwatance idan ya dawo yana tare da matarsa ko hirar daren da suke yi da yanzu ya hana ta yana maƙale da abarsa suna shan soyayya, ita kuwa dama abin da take so kenan a ba ta kulawa ta musamman a dinga ririta ta, hakan ya ƙara narkar da zuciya a cikin kogin kaunar mijin nata...

Sai da suka dauki sati sannan suka shirya suka ce za su koma inda suka fito, ranar Tasakkawato ta sha kuka da kyar suka rabu da juna ita da Abir, Abir ta ce mata ta dauki duk kayan amfanin ta da zarar ta samu lokaci za ta zo kuma za suke waya kullum, da haka dai suka tafi har kofar gida suka yo musu rakiya suna É—aga musu hannu....

Gidan su Bashow suka je inda Maman Bashow ke ta nan-nan da Abir, Zaiyan ya sanar da ita ai Abir na da ciki, ta taya su murna tana murmushi ta ce "Ya kamata ka yi wa abokinka faÉ—a ko zai samu ya yi auren shi ma."

Jinjina kai ya yi suka mata sallama suka fito, key ɗin mota Bashow ya ba shi suka shiga ta ɗaura niƙaf yana kallon ta da mamaki, murmushi kawai ta masa Bashow ya ɗaga musu hannu har suka bar harabar gidan...

Sai bayan La'asar suka isa Yola Abir na ta sha bacci abin ta, gidan su Abir ya nufa har sai da ya kusa isa ya tashi ta ta gan ta kusan Unguwarsu, wasu zafafan hawaye suka zubo mata ta yi saurin gogewa. Hon ya yi Maigadi ya leƙo sai kuma ya koma ya bude musu get suka shigo. Da mamaki Maigadi ke kallon motar har Zaiyan ya fito cikin shigar ta shadda fara ƙal, saurin isowa Maigadi ya yi ya rusuna ya ce "A'a, ranka ya daɗe barka da zuwa saukar yaushe?"

Da mamaki ya kalli Maigadi sai kuma ya basar ya yi murmushi ya ce "Lafiya lau mutanen gidan suna nan kuwa?"

Jinjina masa kai ya yi tare da tabbatar masa duk suna nan, gefen da take ya je ya bude mata ta fito suka nufi part ɗinsu. Hayaniya ce ke tashi a palon Abir ta kalli Zaiyan sai suka ɗan tsaya, sautin muryar Abba suka ji yana faɗin, "Wallahi Baraka Kin cuce mu duniya da lahira, ban taɓa tunanin za ki iya aikata wannan mugun abin ba, yanzu sai ki faɗa mana inda ƴarmu take muje mu nemo ta, marainiyar Allah babu abin da ta tsare miki amma kika mata wannan cutarwar za ki ga sakamako.."

Kasa jurar maganganunsu suka yi Abir ta cire niƙaf ɗin ta buɗe ƙofar palon bakinta dauke da sallama. Gabaɗaya ƙofar suka kallo, wani ihun murna Fatima ta yi ta nufi Abir tana faɗin "Abba ga Baby ta dawo."
Chapter 105 · 0% Book details