Sashe 90
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kujera ya nuna mata cike da izza cikin kakkausar murya ya ce "Baby zauna a kan kujera." Ya faɗa yana nuna mata da hannu. Durkushewa ta yi ta fashe da kuka jikinta na rawa, zama ya yi akan kujerar ya kafe ta da ido yana ciza lip ɗin sa na ƙasa shausƙin son ta na jan shi, tashi ya yi ya iso gaban ta ya tsugunna tare da kai hannu da nufin ya goge mata hawaye. A zabure ta yi baya tana girgiza masa kai cikin karaji ta ce. "Kai waye? Me na tsare maka da kake son takura wa rayuwata? Don girman Allah ka rabu da ni na koma wajan mijina yanzu ban san a wani hali yake ba." Ta faɗa tana haɗe hannayenta duka biyun.
Dunƙule hannu ya yi ya naushi iska yana dafe kai, wani irin tafasa zuciyarsa take da ta ambaci sunan wani a matsayin miji ba shi ba, ɗago da idanuwansa ya yi da suka yi jajur saboda ɓacin rai ya ce "Ba ki da wani miji wanda ya fini Baby, tun da kika tako ƙafarki gidan nan kin zo kenan har abada, dan haka gobe zan sa a rubuta miki takardar sakin wancan mijin naki sai a ɗaura mana aure. Ina matuƙar son ki Baby kuma duk abin da kike so a gidan nan zan miki, kowacce ƙasa kike so a duniya zan kaiki ki shaƙata ki ga duniya, me za ki da wancan mijin naki da alama ma ko abincin kirki baya baki, kalli yadda kika rame kika ƙara baƙi kamar ba ke ba, zan samar miki da duk wani jin daɗin rayuwa ki share wancan mijin naki. " Ya ƙarashe magana zai kamo ta.
Ƙara ta ƙwalla ba shiri ya janye hannun yana faɗin "OK na daina, yanzu faɗa min me kike so a kawo miki? Kina shan giya?"
Kwalalo idanu waje ta yi ta sake rushewa da kuka cikin tashin hankali, yau ji take mutuwar ta ce ta zo wai ita ce a gidan masu shan giya har ana tambayar ta ko tana sha? Girgiza kai ta yi ta tsayar da kukan cikin rawar baki ta soma magana.
"Kai musulmi ne ko kirista?"
Kan shi tsaye ya ce. "Musulmi ne ni."
"Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Allahuma ajurni fi musibati wa akalifili kharan minha! Wannan wacce irin masifa ce nake gani ni Hauwa'u? Ya Allah ka ceci rayuwarmu ni da mijina daga sharrin bayinka."
Saƙare ya yi yana kallon ta, shi bai ga wani abin tayar da hankali ba a maganarsa, ganin ita yake kallo ta daure ta aro jarumta ta gyara zama ta ce "Bawan Allah a ina ka taɓa ganin an yi aure kan aure? Na ce ma ina da miji ko ba ka san haramun ba ne ka ce kana son macen da take da aure? Da ka je Islamiya ba a sanar da kai bambancin haram da halal ba?"
Sake kashe shi ta yi da mamaki, can ya maƙale kafaɗa ya ce "Ni ban san komai ba ita kanta Islamiyar ban san ta ba."
Waro idanu ta yi tana bin shi da kallo, kamar shi matashi ace bai ma san ya bambance haram da halal ba ai abin mamaki ne, sake haÉ—e hannu ta yi ta ce "Don Allah bawan Allah ka mayar da ni inda ka daukoni indai har da gaske so na kake."
Kallon ta ya yi yadda take zubar da hawaye sai ta ba shi tausayi, miƙewa tsaye ya yi ya ce "Zan sa a mayar da ke, amma ki sa mijin nan naki ya sake ki mu yi aure." Bai mata damar yin magana ba ya nuna mata hanyar fita, da sauri ta bi hanyar tana addu'ar Allah ya taimake ta kar ya canja ra'ayi ya ce ya fasa mayar da ita. Shi kuwa sai da ya tsiyaya giya a wani babban glass cup Sannan ya bi bayan ta, a palo ya gan ta tsaye wanda suke palon duk basa nan, gaba ya yi ta bi bayan shi har harabar gidan. Suna ganin shi maza uku suka taso ya tsilla wa ɗaya key ɗin mota cikin ba da umarni ya ce "Ku mayar da ita inda kuka dauko ta, ban da gudu ku tafi a hankali kar wani ya yi gangancin yin gudu mai yawa har a jijjiga mata jiki, in hakan ta faru kuma kun san gabar ba sai na ƙarasa ba. Sannan idan kuka kuskura wani a cikin ku ya mata ko da kallon second 5 ne zai ya am shi hukunci, kar wanda ya mata magana dan ita ɗin mallakina ce dole ku daraja ta ku ba ta girma kamar Sarauniya. "Ya faɗa yana ja da baya ya shiga shan giyarsa da ya fito da ita...
Cike da girmamawa suka ce za su kiyaye, ita dai Abir sakin baki da hanci ta yi tana kallon ikon Allah, da auren ta amma ace dole sai ta so wani dan nuna iko. Motar ta shiga suka ba ta wani baƙin kyale mai kauri suka ce ta daure idanunta ganin Ogan nasu a tsaye suna tsoron taɓa ta, ba muso ta amsa da ɗaura amma ya ce su matsa ya iso bakin motar ya ɗaga hannu a kusan fuskarta ya ce. "Baby ki na gani na?"
Girgiza kai ta yi, hakan ya sa ya yi baya ya ba su hannu suka rufe motar. A kan idanuwansa suka bar gidan sannan ya juya ya koma ciki....
Can naisa da Layin su suka sauke ta ta fito ta kunce É—aurin, doguwar ajiyar zuciya ta sauke hango gidansu da ta yi, amshe kyallen suka yi suka yi saurin barin wajan ita kuma ta yi gaba..
Tafiya take da sauri cike da zullumi ganin wasu samari a bakin hanya duk sun zubo mata idanu, a tsorace ta bi gaban su ta wuce wani ya biyo ta yana faÉ—in " 'Yan mata ba ki ji ba."
A fusace ta juyo ta ce "Malam ni matar aure ce." Tana fadin haka ta wuce fuu sai buga sauri take.
Shi ko saurayin a sanyaye ya dawo ya sanar da su wai aure gareta, amma suka ce karya take kawai dai ta ga ta wuce ajinsa ne...
So take ta yi gudu amma ba ta son ciwon ta ya tashi, hakan ya sa ta rage sauri jin ta soma huci da sauri, sai da ta tsaya ta ɗan huta tana addu'ar ta isa lafiya kar ta faɗi a waje, miƙewa ta yi ta iso kofar gidan daidai lokacin ana kiran Sallar magariba..
Da Sallama ta shiga gidan babu wanda ya ji ta duk sun taru suna ta rarrashin Zaiyan, shi kadai ya ji muryarta ta kawo wa majiyarsa ziyara ya zabura da sauri ya miƙe ya kalli kofar gida, da sauri ya nufo ta itama ta nufo shi da sauri suka haɗe a tsakar gidan tare da rungume juna suka sa kuka su duka mai tsuma zuciya.....
_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na (45)
Gabaɗaya da kallo suke bin su cike da tausayawa, ɗago kansa ta yi tana tsayar da nata kukan, shi ma daina kukan ya yi ya sake rungume ta yana ƙanƙame ta tamkar yaron da ya shekara bai ga mahaifiyarsa ba. Lumshe idanu ta yi tana shafa bayansa cikin wani kalar yanayi marar musaltuwa, sake ɗago shi ta yi jin yadda yake matse ta, a hankali ta raba jikinta da nashi ta kamo hannunsa suka ƙaraso wajan su Ta Sakkwato.
Gamboliya ya cire mayafinsa cike da alhini ya ce "Ƴar shawalwala wai ina kika tafi tun da rana? Kin tayar mana da hankali matuƙa."
Dogon numfashi ta ja ta yi baya ta zauna akan tabarmar da Zaiyan ya tashi da ya ganta, suma duk suka zauna kowa ya zuba mata ido yana son jin abin da za ta faɗa. Ta Sakkwato ta dauko mata ruwa mai sanyi ta ba ta, amsa ta yi ta sha kaɗan saboda muguwa yunwar take ji tafi gaban misali har cikinta ya ƙulle, kallon shi ta yi ganin ya kwanto a kafaɗarta ta girgiza kai, sai da Gamboliya ya sake tambayar ta sannan ta faɗa musu cewar sace ta aka yi.
Waro idanu waje duk suka yi Ladidi ya dafe ƙirji yana faɗin "Na shiga uku an fasa aurena! Amma kin tsallake rijiya da baya da har kika kuɓuta daga hannunsu ba su miki komai ba."
Sannu suka dinga jero mata tamkar mara lafiyar da kan gadon Asibiti, ita kuwa ta yi shuru tana sauke numfashi, karshe ma ta tashi ta kama hannun mijinta suka nufi ɗaki jiki a matuƙar sanyaye. Towel ta dauko daga cikin kayanta ta dube shi ganin duk inda ta nufa yana biye da ita, dogon numfashi ta ja cike da gajiyawa da kyar ta iya buɗe bakinta, "Ka zauna zan yi wanka ka ji, kuma kar ka fita waje har sai na fito."
Maƙale kafaɗa ya yi ya amshe towel ɗin ya daga shi yana duddubawa, ganin hakan ya sa ta ja shi suka shige bandakin, ko a ciki ma haka suka yi wanka yana rike da hannunta ɗaya, ita kuwa duk ta gaji ga takaicin riƙe mata hannu da ya yi ta yi ta magana ya sake mata hannu amma yaƙi ji, bayan ta gama shi ma ta taya shi ya yi wanka sannan suka fito.