Sashe 112
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan sati Iman da mijinta suka duro Nigeria, Zaiyan ya ƙagara ya ga wannan mai kama da shi ɗin da Abir ke cewa kamar tasu ta ɓaci. Abdul ya dauko su daga airport suka nufo gida, ɗakin baƙi aka kai Suhal ita kuma Iman ta yo part ɗin su Abir, sun sha kukan yaushe gamo sannan suka fito palo aka soam hira.
Abdul da Salim suka shigo suka gaisa da Suhal sannan suka fita dan su ba shi waje ya ci abinci, ji ya yi a buɗe kofar an shigo, bai ɗago ba dan shi a tunaninsa Iman ce ta zo sai da ya ji sallama ya yi saurin ɗagowa dan ya ga, waye. Haɗa idanu suka yi da Zaiyan wanda ya sha wanka cikin shigar ƙanana kaya sai zuba ƙamshi yake, murmushi Zaiyan ya yi ya ce "Barka da zuwa abokina sai yau ka dawo daga London ɗin?"
Dariya mai hade da mamaki Suhal ya yi sai kuma ya miƙa masa hannu suka gaisa, zama suka yi Suhal ya dube shi yana murmushi ya ce "Welcome back Damisa."
Da sauri Zaiyan ya kalle shi baki na rawa ya ce...
Maman Nusaiba ce*_
[12/14, 9:49 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na 54
"A ina kasan wannan sunan?" Ya faɗa cike da zallar mamaki tare da zama gefen hannunsa na hagu. Aje cup da ya dauko ya yi ya tashi ya iso kusa da shi, hannunsa ya kama ya ƙura masa na mujiya fuskarsa ɗauke da murmushi idanuwansa sun ciko taf da ƙwalla. Hannu ya kai ya shafa fuskar Zaiyan a yayin da hawayen suka samu damar gangarowa kan kuncinsa, shi kuwa Zaiyan cike da mamakin zubar hawayen nasa ya ɗan gyara zama ya ce "Aboki me ya sa kake kuka?"
Kamar jira yake kawai ya rungume shi ya sa kuka mai sauti har da shashsheka, wannan abu ba ƙaramin tayar wa da Zaiyan hankali ya yi ba, yana bubbuga bayansa ya ce "Wai ko dai wani abin Iman ta ce na yi wa Baby ne? Don Allah ka sanar da ni me ya sa kake kuka?"
ÆŠago da kansa ya yi cikin wani kalar yanayi ya kamo hannunsa, sumbata ya yi jikinsa duk ya dauki rawa da kyar ya iya cewa "Alhamdu Lillah Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana da na ga wannan baya naka, Allah na gode maka da ganin wannan rana."
Shi dai baki sake yake kallon shi har ya gama maganar sannan ya gyara zama tare da goge hawaye, murmushi mai sauti ya yi ya ce "Tun ranar farko da na fara ganin ka naji a jikina kai ɗin jinina ne, hankalina kasa kwanciya ya yi har sai da na gan ka tare da princess, kai ɗin Yayana ne jinina uwa ɗaya uba ɗaya suka haifemu ni da kai, Yaya Zaiyan don Allah ka biyo ni mu tafi ka ga alhalinka. " Ya faɗa yana ƙara rungume shi...
Tsabar mamaki Zaiyan ka sa motsawa ya yi sai bin shi yake da kallo, ɗago shi ya yi zai yi magana sai ga Abdul da Salim sun shigo Abir da Iman na take musu baya. Turus suka ja suka tsaya ganin su rungume da juna fuskakinsu na bayyanar da tsananin mamakin ganin su a haka, Abir da ta san komai murmushi ta yi ta nufo inda suke ta tsaya a kan su, haɗe fuska ta yi ta ce "Kai ɗaga min miji kar ka jinyata masa kafaɗa, ƙato da kai ka wani maƙale masa kamar Babyn goye." Ta faɗa tana zama a kusa da mininta. Baki Salim ya riƙe yana kallon Abir jin abin da take faɗa, kada kai ya yi ya ce "Lalle su Baby an zama futsararrun duniya, yanzu a gaban namu kike cewa mijinki?"
Dariya ta yi tana rufe fuska ganin Abdul na kallon ta yana murmushi, sakin juna suka yi Suhal ya goge hawaye yana fante fuskarsa da murmushi, Iman ta zauna a kusa da shi tana kallon shi ta ce "Ya Suhal me ya sa ka yin kuka daga zuwan mu?"
Girgiza mata kai ya yi bai ce da ita komai ba, Abdul ya samu waje shi da Salim suka zauna sannan ya ce "Suhal wai me ke faruwa ne muka gan ku kuna kuka?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Zaiyan Yayana ne shi."
Saurin kallon shi suka yi Salim ya ce "To amma taya ya zama Yayanka? Shi fa ba É—an Niger ba ne a Nigeria yake."
"Tabbas ɗan uwanka ne Suhal, kuma in sha Allah za mu tafi dan na sada shi da iyayensa kamar yadda na yi wa Mama alƙawari zan cika in sha Allah." Abir ta faɗa tana murmushi.
"Sai magana kuke a dunƙule, ki warware mana ta yadda za mu fahimce ku." Cewar Abdul.
"Kamar yadda ka ji na faÉ—a shi É—in Yayana ne ciki É—aya muka fito, idan za ka tuna kwanakin baya da ka duba account É—inka na Facebook da Instagram ba ka ga an yi ma hacking ba? Kuma da ka dawo ka kwato kayanka?"
Jinjina kai Zaiyan ya yi tare da cewa "Kwarai kuwa dan da kyar ma na amso abuna."
"To ni na kwance shi lokacin da ka kamu da rashin lafiya na ci gaba daga inda ka tsaya."
Saurin kallon shi Zaiyan ya yi baki na rawa ya ce "Am.. Amma saboda me ka yi hakan?"
"labarin yana da É—an tsayi zan sanar da ku komai in kun shirya." Suka baza na zomo hakan ya ba shi damar ci gaba da magana.
"A yadda Wazirin kakana ya sanar da ni ni ma zan sanar da ku dan ku tabbatar da Zaiyan ɗan'uwana ne. Babana asalin sunanshi shi ne Abdulwahid, shi ne ɗa na farko ga sarki Zaidu. Sarki Zaidu yana da mata biyu mahaifiyar Abdulwahid mai suna Sarauniya Zuwairiya ita ce ta farko, wadda ta kasance ita ba jinin Sarauta ba ce, hakan ya sa take fuskantar ƙalubale iri-iri a cikin masarautar. Tun da ta haifi Abdulwahid ba ta sake haihuwa ba sai abokiyar zamanta mai suna Fulani Abida ita ta dinga haihuwa, yaranta biyar hudu mata ɗaya namiji mai suna Haris wanda yake ɗa na biyu a wajan Fulani. Haka suka girma in da kullum cikin gori da faɗa wa Sauraniya bakaken maganganu take, duk abin da ake yi Saurniya Zuwairiya ba ta taɓa ce musu uffan ba dan har uwar mijinsu sai da suka kulla makirci ta tsane ta, babu mai son ta sai mijinta haka ta daure ta ci gaba da rayuwa.. Abdulwahid na zama cikakken Saurayi ya gama karatunsa wanda ya karkata kan kasuwanci, Sarki Zaidu bai so hakan ba dan shi abin da yake so Abdulwahid da ya gama karatu ya fito da mata ayi masa aure zuwa wani lokacin ya sauka ya ba shi kujerar, amma ba yadda ya iya haka ya rabu da shi ya bar shi ya soma kasuwanci. Sosai hakan ya yi wa fulani Abida daɗi dan ba ta so ace ya nuna yana son mulki, dan haka ta dinga zuga ɗanta Haris akan kar ya bari ace za a ba wa Abdulwahid Saurata, idan har aka ba shi shi kuma ya zama fanko. Hakan ya yi tasiri a zuciyarta Haris ya ƙulla gaba da Abdulwahid wanda bai ma san yana yi ba dan shi ta ksuwancinsa yake, kasashe daban-daban yake zuwa yana sayo kaya kama daga kan atamfofi kala-kala, kayan maza Jallabiya da ƙananan kaya, takalma kala-kala na maza da mata. In takaice muku dai babban campany ya buɗe in da ya zuba masu kula da komai, Sauraniya sai ta ji daɗi da ɗan nata bai ƙwallafa rai a kan wannan sarauta ba, hakan ya sa take ƙara ƙarfafa masa gwiwa wajan ganin kasuwanci sa ya haɓɓaka a ko'ina a faɗin Niger da ma kasashen da ke maƙotaka da su suvsan wannan campany na Abdulwahid..
Ganin ya zama cikakken matashin mai kuɗi sai abin ya hana Fulani Abida sukoni, ta dinga bin malamai da bokaye tana son a lalata wannan sana'a tasa ya daina samun customer, amma duk ina taje ba ta samun nasara sai su ce mata ai Abdulwahid na tare da tsari, sannan akwai wata Aljana da ke tare da shi tun da ya zo duniya take jikinsa ba ta bari a cutar da shi, idan kuwa mutum ya dage sai ya cutar da shi to fa takan yi fata-fata da mutum. Hankalin Fulani Abida ya tashi amma saboda sheɗan ya mata futsari a kai ba ta daina bin bokaye ba, har Allah ya ara mata rana ta aika Jakadiya can yankin Mali wajan wani ƙasurgumin boka, bayan ta masa bayani ya ce ai aljanar ya san ta zai saka ta a gwalba kuma aiki kamar an yi an gama ta faɗi me take so. Jakadiya ta ce a sa Abdulwahid ya bi duniya ya lalace kar ya sake waiwayar ahalinsa, ya ce an gama ta aje masa maƙudan kudade ta dawo wa da Fulani albishir mai daɗi, ranar sai da ta mata kyauta mai tsoka tace in aiki ya ci za ta ba ta sarƙar daham mai kimanin kuɗi naira miliyan biyar.