← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 120

Sashe 120

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin Abir sai ƙara girma yake zama da kyar tashi da kyar, ba ta yin komai sai dai ta wanke goma ta sa biyar komai sai an yi mata motsa jiki kaɗai take yi safe da yamma. Zaiyan ya soma fafutukar neman aiki irin nasa aka je aka masa takardar ɗan ƙasa, bai sha wahala sosai ba kasancewar sa jinin sarauta, ya samu takardunsa na makaranta a wajan abokinsa Bashow ya nuna suka tabbatar da ingancin ilimin da ya samu sannan suka ba shi aiki. Mamma ta hana shi amsar aikin amma Mai martaba ya ce ta rabu da shi in lokaci ya yi zai aje aikin, ba dan ta so ba ta rabu da shi. Zaiyan ya ɗauko Abir suka zo Nigeria ziyara, dama kafin ya zo ya yi magana da Abdul yana son gida mai kyau zai saya suna isa daret gidan su Baba suka aje, gaisawa kawai suka yi ya ɗauke su da komai nasu suka nufi sabon gida, ya ɗauko musu maigadi da masu aikin cikin gida, sun sha murna sosai ya ba wa Baba kuɗi har ma da Inna. Kwana biyu suka yi a Yola suka nufi Kano in da suka fara dira gidan su na haya, Tasakkawato kamar ta goya Abir sai kiran matan gidan take tana faɗin "Ku zo ku ga Jiddo."

Duk fitowa suka yi kowa sai murnar yake na ganin Abir, ta gaisa da su tana kallon kofar É—akin su Ladidi ta ce "Wai Mama ina Gamboliya da Ladidi?"

Riƙe baki Tasakkawato ta yi ta ce "Waɗannan ai kwarakwatar tsiya na Jiddo, sun je sun tabo wata karuwa ta sa an zo har gida an kama su, yanzu haka suna can wajan police."

Cike da jimami ta sa aka kai ta Police station É—in ta yo belin su ta yi ta musu faÉ—a karshe ta dawo yi musu nasiha, duk jikinsu ya yi sanyi suka ce mata sun tuba sun daina shigar mata za su dawo asalin su na maza, Abir ta ji daÉ—i sosai ta ba su kuÉ—i masu kauri ta ce su ja jari su koma gaban iyayensu. Ta sha addu'a sosai har kuka suka yi.

Abir tasa Bashow ya nemo mata gida mai kyau ta saya wa Tasakkawato da mijinta, ranar Tasakkawato ta sha kukan murna tana jero musu addu'a zaman lafiya suna amsawa da Amin. Kwanan su biyu a Kano suka wuce Niger...

Wata ranar Asabar cikin dare Abir ta kama nakuÉ—a suka nufi asibiti ta ita, cikin ikon Allah ta haifo yara biyu duka mata. Ranar ko nurses É—in asibitin sun san an haifi jikokin sarki Abdulwahid,sun sha kyautar kuÉ—i, haka aka gyara ta da yamma suka dawo gida..

Haka aka dinga sanar da 'yan'uwa da abokan arziki kowa na taya murna, ana ya gobe suna 'yan Nigeria kwainsu da ƙwarkwatarsu suka yo Niamey. Da dare Zaiyan ya lalleɓi Abir ta ɗauko masa yaran ita da Ikilima suka kawo masa ɗakinsa, Ikilima ta tafi ta bar su tana cewa Abir kar ta jima Mamma ta neme ta ta amsa da to. Kallon yaran yake masu kama da shi yana shafa su, janyo ta itama ya yi ya rungume cikin zallar ƙaunar ta ya ce "Baby kin gama min komai a rayuwa, ban san da me zan saka miki ba da wannan yara da kika haifo min su kyawawa, hakan ya sa ni ma zan miki wata bazata." Ya faɗa yana murmushi.

Ɗago kai ta yi ta kalle shi cikin wani kalar yanayi na shaukin son mijin nata ta ce "Nima ka gama min komai a rayuwa Nury, Allah ya ƙara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma wata kyauta ce za ka ba ni?"

Murmushi ya yi mai kayatarwa ya kama kumatunta ta ce "Na samo dangin su Mamma yanzu haka da su za ayi bikin sunan nan."

Da wani irin sauri ta kalle shi ya jinjina mata kai, saurin tashi ta yi a jikinsa tana dariyar farin ciki ta gyara hijabinta ta ce "Ina zuwa Nury bari na kira Mamma ba zan ji wannan abin farin cikin ba ni kaɗai." Ba ta tsaya ta ji me za ce mata ba ta wuce da sauri, bin bayanta ya yi da kallo yana lumshe idanu.. Ba ta fi minti uku da tafiya ba sai ga su sun dawo tare da Mamma da Suhal har Ikilima, Mamma ta dinga tambayar ya faɗa mata in da suke ta je ta gan su." Ganin duk Mamma ta ruɗe sai ya ɗauki yaran ya gyara gadon ya kwantar da su ya musu addu'a duk suna tsaye sannan ya ce su je, ya yi gaba suka bi shi baya har zuwa wani sashe na ɓangarensu ya buɗe wata kofa ya shiga suka mara masa baya. A zaune suka samu Kawu Sale da wasu mata uku.

Mamma da su Kawu Sale sun sha kuka Sosai ƴar'uwar mahaifiyar su Mamma ta goge hawaye ta ce "Naje Kano sau uku yan unguwar suka ce min ƴar'uwata ta rasu ku kuma ba su san a ina kuke ba, na nemi Baba Malam shi ma aka ce mijin Hassana ya zo ya dauke shi, ku yi haƙuri ku yafe mu Usaina babu kalar neman da ba mu yi muku ba a Kano amma ko labarin ku ba mu samu ba har muka gaji ni da Sale muka dawo Maradi.. " Mamma ta ce "Ba komai Mama ba ku yi mana komai ba, Kawu ina wannan ƙanwar taku?" Ta faɗa tana kallon Kawu Sale. Da hannu ya nuna mata matar da ke gefen shi, suka rungume juna suna ta kuka, Mamma ta ɗago ta sanar da su duk wani abu da ya faru da su tana yi tana kuka. Sun sha hira sosai Zaiyan ya koma ya ɗauko musu jariran suka sa musu albarka, sai da suka kusan kwana suna hira Mamma na kusan Kanwar mahaifiyarsu....

Washe gari aka yi suna lafiya, Hassana ta ci sunan Mom Husaina ta ci sunan Inna Asabe Ba dariya, an sha taro an tashi lafiya kowa sai yaba kyan yaran yake. Washe garin suna su Grandma suka haÉ—a kaya suka ce kuma sai in Iman ta haihu itama cikin ya soma girma, Abir ta ce in Hafsat ta haihu za ta zo suna haka dai suka rabu..

Haka aka ci gaba da kula da 'yan biyu kyautar Allah su da Mamansu har suka yi arba'in ya yi daidai da kwana biyar da haihuwar Hafsat, Abir ta shiga zaga dangi ta fara zuwa maradi ta ga dangin su masu yawa suka mata tara da arziki ta dawo, washe gari ta wuce Nigeria. Har Ruga ta je suka zaga dangi suka je gidan su Baba Inna na ta murnar ganin su, ta wuce gidan Baba Malam suka gaisa sannan ta dawo gida. Ana gama suna da kwana uku Zaiyan ya zo ya É—auke a barsa suka koma gida..

Sai da 'yan biyu suka yi wata hudu Iman ta haifi É—anta namiji, an sha murna sosai aka dinga kula da su ranar suna aka sa wa yaro sunan Abie Abir na jin an faÉ—i sunan yaron ta yi ta kukan farin ciki ta je ta rungume Iman tana mata godiya, murmushi Iman ta yi ta ce "To meye na yin godiya na ga dai Abie ni ma Daddyna ne ko?".

Dariya Abir ta yi suka ci gaba da hira.

Sarauniya Bilkisu ta ga dai in ta sake za ta yi abin da zai sa sarki ya sake ta sai ta watsar da komai ta je nemi yafiyar mijinta da Mamma, suka ce sun yafe mata itama Kilishi ta nemi yafiyar su suka yafe mata, sosai Mamma ta ji daɗi na canjawar kishiyoyin nata.. Sultan ya dage shi Khairat yake so aje a tambayo masa auren ta, Mai martaba ya sa aka je nemo masa auren Khairat su Daddy suka ce su ba su da matsala a sanar da mahaifinta, Malam da suka je wajan shi da magana ya ce shi babu abin da zai ce duk abin da suka yanke daidai ne, nan ya ƙara neman yafiyar Daddy ya ce bai masa komai ba ya yafe masa. Salim na ganin haka ya ce to shi yana son Ikilima, abin ya musu daɗi aka haɗa ranar auren gabaɗaya...

Lokacin aure na yi aka shiga hidimar biki, Abir ita da Iman ba sa zama hidima ta yi yawa, bayan an gama biki aka kai amare gidanjensu lafiya..

*BAYAN SHEKARA BIYAR*

A tsakanin wannan shekarun Abir ta sake haihuwar wasu yan biyun maza, sosai Zaiyan ya yi murna. An yi wa Fatima da Yasmin aure suma, Khairat da Ikilima duk sun haihu..

Cikin nutsuwa ya ke tafiya fadawa na take masa baya har ƙofar ɓangarensa, hannu ya ɗaga musu suka tsaya ya shige su kuma suka koma. A palo ya samu yaran sun ciccira pilows ɗin kujerun palon, Badariya da Sadiya suna gefe Hassan da Husain ne ke ta watsi da komai na palon, suna ganin shi duk suka yo wajan suna faɗin "Abba sannu da zuwa."

Murmushi ya yi ya ce "Yawwa yaran kirki ina Mamanku?"

Sadiya da ke gefen shi ta ce "Ta shige É—aki ta ce mun dame ta."

Murmushi ya yi ya miƙe suka nufi ɗakin. Akan gado suka same ta kwance tana kallo a waya, ganin su ya sa ta daure fuska ta ce "Duk ku fita nan ɗin ma sai kun shigo kun lalata da ba ku jin magana?. Rakuɓewa suka yi a bayan Zaiyan suna miƙo kansu suna kallon ta. Dubara ya musu ya ce su tafi waje zai rarrashe Mama suka fita da sauri. Kayan jikinsa manyan ya cire ya bar na ciki ya hayo gadon, kwanciya ya yi ya janyo ta yana ƴar dariya ya ce "Anty yunwa nake ji."

Dariya ta yi tuna baya ya ja musu bargo yana faÉ—in "Mu yi bacci kafin su Abie su dawo É—akin nan."

Murmushi ta yi ta ƙara shegewa jikinsa ta lumshe idanu....

Tammat bi hamdu Lillah anan na kawo karshen wannan littafi mai suna A HAKA NAKE SON SHI, kuskuren da ke cikin sa Allah ya yafe min, abin da na rubuta daidai Allah ya ba ni ladan da ni da ku maru karatu waÉ—anda suka dauki darasin ciki suk, yi amfani da shi. Mu haÉ—u da ku a littafina mai suna *ANDIZO* Ku da jin sunan ma kun san akwai nishadi a cikin labarin, mu tara da ku a sabuwar shekara in sha Allah bissalam my lovely fans Ina yinku..

_Maman Nusaiba ce_
Chapter 120 · 0% Book details