← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 120

Sashe 34

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fita sai da suka gaisa da Maigadi da sauran ma'aikatan sannan ta shiga suka tafi..

Suna zuwa Ali ya aje ta a ɗan naisa da gidan suka ƙarasa da ƙafa, ita dai mamaki take da an zo kusan gidan sai a aje ta ba za aje har ƙofar gidan ba sai su tsaya a baya. Sai da ya kaita har ƙofar palo sannan ya dawo ita kuma ta sa kai ciki bakinta ɗauke da Sallama..

Yana tsaye a tsakiyar palon ya ji muryarta, saurin juyowa ya yi yana kallon ta. Itama shi take kallo cikin wani kalar yanayi mai wuyar fassara, sosai ta yi missing ɗin shi har ba ta san lokacin da hawaye ya zubo mata ba, kafin ta motsa daga bakin ƙofar sai ji ta yi an rungume ta, kwalalo idanu waye ta yi cikin kiɗima zuciyarta na wani irin bugawa wanda tun da take ba ta taɓa jin wannan yanayi ba sai yau. Wani irin nauyi harshenta ya yi ta kasa furta maganar da take son faɗa, lumshe idanu ta yi cikin kasalalliyar murya ta ce.....

Taku har kullum Maman Nusaiba ce.

[10/17, 12:52 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): Shafi na (18).

Cikin kasalalliyar murya ta ce "Zainnn..!" Ta ja sunan jin ya sakar mata nauyinsa, tsoro da firgici suka kawo mata ziyara a tare. ƙin sakin ta ya yi yana fitar da wani irin numfashi, a kiɗime ta soma ƙoƙarin janye shi daga jikinta amma ta kasa. Jin abin na ƙaruwa ta ƙara shiga tashin hankali, ta daddage ta ɗago shi ta soma ƙoƙarin isa kan kujera dan ta zaunar da shi, amma ta kasa kasancewar Zaiyan ya mata nauyi. Da kyar ta iya jan kafa daya tana kiciniyar raba shi da jikinta sai suka zube a kasa warwas, lumshe idanu ta yi tana jin bugun zuciyarta ya ƙara tsananta, haka kawai ta ji kamar ana kiran sunan Zaiyan cikin majiyarta ta yi saurin buɗe idanu ta sauke shi à kan shi. A zabure ta tashi daga faɗuwar da suka yi sakamakon ganin Zaiyan na fitar da wani irin farin kumfa daga bakinsa, ta shiga jijjiga shi a ruɗe tana kiran sunanshi amma sai kakkafewa idanuwansa suka yi a lokacin, hannu ta ɗaura a ka ta tashi zaune ta soma neman su Baba.

"Baba!" Ta faɗa da ƙarfi cikin rashin sanin madafa, sai ta fashe da kuka tana surutai irin na wanda ya fita daga haiyaci.

"Waiyo Allah! Ka tashi don Allah Zain kar ka tafi ka barni, Baba kuna ina Wai? Inna! Ka tashi ka ji." Ganin ba sarki sai Allah ya sa ta miƙe ta nufi kitchen da sauri har tana haɗawa da gudu, ruwa ta ɗauko a cikin cup tana sharɓe majina ta ƙaraso inda yake. Ruwan ta shafa masa a fuska tana dan bubbuga kumatunsa amma shuru ko gizo bai yi ba, rausayar da kai ta yi tana son tuno wata dabarar da za ta mishi ko ya tashi. Ji ta yi ya damƙi hannunta ta yi saurin kallon shi cikin rawar murya ta ce "Z.. Za.. Zaiyan." Wani irin huci yake fitarwa yana ƙara damke mata hannu ita kuma ta zuba masa idanu tana zubar da hawayen tausayin shi, hannu ta sa ta tallafo kanshi ta ɗaura à kan cinyarta tana shafa kan shi shi kuma sai wani irin gurnani yake yana zabura kamar yaron da damina ta warta.

Sun fi minti 20 da haka ta rasa yadda za ta yi da shi, ta kira su Baba ya fia sau a ƙirga amma shuru hakan yasa ta gane cewa ba sa ma gidan, can dabara ta faɗo mata ta janye shi daga kan cinya ta dauƙi cup ɗin da gudu ta koma kitchen ta ɗauko ruwa rabin cup ɗin. Zama ta yi ta dan nutsu ta soma karanto addu'o'i tana tofawa a cikin ruwan tana yi idanunta a kan shi yana ta zabura yana ƙanƙame jiki, bayan ta gama ta yi bismillah ta soma shafa masa ruwan addu'ar. Zafi sosai jikin nasa ya ɗauka duk inda ta shafa masa ruwan addu'ar sai ya ƙara zafi fiye da na da, hakan bai sa ta karaya ba ta ci gaba da shafe masa ruwan sauran da ya rage ta ɗago kansa ta soma zuba masa à kai tana cuɗa sumars wadda take baka siɗik. Karkarwa jikin ya ɗauka idanunsa na ƙaƙƙafewa wani baƙin abu na fita daga bakinsa, kuka take tana ƙara shafa kan nasa ji take kamar ta kurma ihun neman taimako amma to wa zai ma san ta yi ihun ? Gabadaya ta ma manta da ta kira ko da Abdul ne komai ya kunce mata ta tasa shi gaba tana kallo tana kuka..Zafi jikin nasa yake ƙara yi ita kanta zafin ji take kamar tana gaban wuta, saurin gyara masa kwanciya ta yi ta soma karanto masa Suratul yasin cikin ɗan ɗaga murya. Nan-da-nan ya soma Karkarwa yana yin wani irin ƙara baƙin abin nan na fita daga bakin , ganin yana ɓari jikin ta yi saurin janyo shi ta rungume tana kuka tana ci gaba da karantun, tana gama kai karshen surar ta kamo Suratul Iklas zuwa Nas, tana gamawa ya sarƙe da tari yana riƙe wuya tare da buɗe idanunsa yana mayar da su ya rufe. Tashin shi ta yi zaune tana jera masa sannu, juyo da shi ta yi tana shirin yi masa magana sai kawai ya wanke ta da amai, riƙe shi ta yi ya dinga yin aman yana nishi kamar zai amayo da 'yan hanjin cikinsa, bayan ya gama ta yi baya da shi ta kwantar ta tashi cikin dabara ta tattara rigarta da ya amaye ta nufi toilet.

Tana shiga ta wanke wajan da ruwa, har za ta juya ta ga omo à gefe ta janyo ta zuba ta wanke tas sannan ta fito. Ta kusa karasowa inda yake ta ji an ɗauke wuta ɗik, da sanɗa ta iso tsakiyar palon tana lalibe har ta ji ta yi tuntuɓe da shi ta sunkuya ta zauna tare da janyo shi tana kiran sunanshi.

"Antyyy!"

Ta ji sautin muryarshi ta daki dodon kunnenta, da hanzari ta amsa, "Na'am Zaiyan tashi ka zauna." Ta faɗa a sanyaye tana lalibo hannunsa. Doguwar jiyar zuciya ya sauke ya yunƙura ya tashi zaune tana riƙe da hannunsa, jingina shi ta yi da jikinta ta daura kanshi à kafaɗarta..

"Hauwa'u Maijidda..!"

Ta yi ji an kiran sunanta Wanda ba kowa ma ya san sunan ta haka ba, a ruɗe ta waiwaya inda ta ji an kira sunan tana zare idanu a cikin dubu. Taku ta ji ana yi ana doso inda take ta ƙanƙame Zaiyan Wanda ya yi laƙwas a jikinta ta rufe idanu gaban ta na faɗuwa..

"Hauwa'u Maijidda."

Aka kuma kiran sunan ta ta buÉ—e idanu jin muryar a gaf da ita, tuni ta soma rawar jiki tana faÉ—in, " Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Allahuma ajurni fi musibati wa akalifili khairan minha. A'uzu billahi minan shedanu rajim." Haka take ta maimaitawa a kiÉ—ime.

"budÉ—e idanuwanki Hauwa'u Maijidda."

Ta kuma ji an faɗa a gefen ta, à hankali ta bude idanu tana addu'ar neman kariya daga abin da yake kiran sunan ta, kwalalo idanu waje ta yi cikin tashin hankali sakamakon yin arba da wata doguwar mace fara sol sanye da fararen kaya, zaune take a kan kujera fuskar nan a daure tamau ba alamun rahama, saurin rungume Zaiyan ta yi kamar za ta shige jikinsa ta soma magana "Na haɗa ki da girman Allah karki cutar da mu baiwar Allah." Ta yi maganar tana ɗan kallo kan kujerar sai ta ga wayam ba kowa. Da sauri ta tashi Zaiyan ya riƙe mata hannu ya ce " Anty bani da kowa sai ke."

Baki buɗe take kallon shi cike da al'ajabin abin da ya faɗa, gani take kamar wannan macen da ta gani ce ta faɗi maganar, yau wai Zaiyan ne ke cewa ba shi da kowa sai ita? Duk da shi ɗin ba mai hankali ba ne amma kalmar ta daki zuciyarta matuƙa, sosai wani tsananin tausayin shi ya kamaye mata gangar jiki da ruhi ba ta san lokacin da hawaye suka zubo mata ba sai da ta ji yana goge mata ta ankare, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙifta idanu tana masa wani irin kallo mai wuyar fassarawa a baki. Tuna abin da ta gani ya sa ta yi saurin waigowa ai kuwa ta ganta zaune da inda ta ganta da farko, wannan karon fuskarta ɗauke da damuwa tana zubar da hawaye abin ya ba wa Abir matuƙar mamaki. Tunani take to ita wannan ɗin mutum ce ko aljana ?

"Ka da kiji tsoro Maijidda."

Maganar matar ta katse mata tunanin da take, cike da tsoro ta kuma kallon ta ta ce "Baiwar Allah ke wace ce? Kuma me kike nema a gare mu ?"

Murmishi ta ga ta yi tasa gefe farin mayafin nata ta goge hawayen da suka zubo mata, hannu ta ɗaga sama kaɗan sai ga wuta ta dawo haske ya gauraye palon. Sosai Abir ta gigice da ganin kyan matar, dafe ƙirji ta yi tana ƙura mata idanuɓ

"Babu abin da nake nema a gare ku Maijidda, sanin ni ko wace ce ba yanzu zan sanar da ke ba sai zuwa wani lokacin in na sake haɗuwa da ke." Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta juya mata baya.. Sai à lokacin Zaiyan ya ɗago ya kalli matar, baki ya saki yana nuna wa Abir ita da hannu ya ce, "Anty wannan Maman ki ce ?"

Jin abin da ya fada sai matar ta juyo tana murmishi, waro idanu ya yi yana rufe baki ya ce "A a ga Maman Anty ta zo." Ya faÉ—a yana gyara zama.

Ita kuwa Abir kallon su kawai take, gani ta yi matar ta matso kusa da su ta dafa kan Zaiyan tana kallon shi ba ta ce masa komai ba. Tsoro ya kuma dabaibaye Abir baki na rawa ta ce "Don Allah karki cutar min da shi amana ce Allah ya bani."
Chapter 34 · 0% Book details