Sashe 108
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin haka ya sa suka dinga dukan mu har sai da muka daina motsi sannan suka rabu da mu, muna ɓude ido muka gan mu a wani ɗaki inda Umma ta ce Abie ya aminta da ita za ta yi wa Daddyn Aruf dabara ya sake mu, shi kuma ya ce ya gambace ya mutu da ya aikata zina, ni ma na ce da Abie da ya amince mata gara su kashe mu gabaɗaya...
Ban san iya adadin Kwanakin da muka yi ba a wannan baƙin gida, da niya suke zuwa su sa yaransu su dinga dukan Abie ni kuma su kaini gaban masu shan shisha idan sun zuko hayaƙi su fesa mini a fuska, haka ciwona zai tashi na yi ta tari ina riƙe ƙirji sai sun ga na suma sannan su zuba min ruwa na farfado tukun su shaƙa min magani na dawo daidai.. Kullum haka ake mana suka yi ta gana mana azaba amma Abie ya ce ba zai ba su komai ba, ana haka wata rana suka yo copy takardun kadarorinsa suka ce sai ya sa hannu, ya ce ba zai sa ba Daddyn Hafsat ya fusata ya buga masa kai da bango kan fashe yana da jini, na kwashi kuka suka hana na yi haka na rufe bakina ina kallon Abie kwance kamar gawa. Washe gari suka dawo yana jin jiki ga sun hana mu abinci suka ce ya sa hannu ya ce ba zai sa ba ai dukiyarsa ce ba ta wani ba, akan me za su nemi kwace masa duniya? Sosai suka fusata sai suka hana ake bamu abici sai dai a zuba gishiri a cikin ruwa a ba mu mu sha. Ranar kwana na uku mun galabaita suka manta ba su rufe kofar ba Abie ya lallaɓa ya ga ba kowa duk sun sha giya bacci ya kwashe su, ya ce mu fita.. Ɗaya daga cikin su ya motsa ya tashi zaune har mun je baƙin kofar fita Abie na ganin haka ya yi saurin turani waje ya ce na yi maza na samu na bar wajan na boye, haka ina ji ina gani na tafi na bar Abie a cikin wannan yanayi na tsakanin mutuwa da rayuwa. Har na ɗan yi nisa naji muryoyinsu na shige gefen hanya jikin wata bishiya na rakube ina sauke numfashi na azaba, sai da naji sun koma na fito na ci gaba da tafiya da ɗan kuzarin da ya rage min sai jiri nake ji.. Ina tafiya ina kuka har na iso bakin hanya na kasa samun mota saboda lokacin ko tsuntsu ba ya motsi talatainin dare ne, na ci gaba da bin gefen hanyar ina tafiya har gari ya waje ban yi rabin isa kusa gari ba ma ballantana na ce na tsira, ina tafiya ina hango gari amma na kasa isa tun safe har rana ta take, wata Ruga na gani na isa ina haki na ce su taimaka min da ruwa, ganin yadda jikina yake sai suka ban ruwa suna yin baya-baya da ni suna ce min lafiya? Na ce musu sace ni aka yi shi ne na gudo, ruwan na sha kaɗan naji cikina ya ƙulle na isa inuwar da ke gidan nasu na zube anan ina mayar da numfashi. Mai gidan ya sa aka yo Kunu mai ɗumi suka tashe ni na sha shi ma ba me yawa ba saboda yunwa ta riga ga da ta dira min ciki, na kwanta suka sani a gaba suna min sannu har bacci ya kwashe ni na walaha, ban farka ba sai La'asar suka nuna min banɗaki da ƙyar na yi Sallah a zaune, bayan na gama na ce zan tafi na musu godiya suka ce na tsaya na samu lafiya za su kaini da kan su, amma na ce musu na gode dan ba na son su biyo ta kan gidan su same har na jaza musu, haka na juya na hau hanya lokacin da ɗan kuzarina na dinga tafiya dan na rasa motar da za ta dauke ni duk wanda na tsayar ba ya tsayawa. Sai da na shigo gari ina ta son tare mota kawai naji ana cewa "Ga ta can ku bi ta."
Na kwasa a guje ban taɓa yin gudun da na yi ranar ba, na karyo wata kwana na shigo wata Unguwa na rasa ina zan nufa sai na bi wajan wata bola zan tsallama na faɗa wani kango dan na buya sai na kasa, suka tarar da ni a wajan saboda na taka wani danƙo. Da suka kaini wannan kango suka shaƙa min maganina ganin ciwona ya tashi saboda gudun da na yi, sun so su min faɗe sai Allah ya dube ni da idanun rahama ashe a lokacin Zaiyan yana nan a kwance cikin wannan kangon sautin kukana ya tashe shi a bacci, inda ya musu duka har suka sare shi a lokacin.." Ta ƙarashe maganar tana kallon Zaiyan da shi ma ita yake kallo..
Kowa ya yi tsit in ban da kukan Grandma da su Fatima babu abin da kake ji, har Abdul ya yunƙuro zai yi magana ta ɗaga masa hannu tare da cewa "Bayan na dawo gida Umma da Daddyn Aruf suke ta yi min barazana akan in na sanar da wani abin da na gani za su kashe Mom, haka zan sha kuka na gode Allah karshe ma video suke yi wa Abie suna azabtar da shi su turo min, shi kuma Abie zai yi ta cewa kar na kuskura na yarda dan na ga wannan vidéo da suke masa suna turo min na miƙa wuya na ba su abin da suke so, karshen da suka ga naki ba su abin da suka nema suka kashe Abie suka jifo gawarsa bakin hanya, wanda aka same su a tare da Zaiyan. Shi kan shi Zaiyan a lokacin su ne suka sace shi suka masa wani abin.. "
Kuka ta fashe da shi ta kalli Umma ta ce "Yanzu sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha kun kashe min iyaye.."
Babu abin da kake ji sai muryar Grandma da take jero wa Umma tsinuwa, Ammi ta miƙe tsaye ta isa gaban Umma ta zabga mata mari tana kuka ta ce "Wallahi kun yi asara a rayuwar ki, dama ke kika zugani nake tsangwamar Abir ashe da abin da kike aikatawa bayan haka? To ki jira Wallahi za ki ga ƙarshenki yadda zai kasance fasiƙa azzaluma."
Daddy ya ce ya saki Umma saki ɗaiɗai har uku kuma bai yafe mata cin amanarsa da ta yi na kawo masa ƙato kan gadon aurensu na sunnah suka aikata zina, ihu Umma ta kurma ta yi kukan kura ta damko Abir ta kai mata duka a ruwan ciki.
Wani kalar azababben ƙara Abir ta ƙwalla wanda har sai da jijiyoyin kanta suka fito ta ƙanƙame hannun Zaiyan, Abdul ya zo ya damƙi Umma ya kifa mata mari ya hankaɗa ta ta yo baya ta faɗi, kafin ta motsa ya yi saurin ciro ankwa ya goya hannunta ta baya ya ɗaura masa..
"Ki ka tona min asiri sai na kashe ki É—iyar mayya." Umma ke faÉ—a Abdul ya tura ta waje ya saka ta a mota ya ce da Ali su kaita su kulle a É—aki wanda ake tsananin horo sannan ya dawo ciki.
Zaiyan duk ya rikice ya É—ago da ita sai yarfa hannu take tana faÉ—in "Waiyo Yaya zan mutu ciki, Waiyo Allah.."
Kafin Ammi ta É—ago da ita sai ganin jini suka yi ya soma malalauwa daga jikinta, hankalinsu a mugun tashe Zaiyan ya amshe ta daga hannun Ammi ya fita da ita da gudu Abdul da Ammi suka biyo su baya. Mota duk suka shiga Abdul ya ja a guje suka nufi Asibiti........
_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na 53
Kafin su isa Asibiti sai da ta suma sau uku tana darfafaɗowa, hankalin Zaiyan ya yi mugun tashi ga jinin da yake zuba kamar an ƙara masa gudu. Suna isa Asibiti aka fito da gadon ɗaukan marassa lafiya a daura ta, amma Zaiyan ya ƙi su taɓa ta ya dauke ta da sauri suka nufi ciki norses ɗin na biye da shi har ɗakin emergency, ƙin fitowa ya yi suka yi ta fama amma ba ce ba fa zai fita ya bar matarsa ba, sai da Abdul ya shigo ya janyo shi yana ba shi baki tukun ya fito. Kasa zama ya yi sai safa da marwa yake yana jinjina kai, shi kansa Abdul ya bala'in shiga damuwa ganin ƙawar tasa kuma amanarsa a wannan yanayin, Ammi ta yi tagumi ta zuba wa ƙofar ɗakin idanu...
Suna nan zaune sai ga su Fatima duk sun iso, Khairat kuwa har yanzu ba ta daina kuka ba sai jero wa Umma Allah ya isa take tana nanata kalmar ita ba ɗiyar gidan ba ce. Ko nan da can ba wanda ya motsa ya je duk sun zauna ba e ba a'a, sai da suka ɗauki kusan minti 45 sannan aka buɗe ƙofar, duk suka yi saurin tashi suna rige-rigen tambayar Doctor Hashim. Kallon su ya yi sai kuma ya dubi Abdul ya ce "Aboki ina mijin nata? Ko da yake shi ba zai ma gane ake nufi ba kai zo muje." Ya faɗa yana yin gaba sai ya ji an damƙo shi ta baya, da sauri ya juyo suka haɗa idanu da Zaiyan wanda idanuwansa suka yi jajur saboda tashin hankalin da yake ciki, sai da Doctor Hashim ya ji tsoro ganin yadda yake kallon shi ya dauka duka zai kai masa, amma ya ji ya sake masa riga ya nisa ya ce "Ni ne mijinta muje tare da Yaya Abdul sai ka mana bayanin, wa ma ya ce maka ba zan gane bayanin da za ka yi min ba?" Ya faɗa yana ɗaure fuska tare da hararar shi. Saurin yin gaba Doctor Hashim ya yi yana jin gabansa na faɗuwa yadda Zaiyan ɗin ke masa magana, su Ammi suka zauna a nan su kuma suka mara masa baya zuwa office ɗinsa. Bayan sun zauna ya gama rubuta komai ya ɗago ya dube su, a nutse ya fara faɗin "To Alhamdu Lillah mun yi nasarar ceto rayuwarta.."