← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 120

Sashe 86

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikinta ne ya yi sanyi zuciyarta ta raunana sai yanzu take tuna irin kuskure da ta dinga tafkawa, É—ago da kai ta yi ta ce " Am so sorry Yaya Suhal, ba zan sake cewa ka sakeni ba in sha Allah, amma ka faÉ—a min ina Sajida take?"

Wani sanyi ya ji ya ratsa zuciyarsa ya yi ajiyar zuciya ya ce "Sajida ai ta rasu tun lokacin da muka dawo gida da sati biyu, kawai dai naƙi faɗa wa Princess ne ganin hali da take ciki."

Da sauri ta ɗago ta kalle shi baki na rawa ta ce "Wa.. Wai Sajidar ce ta rasu? Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Allah ya jiƙan ta da rahama."

Amin ya ce ya kalli Agogo ya yi fuskar tausayi ya ce "Yanzu haka saura minti 20 a fara taron nan ga shi kin tsare ni da rigimar nan taki, muje na miki wanka ko na tafi."

Turo baki ta yi sai kuma ta yi saurin faÉ—in "Amma me ya sa ka ce min ka aureni ne dan ka tseratar da rayuwar Anty Baby? Don Allah ka bar ni a duhu ka sanar da ni dalili ko zuciyata za ta samu salama." Ta faÉ—a tana marairaicewa kamar za ta sa masa kuka.

Ce mata ya yi ba yanzu ba amma wani lokacin zai sanar da ita komai da ya shafi rashin auren Yayarta ta, ba dan ta so ba ta haƙira suka shige toilet ya mata wanka sai mita take wai ba shi da kunya, murmushi kawai yake dan ya lura ita rashin kunya da kauɗin bakin nan a jininta yake. Bayan ya gama shirya ta ya kama hannunta suka nufi can wani ɓangare daga masarautar ya sada ta da su Mamma, da sauri ta iso suka rungume juna ita da Ikilima suna murna ta durƙusa ta gaishe da su Mai martaba, fuska cike da annuri yake amsa mata ta kalli su Kilishi har za ta share su sai kuma ta tuna a gaban wa take ta gaishe su, sai da Kilishi ta mata kallon tsaf sannan ta amsa, Saraunjya Bilkisu kuwa ko kallon ta ba ta yi suka ci gaba da hira...

_NIGERIA_

Tun lokacin da ta kashe waya ta dinga kuka tana tunanin rayuwarta ita da mijin nata, ji ta yi ana goge mata hawaye ta ja dogon numfashi jin ɗumin hannunsa akan kumatunta, kasa juyowa ta yi ta kalle shi saboda ba ta son kallon da yake mata yana saka ta a wani kalar yanayi, shi kuwa bai ma san dawan garin ba wai amarya ta yi kashi a moɗa! Jin yana taɓa mata wuya ta yi saurin kai nata hannun ta ɗaura akan nasa amma ta kasa janyewa ta yi shuru idanuwanta a lumshe, kallon ta yake kamar mai nazarin wani abu daga gareta, sai da suka kai minti biyu a haka sannan ya matso kusa da ita ba zato ba tsammani ta ji ya rungume ta tsam a jikinsa. Kwalalo idanu waje ta yi zuciyarta na bugawa da sauri, duk da ba wani sabon abu ba ne ya rungume tan amma yau dai ta ji ya bambanta da sauran, a hankali ta buɗe fararen idanuwanta wanda tsoro ya cika su ta sauke su a kan shi, wani kalar kwarjini na musamman ta ga ya mata, ga gemunsa da kullum take gyara masa ya ƙara wa fuskar tasa kyau, lips ɗinsa da yake saɓa su ta ƙurawa idanu tana jin ƙarfin bugun zuciyarta na ƙaruwa, kwayar idanuwansa ta kalla wanda shi ɗin ma ita ya tsare da kallo suka dinga kallo juna, dam! Ta ji gabanta ya wani kalar faɗi har sai da ta yi saurin kai hannu ta dafe ƙirjinta da yake harba mata. Sake buɗe idanu ta yi ta kuma kafe shi da kallo, sak Suhal take gani a gaban ta, komai nasa irin na Suhal kawai launin fata ne ya bambanta su, ajiyar zuciya ta sauke babu abin da yake matuƙar birge ta a fuskarsa irin gemunsa mai haɗe da kwantaccan saja sun luf-luf, ga idanuwansa farare tas duk kyan nata sai ta ga nashin ya fi nata haske.

Baki ta daga da niyar yi masa magana ta ji an dauke wutar ɗakin,. Tunani ta yi ko 'yan nepa ne suka dauke wutar sai dai ta ga saɓanin haka jin ɗakin ya ɗauki girgiza kamar zai kifa cikin ƙasa, ƙara riƙe hannun Zaiyan ta yi da ya zama kamar gunki ɗan hasken da ke shigo musu ta ƙofa shi ma ya ɗauke, lumshe idanu ya yi suka ji kamar ana taɓa wani abu kamar leda. Tagumi Abir ta yi dan ita a yanzu dai babu wani abin da zai firgita ta, haske ne ya bayyana a jikin bango ya dinga matsowa kusa da, kallon wajan duk suka yi suna son ganin abin da zai bayyana. Cikin shigarta ta kamala ta bayyanan musu suffarta fuska ɗauke da damuwa, zabura Zaiyan ya yi yana nuna ta ya ja baya ya koma bayan Abir yana kyarma, karshe ma ya yi kamar ya suma hakan ya tayar da hankalin Abir ta dubi matar ta ce "Haba Mama ya za ki firgitar min da shi?" Ta faɗa kamar za ta fasa kuka..

Murmushi ta yi ta zauna a inda Zaiyan ya tashi ta kama hannun Abir, kallon ta Abir ta yi sai sannan ta ce. "Na zo ne in miki godiya akan kulawa da Zaiyan da kike, sannan ina matuƙar farin ciki da ke ce kika kasance matarsa duk da lokacin da ki ka yi hakan ba kya cikin haiyacinki, na zo na muku bankwana ne zan yi wata tafiya ban sani ba ko zan daɗe ban dawo ba, amma kuna zuciyata duk inda zan je." Tsagaitawa ta yi sannan ta ɗaura "In na dawo in sha Allah zan sanar da ke komai game da Zaiyan, da inda ya fito da yadda aka yi ya samu ciwon haukan nan har ma da iyayensa duk zan miki bayani a kan su."

Da sauri Abir ta ce "Mama please ki faÉ—a min shin iyayen Zaiyan suna raye ko sun mutu? In suna raye a wani yanki suke ko a wani gari suke? Sannan me ya sa in dai har suna da rai suka kasa neman jininsu? Ki faÉ—a min iya wannan kafin ki tafi please Mama." Ta faÉ—a tana zubar da hawaye.

Girgiza mata kai ta yi sannan ta ce "Ki yi haƙuri ba yau na yi niyar faɗa miki labarinsa ba, yanzu lokaci ya tafi zan tafi sai mun sake haɗuwa, kuma karki damu duk komai zai zama daidai." Tana gama faɗin haka ta miƙe, da hanzari Abir ta miƙe itama cikin raunanniyar murya ta ce "please Mama me ya faru da ni har aka aura min Zaiyan? Ko ciwon hauka ni ma na yi ban sani ba?"

Juyowa ta yi ta kalle ta tare da yin murmushi ta ce "Abin da kaɗai zan iya ce miki shi ne, asiri aka miki amma hakan ma ya min tun da ba su cutar da ke ba." Tana faɗin haka ta ɓace ɓat a ɗakin..

Dafe kai Abir ta yi sai kuma ta sunkuya ta ɗago Zaiyan da ta miƙe ya faɗi ruf da ciki ta gyara mana kwanciyar, zama ta yi ta yi tagumi ta lula duniyar tunani..

A ɓangaren Abdul kuwa yanzu ya zama wani sha ka tafi, duk wani abu da ake a office ɗinsu na 'yan sanda sai ya sanar su Alhaji Mustapha. Ita kanta Hafsat wani lokacin har mamaki take in ya ce mata meeting zai yi da Daddynta abin na tsaya mata a rai, abin da ya fi damun ta ma da ta masa maganar Abir sai ya ce mata bai san ina take ba, haka za ta haƙura ta koma gefe tana kallon shi...

Baba da Inna tun washegarin Abir ta gudu suka ga takardar da ta aje musu, hankalin su ya tashi ganin abin da ta rubuta ya yi mugun tayar musu da hankali.

Baba ya rasa me zai yi ya dinga danna mata kira amma wayar a kashe dole suka haƙura suka zuba wa sauratar Allah ido....

_BAYAN WATA BIYU_

Yau ta ji za ta leƙa Istagram dan haka ta janyo Computer ta ta buɗe , saƙo ya yi ta zuwa amma ta kasa budewa, wani saƙo ne ya ja hankalinta na friend ɗinta na Tiktok *Big Boy*, a hankali ta buɗe saƙon nashi.

_"Hello my dear friend, how are you? So naji duk abin da ya faru da ke kuma nasa an yi min bincike an tabbatar min da e lalle abin da ake faɗa a Tiktok ba ƙarya ba ne gaske ne, abin da nake son isar miki ni dama na jima ina tsananin son ki, to amma da na ga kin sa Invitation ɗin aurenki sai na haƙura na koma gefen ina ba wa zuciyata haƙuri. A takaice dai ina son ki sosai kuma a shirye nake ko nawa ne zan kashe dan na aure ki, Dad ɗina zai yi min duk abin da nake so dan haka in kin ga saƙona ki ba ni amsa, amma karki kuskura ki furta min kala ɗaya wadda indai ina son abu na tsani a faɗa min ita, karki ce ki na da wani saurayin dan zan iya kashe mutum a kanki, I love you Habibty na. "_

Kwalalo idanu waje Abir ta yi tana sake nanata Kalmar so, gabaɗaya hankalinta ya yi mugun tashi da ya ce zai iya kisan kai a kan ta. Ƙarfafa zuciyarta ta yi ta masa reply.

_"Am so sorry bawan Allah ni ai tun tuni na yi aure da jimawa, dan haka karka sake turo min wani sako wanda ya shafi so ni É—in matar aure ce, please and please ka da ka sake yi min magana."_

Kamar jira yake ta tura masa ta ga ya ɗaga, kafin ta motsa ta ga ɗan gajeran saƙo.
Chapter 86 · 0% Book details