Sashe 69
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Anty ni ma ki wanke min irin naki." Ya faɗa yana nuna mata jikinsa. Lumshe idanu ta yi jin yadda sanyi ke shigar ta kaɗan-kaɗan, bude idanu ta yi ta sauke su a kan shi ya tsayar kamar yadda yaro ke tsayawa a gaban mamansa in yana son wani abu, girgiza kai ta yi ta ce "Ba kai ka ɓata min jiki ba naki na wanke ma ɗin." Ta faɗa tana hade fuska.
Baki ya riƙe yana daga kai sama zuwa can dai ya ce "Zan saya miki wani kayan fa."
Maisar ta dauko ta nuna masa ya tsugunna ta wanke masa, bi musa ba ya tsugunna ta wanke masa kai da ƙafafu sannan ta ce y tashi su shiga ciki ya yi wanka, da sauri ya tashi ya kama hannunta suka shige ciki.
A palo suka samu Inna ta yi wa Zaiyan dubara ta shige toilet shi ma Baba ya lallaba shi ya shigar da shi toilet, bayan ta gama wankan Inna ta dauko mata zani ta yi É—aurin kirji ta fito da shi sai a lokacin ta yi tunanin wani kaya za ta saka?
Dafe kai ta yi ta zauna a bakin gadon Inna sai ga ta Inna ta shigo da kaya a hannunta, miƙa mata ta yi tare da cewa "Ungu ki sa wannan na ga ku 'yan zamani ne kayan maza ma sakawa kuke, wannan na Zaiyan ne a cikin wanda kika sayo masa ne na ga ya yi kama da na mata na ce bari na kawo miki ki sa."
Murmushi ta yi tana amsar kayan ta daga su tana gani, riga da wando ne rigar mai haÉ—e da hula ce wando kuma dogo hakan ya mata, tashi tsaye ta yi ta ce "To Inna na gode bari na to."
Fita Inna ta yi ita kuma ta saka kayan ta ga wadon ya mata tsaye rigar ma ta mata yawa kasancewar ya fita tsawo sosai, murmushi kawai take in ta kalli kayan da ranar da ta kawo masa su a ranar ya sa su yana murna. Bayan ta sa ta fito palo inda ta samu Zaiyan ya tubure yana ta cewa ina Antynsa take? Ƴar dariya ta yi ta ƙaraso tare da cewa "Gani fa babu inda na tafi."
Murmushi ta ga ya yi ya iso inda take tsaye ya kama hannunta yana jan ta y ce "Zo muje na ciro miki mangwaro Anty."
Bin sa ta yi suka fito harabar, bishiyar mangwaro ya hau ya tsinko mata guda uku manta nunannu sannan ya sauko ya zauna a gindin bishiyar ya ce "Anty zo ki sha." Ya faɗa yana kai wa bakinsa. Da sauri ta amshe tana faɗin "Bari na wanke sai ka sha." Ta wanke su yana tsaye a gefen ta ta miƙa masa ɗaya suka dawo suka zauna yana sha yana ta zuba mata shirme, ta wuni a gidan ita da Zaiyan suna harabar gidan suna ta wasanni sai yamma ta tafi gida..
Umma ta dawo wajan Malam ta ta zayyano masa yadda komai na auren Abir ya kasance har ya dawo kan Iman ta ɗora da cewa "Amma Malam ai ba haka muka yi da kai ba ko? 'yata babbar ita zai aura amma na ga saɓanin haka, ko dai wani abu na yi wanda ya saɓawa dokar aikin?" Ta faɗa tana mai rausayar da kai.
Zane Malam ya yi a kan ƙasar da take gabansa, bayan ya gama ya ɗago ya gyara zama yana kallon Umma ya ce "Hajiya ai ni aikina yana ci sosai, ina tunanin dai da sunan karamar ne aka yi aikin shi y sa hakan ta faru."
Nisawa ta yi ta zarga handbag É—inta ta dauki daurin 'yan rafa ta dire masa a gaban shi, jinjina kai take tana murmushi ta ce "To duk ba matsala Malam hakan ma dai ya yi daidai tun da itama wadda ya aurar É—iyata ce, yanzu ga wannan ina son a kashe ta kawai kowa ma ya huta."
Da hanzari Malam ya dauke kuɗin ya zuba su a lajihun babbar rigarsa ya gyara rawanin kansa ya ce "Na faɗa miki tun zuwan ki shekarun baya ba zai yiyuba a kashe ta, amma yanzu za a iya haukatar da ita ko a sa kowa ya ƙyamace ta da haka baƙin ciki ya kashe ta." Ya faɗa miƙa hannu gefensa ya dauko wata leda ya miƙa mata, amsa ta yi ya ce "Wannan duk ta yadda za ayi ki turara mata shi ta shaki hayaƙin."
Kwalalo idanu waje Umma ta yi tana juya ganin ta ce. "To ai Malam cutar asma gare ta in ta shaki hayaƙi ciwon zai iy tashi, ni kuma bana son kowa ya gano abin da nake so nake komai ya tafi cikin tsari ba tare da kowa ya nakara ba."
Shuri Malam y yi sai kum ya saki murmushi ya ce. "To shi kenan ki bari za mu yi aikin da kan mu, sannan ina ƙara jaddada miki kar ki bari a gano wannan ajiyar tamu."
Jinjina kai ta yi ya amshe maganin ya b ta wani ya ce "Ki zuba mata a cikin abinci in ta ci za ki ga abin da zai faru."
Da murna Umma ta amsa ta tafi..
Haka kullum Abir ke tafiya gidan su Baba su wuni suna ta shawayi a harabar gidan, hakan na ƙara mantar da ita duk wata damuwa da take ciki. A cikin watanni 5 ta ƙara shaƙuwa da Zaiyan fiye da misali ba ta iya wuni sai ta gan shi, wani abu dake samun ta rashin samun kulawar Yayan nata da har da Grandma duk kowa ya ja baya da ita ba mai cewa ya ta tashi ko mai ta ci, haka kullum za ta yi ta kiran Abdul a waya amma yaƙi dauka in ta kira Hafsat ta tambaye ta ko ina yake dai ta ce mata ai yana nan, wannan abu ba ƙaramin ƙona mata rai yake ba ga shi ta rasa wa za ta faɗawa ta ji sanyi a zuciyarta.
Yau dai ta shirya cikin shigar ta ta abaya Arabian gown ta É—an sa kwalli ta fito tana danna wa Ali kira, yana dauka ta ce masa ya zo ya kai ta gidan Abdul ya ce ga shi nan zuwa. Umma ce ta kutso kan motarta harabar gidan Abir ta bi ta da kallo, tana fitowa Abir ta saki ranta tana murmushi ta ce "Umma sannu ko biki ake ne?"
Dariyar Allah sarki ta mata tana wayamcewa ta iso inda take, kallon ta take sama da ƙasa abin da ya bai wa Abir mamaki har za ta yi magana sai ta tsinkayo muryar Umma na cewa "Abir anya kuwa kina lafiya? Yau an fi sati ina zuwa part ɗin ku dan na kira ki Iman sai damuna take kin ƙi ɗaukan kiran ta in ta kira ki, ina fatan dai ba gama kike yi wa ƴar kanwar taki ba." Ta faɗa tana yin shu'umin murmushi tare da dafa ta tana shafa kafaɗarta.
Nisawa Abir ta yi cikin tsananin damuwa ta É—ago ta kalli Umma idanuwanta har sun cika da kwalla, murmushi Umma ta kuma yi tana mata wani irin kallo wanda ita kadai ta bar wa kanta sani. Sunkuyar da kai ta yi sannan ta ce "Umma Wallahi ba gaba nake da Iman ba, abin da ya sa na daina É—aukan kiran ta in ta kira sai dai ta tasa ni gaba tana min kuka wai sai na sa Yarima ya kawo ta Nigeria, hakan ya sa na daina É—aukan kiran ta dan na yi ta ba ta hakuri ta daina maganar zuwa Nigeria tun da mijinta ba ya son kawo ta yanzu, amma fir ta kafe har kwana hudu ta yi a É—aki ta rufe kanta ba ta fitowa waje za ta kashe kanta dan ya ce ta bari ba yanzu ba."
Zaro idanu Umma ta yi cike da ganin wautar Iman ta ce "Wai Iman ɗin ce ta yi haka? Wallahi sai na ci mutumcin ta tun da mu take so ta mayar ƙananan mutane, ba ta gidan sarauta komai na gulma da tsugudidi ba ne? Ke rabu da ita sai na ci ubanta tabbas, yanzu yaushe ne ta yi hakan za ta kashe kanta?" Ta faɗa tana jin da Iman a kusa da ita take to tabbas babu abin da zai hana ta zane ta, saboda yadda take son ruguza mata burin da ta ci akan ta..
Ajiyar zuciya ta sauke ganin yadda Umma ke sababi ta ɗan tausayar da kai ta ce "Wallahi Umma Iman sai dai ki mata addu'a ta kafe akan ita lalle ba ta son Yarima tun da auren cin amana ne aka mata, na nuna mata babu wata cin amana ta kwantar da hankalinta amma taƙi, yau Ikilima ta kirani take sanar da ni Iman ba lafiya ana mata karin ruwa duk ta rama saboda ko abinci ba ta ci ta rufe kan ta a ɗaki, hankalina ya tashi da naji haka na ce yaushe hakan ta faru? Ta ce min yau ne ta je sai Yarima ke sanar da ita halin da suke ciki ita da shi a gidan, to da kyar dai ta sidin Goshi ta yarda ta bude mata kofa inda tana budewa ta suma a bakin kofar. Amma don Allah Umma kar ki mata faɗa dayawa ki bata mata rai kuma ta yi abin da ya fi haka ma, ki mata nasiha kawai da addu'a kin ga yarinya ce har yanzu 16 gareta ba za ta yi wani dogon tunani ba in za ta aikata wani abin."
Ta karashe maganar tana gyara zama Jakarta bisa kafaÉ—a..
Gyada kai kawai Umma ke yi, wato ma ita Iman za ta kunyata ta je garin shirme ya sako mata ita duk wani alwashin da ta ci ya tashi a banza? Kwafa ta yi ta ce "OK Abir ba komai zan mata nasihar, yanzu ke ina za ki fita da ranar nan?"
Murmushi ta yi ta ce "Gidan Yaya zan je ga ma Ali nan y iso."