Sashe 49
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dawowa ya yi ya zauna a kusa da Abir ya shafa cikinsa yana kwaɓe fuska ya ce "Anty yunwa nake ji." Ya faɗa yana kafe ta da idanu.
Inna ce ta tashi ta kawo masa tuwo da miyar kuɓewa, ai kuwa ya dinga ci yana zuba miyar a jikin rigarsa, bayan ya gama cinyewa ya yi gyatsa yana sa hannunsa mai miyar ya goge bakinsa da shi, gabaɗaya miyar ta ɓata masa fuska har kusan kunnuwansa miyar ce, ya kalli Abdul ya ce "Baba yunwa nake ji."
Kitchen Abir ta koma ta ƙaro masa abincin nan ma ya cinye, duk jikin kayansa ya ɓaci da miya Baba ya tashi ya kama shi tare da Abdul suka ce ya zo ayi masa wanka, ai kuwa ya kwace yana hararar su ya ce "Anty wai za su yi min wanka.".
Runtse idanu Abir ta yi har sai da ya sake maimaita mata ta dube shi ta ce "Ka je ayi ma wanka, in kuma ba haka ba zan yi tafiya ta ba zan sake dawowa ba, kuma daga yau na hana kake ce min Anty." Da sauri ya miƙe yana kallon ta sai kuma ya dawo gaban ta ya ce "zan je ba za ki tafi ba ko?"
Gyaɗa masa kai ta yi ya miƙe ya isa wajan Baba ya kama shi suka nufi banɗaki, yana tafiya yana waiwayowa yana ce mata "Anty ba za ki tafi kina nan?"
E take ce masa har suka shige banɗaki, Inna ta tashi ta je ta dauko masa wani kayan ta ɗan buɗa toilet ɗin ta miƙa wa Baba ya amsa..
Sallama suka yi wa Inna Abdul ya ce za su dawo gobe ta musu godiya tana saka musu albarka suka bar gidan..
Tsaye yake yana zarya a babban palon, gabaÉ—aya jikinsa ya yi sharkaf da zufa sai goge ta fuska yake yana fesar da iska. Wayarsa ce ta soma ringing ya yi saurin dubawa, ganin number babu suna sai ya yi tunanin ko É—aya daga cikin su ne ya canja taku ya daga tare da karawa a kunne ya ce "Hello."
Muryar da ta amsa masa ce ta sa shi zabura har wayar ta suɓuce masa ta faɗi, hannu na rawa ya sunkuya ya ɗauka ya duba ya ga har yanzu mai kiran yana nan. Ya daɗe a haka ba a yi magana ba ai kuwa ya fusata ya ce "Kai yaro in kana cin ƙasa ka kiyayi ta shuri! Hawainiyarka ta kiyayi rama ta Wallahi! Kai gani kake tsoron ka ne ya sa muke ɓuya ko me? Ka yi kuskure Damisa da har ka sake dirowa Nigeria, tabbas wannan karon sai dai uwarka ta haifi wani ba dai kai ba, idan kuma ta gama haihuwa sai ta ci gaba da jimami in ka mutu." Ya ƙarashe maganar yana huci ga zufa da take ta yanko masa, duk sanyin AC da yake sanyaya palon ji yake kamar a gaban tukubar gashin tsire yake..
Dariya Damisa ya yi daga cikin wayar sannan ya ce "Alhajin Allah kenan, ai daga yau ka soma lissafa kwanakin ka Damisa ya dawo, ai ja da baya ba tsoro ba ne ga rago shirin faɗa ne! Matuƙar ina doran duniya ba zan taɓa barin ku a raye ba, na girma ne da muradin daukan fansa dan haka ban ga wanda zai ceceku daga hannuna ba. Wannan yarinyar da ka yi wa faɗe har ta yi ciki ka sa aka zubar karshe ta mutu kuka jefar da ita, to ina so ka sani tana nan a raye kuma ni nan zan tsaya mata wajan ganin an kwata mata haƙƙin ta da kika ɗauka. Mugaye kawai azzalumai masu suffar hawainiya."
Tun da ya fara maganar Alhaji ya yi sumar tsaye, tunani ya dinga yi waye ya sanar da Damisa wannan rufaffan sirrin nasu? Girgiza kai ya yi yana ƙarfafa wa kanshi gwiwa ya yi dariya wadda shi kan sa ya san ta yaƙe ce, zama ya yi ya ce "Kai ɗin banza! Waɗanda suka fika zarra ma sun zo sun kara da mu ba su ji dadi ba sun bar duniyar bare kai ɗan ƙaramin kwaro, ina mai tabbatar maka da kaina zan fasa kaika da bindiga."
Dariyar basawa Damisa ya yi ya ce "To mu zuba mu gani shege ka fasa ɗan halak sai yanka, bar ganin ƙanƙantar allura itama ƙarfe ce!"
Ƙit ya kashe kiran, Muzurai Alhaji yake yana sauke wayar ya yi saurin shiga app ɗin kira ya ga number da ya kira shi da ita, wata number ya kira ya ci sa'a an ɗauka, da sauri ya soma magana.
"Hello maza ga number nan zan zano maka ka duba min daga ina mai kiran yake."
Cike da girmamawa ya ce "OK Sir."
Zano masa number Damisa ya yi shi kuma yana sawa a kan computer da ke gaban shi, Alhaji na gama ba shi ya katse kiran ya zauna a kan kujera yaraf yana sauke numfashi, bai taɓa tunanin Damisa zai taɓa dawowa ba a yadda suka yi masa kisan gilla, sai ga shi ya rayu ya dawo da zafin sa fiye da yadda suka san shi a baya. Kira ne ya shigo wayar tashi ya wawuro wayar da ya yi jifa da ita gefe, ganin Alhaji Mustapha ne ke kira ya yi saurin dagawa yana huci, kafin ma ya ce wani abu Alhaji Mustapha ya soma magana a ruɗe.
"Hello kana jina? Wallahi in ba mu tashi tsaye ba wannan É—an iskan yaron sai ya goge masa hadda, wai ni zai kira yake faÉ—a min maganar banza to Wallahi wannan karon sai na sa an daddatsa min naman jikinsa na ba wa kare ya cinye."
Yana dasa aya Alhaji ya kaɗa kai yana jin muguwar tsanar Damisa a zuciyarsa, kwafa ya yi ya ce "Hmmm. Yo ai ni ma yanzu ya kira ni yake min maganar banza, in dai muka sake sai wanki hula ya kaimu dare muna ji muna gani, ya kamata ka yi abin da ya dace, daga ɓangaren ka ni ma zan yi wani abu tun da Uwa Dudu ta ce ba ta iya ganin suffar Damisa kodayaushe kamar yadda muke ganin fuskarsa a rufe itama haka take gani. Amma ya kake gani ko za mu iya samun wani gagarumin malami ko boka wanda zai kashe mana Damisa cikin ruwan sanyi? "
Alhaji Mustapha ya nisa yana tunani, can ya yi murmushi ya ce "Wannan yarinyar da take mana aiki ta ce min tana da wani riƙaƙƙen boka amma inda yake akwai nisa, ta ce yana can kan dutse aikinsa kamar yankan wuƙa."
Murmushi Alhaji ya yi ya ce "Yawwa har naji sauƙi yanzu ka nemo mana ita sai ta mana kwatance kawai, amma kuma duk da haka muke sa ido a kan shi kafin aikin ya hau kansa."
Haka suka ci gaba da tattaunawa suna tsara yadda za su bi wajan kashe Damisa, har Alhaji zai kashe Alhaji Mustapha ya yi saurin cewa "Sir abu ma fi sauƙi mu haɗa har wannan shegun yaran da uwarsu, ka ga sai mu yi yadda muke so."
Dariya suka sa sannan ya kashe, bai fi minti uku ba sakon wanda yake bincikar masa number Damisa ya shigo. Inda yake sanar masa wanda ya kira layi yana kashe kiran ya daina aiki da sim É—in, sosai Alhaji ya ji mugun haushi amma da ya tuna abin da suka tsara sai ya yi dariya ya tashi ya fita...
Washegari Suhal ya dawo da kayan aiki dan ya duba Zaiyan, bai daɗe da zuwa ba sai ga Abdul tare da abokin shi da Abir sun yo sallama. Yana ganin ta ya kawar da kai gefe, murmushi Doctor Hashim ya yi dan shi Zaiyan na birge shi, ita kuwa kallon shi take ganin yadda ya yi mata sihirtaccan kyau na musamman ta yo inda yake cikin nutsuwarta. Tana isowa ya kalle ta ya haɗe girar sama da ƙasa ya ce "Mun yi baram-baram." Riƙe baki ta yi tana mamakin kalmar da ya faɗa ta ce "Zaiyan da ni ɗin ce aka yi baram-baram? Ni ce fa Antyn ka ko ka manta?"
Hararar Abdul ya yi yana hura hanci ya ce "Ba ke ba Anty da Baba ne muka yi baram-baram, shi ne ya sace ki ya gudu gidansu nake ta neman ki, Anty wai ina ne gidanku nake zuwa muna magana? Kin wannan abokin nawa." Ya nuna mata Suhal, ya ci gaba da magana.
"Yau shekarar shi ashirin a gidanmu bai je ko'ina ba muna tare da shi har London muka je, amma shi Baba ko tsoron Allah ba ya yi ya sace ki dan kar aje London da ke yanzu ga shi har mun dawo abin mu. Kin ga da kina nan da na sayo miki kayan wasa ba sai kin je aron na wasu ba.."
Dariya Doctor Hashim ya yi yana zama ya ce "Wai yaushe Zaiyan ya zama mai surutu ban sani ba? "
Murmushi Abir ta yi ta ce "Ga dai zahiri ka gani Yaya Hashim tun jiya yake ta zuba mana surutu." Ta faÉ—a tana kallon shi.
Baba ya yi murmushi ya ce "Ai ko bacci da kyar ya yi, jiya da dare ya yi ta kuka yana cewa an sace masa Antynsa da abokinsa naje na kwato masa su, sai da muka dinga masa addu'a kafin ya samu ya yi bacci asuba na yi ya tasheni wai mu tafi Masallaci shi ma zai yi Sallah. Da kyar na masa dubara na ce ya yi a gida zan je na dawo sai mu tafi."
"Allah sarki bawan Allah."