← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 120

Sashe 10

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy da bai ce komai ba tun zuwa Barrister ya kalle shi ya ce "To ya muka iya da ikon Allah Barrister, gardama ce irin ta Yaya Ibrahim na faɗa masa in zai fita yake tafiya da masu tsaron lafiyarsa, amma gani yake kamar suna takura masa ƙarshe ma ya ce iya aikin su su bi shi office da kuma tsaron cikin gida ,ya fi so ya tafi shi kaɗai ƙarshe duk wasu officer ya mayar da su yin aiki, yanzu ga shi an ma rasa a wani hali yake a yanzu."

Mami da tun dazu take jan tsaki ta miƙe ta ce "Sai an jima ni zan je ɓangarena tun da maganar nan dai ba ta shafe ni ba."

Sake da baki Abba ke kallon ta har ta fita daga palon, haka ita ma Umma ta miƙe tsam ba ta yi magana ba ta bar palon. Duk ba wanda ya ce wani abu sai da suka bar palon sannan Barrister ya ce "My daughter za ki iya gane mutanen da suka kama ki?"

Dam! Ta ji zuciyarta ta buga ta sunkuyar da kai, to ita me ake so kuma ta faɗa bayan wanda ta faɗa? Shi ma ɗin dan ba ta da yadda za ta yi ta haɗa da ƙarya ta faɗa. Ganin taƙi cewa komai yasa Abdul gyara zama ya ba wa Barrister labarin da ta ba su, shi kuwa ya yi shuri yana nazarin maganar ko zai samu amsar da yake son samu, amma sam abin ya kulle masa kai hakan yasa ya kuma cewa "Uwar masu gida, za ki iya tuna kamannin mutanen?"

Goge majinar da ta fito daga hancinta ta yi sannan ta ce "Ni fa ban taɓa ganin fuskar ɗayan su ba, duka kullum fuska a rufe suke shigowa ɗakin da suka saka ni."

Ajiyar zuciya Barrister ya sauke ya ce "Ok to kukan ya isa haka yi haƙuri, in sha Allah zan ci gaba da bincike akan lamarin, akwai wani abokina D.P.O. ne na masa bayanin ɓatan amma tun da kes ɗin na hannun Abdul zan masa magana na ce an amshi kes ɗin, sannan in sun kira ku sanar da ni Alhaji ni zan koma, amma kafin nan ina son yin magana da Uwar masu gida. "Ya faɗa yana kallon ta.

Grandma ta ce "To Huzaifa mun gode kwarai ke kuma tashi ku je waje in kuma mu ba ku waje to?" Da sauri ta ce "A a Grandma mu je bakin motar shi kawai."

Ba ta musa mata ba ta tashi ta gyara mayafinta sai kuma ta ga daga gefe wajan da Mahaukaci ya taɓa mata ya yi dauɗa. Ajiyar zuciya ta sauke ta bi bayan Barrister suka fita..

Bayan sun fita Abdul ya ce "Anya kuwa Daddy ba akwai abin da Baby ke ɓoye mana ba?"

Murmushi Daddy ya yi ya ce "Haba kai kuwa taya ma za ta ɓoye mana wani abu bayan ta san ba ta wanda za ta faɗa wa damuwarta sai mu iyayenta, ka daina wannan maganar kar ma ka tarbe ta da ita."

Ba dan ya yarda ba ya ce da Daddy to kawai dan a bar maganar...

Suna fita bakin motar Barrister ya dubi Abir yana ɗan murmushi ya ce "Abir ki yi haƙuri in sha Allah mahaifinki zai kubuta kin ji. Sannan ina so ki faɗa min gaskiyar komai da kika gani bayan an sace ku."

Cikin ƙosawa da maganar ta ɗago da idanunta wanda suka yi jajur saboda kukan jda ta ci ta sauke su a kan Barrister, shi ma ƙura mata idanu ya yi sosai yarinyar ke ba shi tausayi ita kuka ba ya mata wahala ballantana wannan mai dalili ne. Shi ya fara ɗauke idanunsa daga kanta tare da ɓala yatsu biyu, da sauri ta sauke nata idanun a kunyace ta ce "Uncle iya abin da na sani shi na faɗa maka ku yarda da ni mana." Ta faɗa tana rufe fuskarta da mayafi..

Wani iri ya ji ba daÉ—i ya ce "OK zan kira ki idan na samu lokaci je ki ciki." Turo baki gaba ta yi ta tsaya ba ta tafi ba, har ya buÉ—e marfin motar ya ga tana tsaye sai ya dakata ya dube ta tare da cewa "Ya dai? Ko akwai magana ne?" Ya jero mata tambayoyi.

Saɓa baki ta yi cikin Shagwaɓar da ta zame mata jiki ta ce "Uncle ai ba ni da waya sun kwace min ita."

Murmushin gefen ba ki ya yi ya ce "that is very good my little, zan sa a bibiyi number in dai wayar a buɗe take tabbas za mu gano inda suke, yanzu ba ni number da kike da ita." Ya faɗa yana miƙa mata wayarta tsadaddiya

Ajiyar zuciya ta sauke ta amsa ta sa masa number sannan ta masa sallama ta shige ciki...

Ko da ta dawo Abdul ya tsare ta da tambaya.

"Baby me ya ce miki?"

"Ƙarin bayani ya nema." Abin da ta faɗa kenan ta ɗauki jakarta ta nufi ɗakinta.

Kwafa ya yi yana nufar ɗakin Grandma ganin duk sun tashi daga shi sai Grandma da Laraba ke mata tausa, ganin ya nufi ɗakinta ta daddage ta ce "Kai Abdullahi uban me ka aje min a ɗaki da za ka shiga? In ce ba da kuɗin uwarka Sa'ade aka gina min ɗakin ba dai ko? To maza ka yo baya ƙaton banza tuzuru sai warin balaga kake ka zama rikakken namiji ba mata, to ni ba ƴar banza ba ce irin iyayen naka da suka saya ka sai abin da ka ga dama kake yi. Yanzu ba dan ba ma ni zuciyata a tsakake take ina zan yarda ka zauna kusa ma da ni kana warin balaga." Ta ƙarashe maganar tana gutsirar goron da ke hannunta ta ƙara masa da harara.

Sai da ya tsaya ta gama sannan ya ba wa iska ajiyar ta ya shige É—akin. Ganin ya shiga ta kwashi salati "Muhammadu Rasulullahi sallallahu alaihi wa sallama ni Hauwa'u! Wannan wacce irin fitina ce haka? Na ce kar ka shigar min É—aki amma dan jafa'i sai ka shiga, za ka fito ka sameni a palon nan sai na ma wankin babban bargo."

Ita dai Laraba ƙunshe dariyarta take kar ta fito ta yi laifi Grandma ta yi mata tatas kamar yadda ta saba mata...

Labari ya karaɗe cikin garin Yola da kewayanta na ɓatan Alhaji Ibrahim Maitama, hatta social media duk inda ka nufa maganar sace shi kawai ake yi, har ma da masu ƙarawa labarin gishiri. Wasu su ce ai abokan kasuwancinsa ne suka haɗa masa tuggu aka sace shi, wasu kuma su ce kawai mahassada ne abin dai kowa da kalar ƙagen da yake faɗa..

Abir duk ta ƙara ramewa ta yi zuru-zuru kamar ba ta cin abinci, tunanin Abie ɗinta take ba dare ba rana ga tunanin yadda za ta ga mahaukacin nan duk ya addabe ta..

Yau ma kamar kullum tana zaune ta lula duniyar tunani can ta tuna number dattijon nan, da sauri ta miƙe ta fito zuwa ɗakin Mommy. Da Sallama ta shiga inda ta samu Mommy ba ta ɗakin, jin ƙaran ruwa a banɗaki yasa ta gane wanka ta shiga, cikin sauri ta ɗauki wayar Mommy ta duba ɓangaren kira ta shiga neman number, sai da ta sha wahala sannan ta samo number ta yi saurin ɗauka ta fita..

Cin karo suka yi da Yasmin ita ma tana sauri, saurin kallon Abir ta yi ganin ita ce yasa cikin ɓacin rai ta ce "Ke wata irin mahaukaciya ce? Ta ya za ki buge ni ko ki bani haƙuri kike ƙoƙarin wucewa?" Ta faɗa a fusace.

Ko uffan Abir ba ta ce da ita ba abin da ya ƙara tafasa zuciyar Yasmin ta ɗaga hannu ta zabga mata mari ji kake tass!

A ruÉ—e ta juyo tare da dafe kuncinta saboda wani irin zafi da ya ziyarci dukkan ilahirin jikinta har sai da ganinta ya É—auke na wucin gadi.

"Last warning! Idan kika sake min irin haka sai na kakkarya ki mai ƙirar aljannu jikar mayu, ban san me Yaya Salim ya gani a tare da ke ba har yake wani rawar jiki a kank...

Kafin ta ƙarasa ta ji saukar wani gigitaccan mari kan fuskarta, ta juyo a ruɗe dan ganin wanda ya mare ta sai suka haɗa idanu da Abdul nan-da-nan jikinta ya ɗauki rawa, shi kuma tun lokacin da ta mare ta yake tsaye a kofar palon yana kallon ƙarfin hali irin Yasmin, ta bangaje ta kuma ta mare ta ɗan iya shege. Abin da ya ɓata masa rai ya harzuƙa shi da ta haɗa ta da Salim nan-da-nan ya ji zuciyarsa ta ɗauki wani kalar zafi marar iyaka..

Da sauri Abir ta dawo bayan Abdul ta kwanta a bayansa ta saki kuka, ita ba marin ba ne ya ɓata mata rai da take haɗa ta da aljannu shi ya fi taɓa mata zuciya, duk da ta saba jin wannan kalmar a wajan su Mami da sauran yaran gidan.

Dawo da ita ya yi gaban shi ya shiga goge mata hawaye yana ba ta haƙuri har ta daina kukan sannan ta zare jikinta daga nasa ta wuce ɗakinta, ita kuma Yasmin ta yi ƙiƙam tana musu kallon ɓakin ciki, sai da ya daka mata tsawa sannan ta fice da gudu..

Shirin Makaranta take ta yi cikin ɗan kuzarin da ya rage mata ta fito inda ta samu Mommy zaune ita da Laraba tana ba ta labarin ƙauyensu, kallon ta Mommy ta yi ta ce "Kin shirya?"

"E Mommy zan wuce ayi mana Addu'a."

"Allah ya kiyaye ki a dawo lafiya."

Murmushi ta yi tare da matsowa ta yi kissing É—in Mommy sannan ta wuce waje. Direba ta samu yana jiran ta, sai da ta gaisa da su Maigadi sannan ta shiga suka tafi..

Tsaye ya yi a bakin hanya yana goge sandarsa yara na tsokanar shi yana nuna musu sandar, kamar an ce ta waiga ta gan shi cikin sauri ta ce "Direba dakata please." Ta faÉ—a tana waigen shi

Saurin taka birkin ya yi ya tsaya ya juyo ya kalle ta ya ce "Ranki ya daÉ—e lafiya dai."

"E lafiya lau buÉ—e min na fita akwai abin da nake son yi a nan."
Chapter 10 · 0% Book details