Sashe 8
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_"Wato ke mai kunnan ƙashi ce ko? Kin yi alƙawari amma kika karya kin manta sharadin mu da ke?"_
Da sauri ta miƙe tsaye ta nufi hanyar fita daga Asibitin saboda kiɗimewa ba ta san ta fita daga Asibitin gabaɗaya ba sai da ta ji ƙaran motoci na wucewa ta gane ta fito a waje take. Waige-waige ta dinga yi hagu da dama ai kuwa ta ga wasu maza biyu na kallon ta, da gudu ta nufi hanyar komawa cikin Asibitin sai ji ta yi ta yi karo da wani abu ta faɗi Tim!....
Littafin nan dai na kuÉ—i ne my sister.
_Taku har kullum Maman Nusaiba ce_
[6/20, 7:26 PM] Ummu Amjad: [10/25, 3:35 Yamma] My Addatyna: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~
Daga Alƙalamin
_*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
_+966577675904_
*بسم الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…*
Shafi na biyar (5)
Tallah !! Tallah !!
Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji.
Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa.
RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal.
Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal
Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.
Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank
Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku.
A kiɗime ta yunƙura cikin kuzarin da ba ta san tana da shi ba ta miƙe tsaye, ba ta ma tsaya ganin abin da ta ci karo da shi ba ta nufi ƙofar Asibiti da gudu sai dai kafin ta isa ta ga an sha gaban ta, ware dara-daran idanuwanta ta yi a kan ɓakar ƙafarsa wadda taɓo da ƙura suka mata fenti, saurin kallon shi ta yi gabanta na faɗuwa kamar yadda shi ma ita ɗin yake kallo.. Kamar kullum yau ma sanye yake da gaggayen wandonsa wanda tun farkon haɗuwar su ta gan shi da shi, ƙafarsa ba takalmi haka yake yawo, riga biyar ce a jikinsa ɗaya kan ɗaya kowacce ta yi mugun yin dauɗa. Wani irin sanyi ne ya ziyarci zuciyarta har ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba ta gyara tsayuwarta tare da lumshe idanu, buɗe idanuwanta ta yi ta juya bayan ta suka haɗa idanu da mazan nan har yanzu suna inda suke a tsaye sai daddana waya suke lokaci zuwa lokaci suna kallon agogon dake hannunsu..
Ganin ta juya tana kallon su ya yi saurin sunkuyawa ya ɗauki sandarsa ya sakala a kafaɗa tare da yin dariya ya shiga zagaye ta yana cika sadar a ƙasa, sai da ya dawo gaban ta ya ɓata fuska ya ce "Imm Anty tafiya kike yi?"
Murmushi ta yi ganin yadda ya harɗe kamar ɗan fulani, ƙura mana idanu ta yi shi kuma ya dinga tambayarta ina za ta je amma ba ta ji mai yake faɗa ba dan ta yi nisa a kallon da take masa, sai da taɓa hannunta sannan ta yi firgigit ta saki murmushi ya kuma tambayar ta ce "A a ina jiran yayana ne." Ta faɗa tana dawowa gefen shi, haka kawai ta ji yau so take ta zauna da shi su yi hira duk da ta san ba ma zai gane inda maganarta za ta dosa ba..
Sauke sandar ya yi yana dariya ya shiga zagaye ta yana faɗin " Anty ta yi tafiya! Anty ta zauna! Anty ta miƙe!"
Murmushi Abir ta yi jin yadda yake kiran ta da Anty har da waƙa abin sai ya ba ta nishadi, Jakarta dake riƙe a hannunta gam sakamakon tsoron da ta ji lokacin da za fito a razane ta buɗe ta ɗauko gorar ruwa mai sanyi ta miƙa masa, shi kuwa ya tsare ta da kallo idan ya kalle ta sai kuma ya kalli gorar. "Ga shi maza ka sha ruwa." Ta faɗa tana nuna masa ruwan.
Amsa ya yi ya É—aga gorar yana duddubawa yana faÉ—in "Allah sarki abokina kai ne haka? Ina kwana? Dama haka kake ban sani ba?" Ya faÉ—a yana shafa rubutun dake jikin gorar.
Ƴar dariya ta yi ƙuncin da ke zuciyarta na yayewa, sosai ta shagala da kallon shi yana nuna mata gorar tare da tambayarta.
"Anty ga abokina nan ya ce ki bani kayansa zan kai masa."
To kawai ta ce masa ya ci gaba da surutai barkatai wata maganar ita kanta ba ta gane me yake nufi sai dai ta bi shi da to ko a a.. Duk da hankalinta ba a kwance yake ba amma haka take biye masa in ya yi magana ta amsa masa, juyowa ta kuma yi dan ta ga mazan nan ko suna nan sai ta ga wayam ba kowa. Ajiyar zuciya ta sauke ta dube shi ta ce "Ya sunanka wai?"
Dariya ya mata ya ce "Ya sunanka zai ci abinci." Ya faÉ—a yana É—aga gorar tare shafa bayan.
Suna a haka sai ga motar Salim ta iso bakin Asibitin, da sauri ya fito ganin ta tsaye da Mahaukaci riƙe da makami, a ɗan naisa da su ya tsaya ya ce "Baby waye wannan ɗin?" Ya faɗa a tsorace. Murmushi ta yi ta ce "Shi ne wanda nake ba ku labari, kawai na fito ne na haɗu da shi."
"Kwalalo idanu waje ya yi ganin yana kallon shi nan-da-nan tsoro ya cika masa zuciya, shi kuma kallon shi kawai yake yana dariya abin da ya ƙara tsoratar da Salim. Baki na rawa ya ce "To..To zo mu tafi gida."
Kallon shi ta yi cikin wani irin yanayi, ji take kamar su É—auki lokaci mai tsayi a haka tana hira da shi, sai da Salim ya sake maimaita maganar sannan ta rausayar da kai kamar za ta yi kuka ta ce" Sai an jima." Ta faÉ—a tana juyawa ta soma tafiya.
Da sauri ya biyo ta ya ce "Anty abinci nan ci." Ya faÉ—a yana kama mayafinta yana marairaicewa kamar zai sa mata kuka. Ita kuma sai ta ji wani irin abu ya soki zuciyarta ta ji ba za ta iya tafiya ta bar shi ba.
Kallon Salim ta ya yi sai ya ce "Baby bari na sayo masa abincin."
Girgiza kai ta yi ta ce "Yaya don Allah taimako nake so ka min." Ta faÉ—a tana narkar da murya.
"Indai ba a kan wannan Mahaukacin ba ne zan taimaka, amma in dai akan shi ne ba ma zan iya ba." Ya faÉ—a yana haÉ—e rai.
Saurin kallon shi ta yi cikin rashin sanin abin yi ta ce
"Don girman Allah Yaya mu É—auke shi a kai shi Asibiti, duba ka ga yadda kayan jikin shi suke fa, ina so na taimake shi kamar yadda ya taimake ni." Ta faÉ—a tana goge hawayen da ya zubo mata.
"Wallahi ba zan É—auki Mahaukaci a cikin motata ba, so kike ya kashe mu gabaÉ—aya? Ke wai ma meye damuwarki a kan wannan Mahaukacin wanda bai san kansa ba bare ya san abin da ya dace da shi ba?" Ya yi maganar yana nuna shi da yatsa.
Hawaye ne suka cika mata ido murya na rawa ta ce "Don Allah fa Yaya Salim ka taimaka mu ɗauke shi a motar nan, ina so zan kula da shi na kai shi Asibiti ko Allah zai sa a dace ya samu lafiya, ka ga in na yi haka na samu lada kai ma kuma ka samu lada mai yawa na taimako." Ta faɗa tana durƙusawa a gaban shi ta kama ƙafafuwansa tana kuka.
Duk wanda ya zo wucewa sai ya tsaya yana kallon su har wani da ya zo wucewa ganin tana kuka ta riƙe masa ƙafa ya tsaya, kallon Salim ya yi cikin nuna tausaya mata ya ce "Haba bawan Allah kai wani irin azzalumi ne? Ta ya yarinya za ta durƙasa a gabanka tana kuka, amma dan rashin sanin darajar mata ka kasa yi mata abin da take buƙata? Ni a gani na ko ba ka son ta bai kamata ka nuna ba ka son ta ba a gaban idanunta, don Allah ku samu waje ku zauna ku fahimci juna." Yana gama faɗin haka ya wucewar shi bai ma tsaya ya ji mai Salim ɗin zai faɗa masa ba. Shi kuwa Salim in ransa ya yi dubu yau Abir ta gama ɓata masa shi, ta zubar masa da mutumci har mutane na tsayawa su ce ya ci zarafin ta bayan ba su san akan Mahaukaci take wannan roƙon ba. A fusace ya ce "Kin san Allah in ba ki tashi ba muka tafi zan bar jin tausayin ba ki da lafiya na lafta miki mari a bakin titin nan, za ki tashi ko sai na miki duka?" Ya faɗa yana ɗaga murya.
Idan akwai abin da Abir ke matuƙar tsoron ayi mata ya gigita mata rayuwa to bai wuce a mata tsawa ba, hakan yasa ta miƙe da sauri duk da tsoron da take ji amma ba ta fasa faɗin abin da take son faɗa ba.
"Shi kenan kar ka taimaka min Yaya Salim, nasan yau da Yaya Abdul ne na nuna masa wanda ya ceci rayuwata na kuma nemi ya taimaka masa ba zai min wannan wulakancin ba, ni ce fa Ƙanwarka Yaya Salim ko ka manta ne?" Ta faɗa tana fashewa da kuka tare da rufe bakinta dan kar sautin kukan ya fito...
Shi kuwa ganin tana kuka ya matso kusan Salim ya durkusa shi ma yana kuka kamar yadda ya ga tana yi, ganin ba ta fasa ba sai shi ya daina ya yi zunbur ya miƙe tsaye ya dubi Salim tare da ɗaga sandar da ke hannunsa ya ce "Kai ne kasa Anty kuka ko?" Ya faɗa yana ɗaga sandar zai sauke masa.