← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 120

Sashe 58

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka Abir ta dawo kamar kurma abinci sai Abdul ya zo ya saka ta a gaba take ci, idan kuwa ya dage sai ta ci dayawa sai ta sa masa kuka dole ya rabu da ita. Shi kan shi Abdul É—in dauriya ce yake a matsayinsa na namiji kuma babban É—a gidan, kullum sai ya yi kukan rashin Mom musamman idan ya shirya zai fita aiki da ya shiga part É—in su, sai ya ga kamar zai ga ta fito daga kitchen dauki da breakfast É—in sa ta ce ya zo ya karya kafin ya fita.

Tun da ya koma bakin aiki ba ya samun abincin kari saboda Umma ta ce sai dai yake zuwa ƙabarin Mom tana ba shi abincin tun da dama can ba nata yake ci ba, dan haka yanzun ma ba zai ci ba duk da Mom mutuwa ce ta yi ba wani gari ta tafi ba. Idan ta faɗa masa haka sai dai ya girgiza kai ya wuce part ɗin su in ya samu Laraba ta gama sai ya ci, in kuma ba ta gama ba haƙura yake ya tafi haka bai karya ba..

A ɓangaren Abir kuwa sam ba ta iya bacci rashin Mom a tare da ita in ta tuna yana gigita duniyar ta, gabaɗaya ta ƙara ramewa ta ƙanjame kamar wadda ta yi shekara tana jinya abin ka da mai ƙaramin jiki, ba ta da aiki sai kuka sai kallon photon Mom. Abin da take son sani shin ina dangin Mom suke? Ko suma sun mutu kamar yadda Mom ɗin ta mutu? In kuwa suna rayé me ya sa ba su nemi Mom ba har tsayin wannan shekarun? Wannan tunanin kadai yana hanata sukoni in ta tuna ita dai ba ta kowa a dangin uwa da ta sani face Abdul, Shi kaɗai ne gudan jinin ta da za ta bugi kirji ta ce ga dangin mahaifiyarta...

Suhal yau ya sauka Nigeria shi da Ikilima sun zo gaisuwa, sosai Abir ta ji haushin rashin zuwan sa lokacin da aka yi mutuwar duk da kuwa ya faɗa mata uzirin shi ba ya ƙasar ya tafi Ghana ne wajan wani taro da Maimartaba ya tura shi ya wakilce shi. Suna sauka a airport Abdul da Salim suka je ɗaukan su, bayan sun isa sai da ya kira Suhal ya masa kwatancan inda suke tsaye suna jiran su.. Tun daga naisa Ikilima ta hango Abdul da ba ta gani ta kyale ta daddaɓi Suhal ta ce "Yaya kalli wani haɗaɗɗan gaye."

Murmushi kawai ya yi yana kallon Abdul har suka ƙaraso, hannu ya miƙa masa suka gaisa Ikilima ta ce "Sannun ku."

Da fara'a suka amsa da yawwa sannan suka nufi motar suka shiga sai gida.. Suna isowa gidan Ikilima ta kalli Suhal ta ce "Yaya ina Anty Princess É—in take ne?" Dafe kai ya yi yana hararar ta ya ce "Ke wai me ya sa kin fiya surutu ne?" Cuno baki gaba ta yi ta fito suka nufi ciki. A palo suka samu Grandma tana jan tasbaha ta manne farin glass a idanunta sai kallon su take, zama suka yi Suhal ya ce "Grandma ina yini? Mun same ku lafiya?"

"Alhamdu Lillah ɗan nan ya iyayen naka suke? Wannan fa ko ƙanwar ka ce?" Ta faɗa tana kallon Ikilima da take yaba kyau da tsaruwar gidan.

Murmushi ya yi ya ce "E Autar mu ce ai."

Jinjina kai ta yi sai kuma ta yi murmushi ta ce "Allah sarki har ka tuna min da tawa Autar, itama yau za su sauka Nigeria wajan dare ƙila, amma ta ce idan ba su zo ba yau ko gobe to gaskiya ba za su samu zuwa ba, ba su zo wajan mutuwar nan ba mijin nata sunƙi ba shi hutu har ita kanta su zo ganin gida." Ta faɗa tana goge idanu. Suhal ya tankwashe ƙafafunsa ya ce "Grandma ya kuma muka ji da rashin Mom? Wallahi mutuwar nan ta taɓa ni sosai, lokacin bana gida ina Ghana sai yau ɗin nan na dawo da safe na ce ba zan bari sai na huta ba gara na zo na yi gaisuwar nan tun da an zama ɗaya." Ya ƙarashe maganar yana sauke numfashi.

Tashi Abdul ya yi ya nufi ɗakin Abir dan ya sanar da ita zuwan Suhal. Ko da ya shiga cikin bargo ya same ta ya tako har bakin gadon ya zauna tare da sa hannu ya yaye bargon, ƙura mata idanu ya yi ganin yadda take bacci amma sai zabura take tana jan numfashi, hakan ya tabbatar masa ba ta jin daɗin baccin yi kawai take. Addu'a ya dinga tofa mata har ta fasa zaburar, a nutsu ya yi Bismillah ya kai hannu ya shafo fuskarta cikin wani irin yanayi na tausayin halin da take ciki ya ce "Baby! Baby tashi mana Suhal ya zo suna palo ke ake jira?"

A hankali ta shiga buɗe idanuwanta tana mayar da su tana rufe wa har ta gama buɗe su a kan fuskarsa, turo baki gaba ta yi kamar za ta sa kuka ya yi saurin ɗago ta ya zuro da ƙafafunta bakin gadon, kallon ta ya yi ganin yadda take yatsine fuska ya ce "Kin ga yi hakuri ki tashi ki wanke fuskar ki ki kimtsa ki fito ya zo shi da ƙanwar sa."

Waro idanu ta yi alamar mamaki sai kuma ta mike ta zari É—ankwalinta da É—an kuzarin ta ta nufi toilet.

Yana nan zaune har ta fito ta ɗan shafa mai sai ya fita ya ba ta waje ta canja kaya sannan ta nufi palo. Tun daga naisa yake kallon ta ganin yadda ta rame sosai, wani irin abu ne ya kawo masa ziyara ya lumshe idanunsa yana mai ƙara jin tsananin ƙaunar ta a cikin zuciyarsa. Zaunar da ita ya yi suka tashi har grandma suka ba su waje, Ikilima ta ƙura wa Abir idanu tana ƙare mata kallo, matsowa ta yi kusa da ita ta kamo hanayenta cikin tausayawa ta ce "Anty Princess sannu kin ji, Allah ya jiƙan Mom da rahama ubangiji ya haskaka makwancin ta."

Goge hawayen da suka zubo mata ta yi murya na rawa ta ce "Amin Auta na gode sosai. Ya Suhal barka da zuwa ya su Mamma Kun zo lafiya?"

Numfashi ya ja yana jin kamar ya rungume ta ya yi ta rarrashin ta har sai ya ga ta yi dariya, sosai yake jin zafin kukan da take ya ɗan jumƙe hannunsa na dama ya buɗe sannan ya ce "Alhamdu Lillah Princess, Allah ya jiƙan Mom ya haskaka kabarin ta, Mamma ta ce ayi miki gaisuwa kuma ta ce ki rage damu ki daina kukan nan addu'a kawai Mom ke buƙata.."

Jinjina kai kawai ta yi sai ga Iman da Laraba sun shigo da sallama dauke a kayan abinci, sannu da zuwa suka masa sannan suka ja Ikilima har Abir aka bar Suhal ya ci abinci. Abdul ne ya shigo palon shi da Salim suka dauki kayan abincin suka nufi ɗakin baƙi ya biyo su a baya.

Daret wajan cin abinci suka wuce inda sun gma jera abinci, sun zauna kenan sai ga Umma ta shigo ganin Ikilima ya sa ta yin fara'a tana fadin "A a mutanen Niger ne har an iso?"

Murmushi Ikilima ta yi ta durƙusa ta gaishe da Umma ita kuma ta amsa tana washe baki, sabuwar mai aikin ta ce ta iso da ƙatuwar kula guda biyu ta kalli Iman ta ce "Ke Iman tashi ki kaiwa surikin namu abinci ki zuba masa ya ci ya ƙoshi, ki ce masa kar ya yi kara ya ɗauka nan kamar gidan su ne." Ta faɗa tana miƙa mata kular, miƙewa Iman ta yi cike jin daɗin Umma ta mutumta su Ikilima ta am shi kular ta nufi ɗakin baƙi. Da sallama ta shiga ta sami Abdul da Salim da Suhal na shirin cin abinci, kallon ta Abdul ya yi ya ce "Ya dai Iman?"

Aje abincin ta yi tana murmushin jin daɗi ta ce "Yaya Umma ce ta ba da abinci ta ce a kawo wa Yaya Suhal ya ci kuma kar ya bar saura ya cinye duka abincin da ta zubo." Ta faɗa tana buɗe kular, ƙamshin haɗaɗɗiyar shinkafa da kaza ya daki hancin Suhal nan da nan ya ji yawunsa ya tsinke, kallon kular ya yi yana murmushi ya ce "Ai kuwa naji daɗi kuma ki ce wa Umma na gode sosai da wannan karamcin zan shigo na gaishe ta, zubo min na ci ki gani kar ki ce wa Umma ban ciba."

Dariya ta yi ta dauki filet ta zuba masa haɗi da cokali ta miƙa masa, amsa ya yi ya soma ci sannan ta fita. Kamar haɗin baki tana fita sai ga Yasmin itama ta shigo ɗauke da abinci, murmushi Salim ya yi ya kalli Suhal ya ce "Iyye wato yau dai kai ɗan gatan su Umma ne, ga Ammi ma ta kawo maka nata girkin."

Murmushi kawai ya yi Yasmin ta aje ta gaishe da Suhal ya amsa ba yabo ba fallasa ya ci gaba da cin abinci, sai da ta ɗan jima sannan ta ce "Ammi ta ce a kawo wa surikin ta girki ne ta yi na musamman dan shi." Ta faɗa tana hararar kular Umma haushi ne ya turniƙe ta ganin yana cin abincin Umma ta haɗe rai ba ta ma saurari mai za su ce ba ta wuce fuu..

Da kallo suka bi ta Salim ya yi dariya ya ce "Ja'ira kawai."

Bayan kowa ya gama cin abincin Suhal ya nemi Abdul da Salim su yi masa iso wajan Umma da Ammi su gaisa kafin su Abba su zo, Abdul ya shiga part É—in Ammi da sallama ya samu duk suna zaune a palo kamar ba su jiran shi. Murmushi Ammi ta yi tana kallon Abdul ta ce "A a Abdul, ina surikin namu yake? ."

Kawar kai ya yi sai kuma ya daure fuska ya kalli Fatima ya ce "Ke matso nan."
Chapter 58 · 0% Book details