Sashe 31
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Mustapha ya murmusa yana kallon ta ya ce "My daughter ya aka yi na ga duk kin ƙara ɓaki? Ki yi haƙuri kin ji ki daina saka damuwa a ranki komai zai yi daidai, Hafsy ta ce a gaishe da ke za ta ma zo muku hutu ranar Juma'a." Ya faɗa cikin iya takunsa.
Goge hawaye ta yi kanta a ƙasa ta ce "To Uncle in sha Allah zan rage damuwa, da zan fi kowa jin dadi in Hafsy ta zo mana hutu."
Murmushi ya yi sannan ya dubi Abba da Daddy da Daddyn Aruf da Mommy da Grandma ya ce "Alhaji Sulaiman na zo ne akan wata magana wadda nake son a sauke nauyinta kar a bar É—an'uwana cikin masifa."
Saurin kallon shi Abba ya yi ya ce "To wannan wani irin nauyi ne haka?"
Ƙara gyara zama ya yi ya ce "Ni da Jarmai da Alhaji Tanko ɗan ƙasar Niger mun zuba hannun jari a wani company, to bayan wata biyar kasuwancin ya yi albarka muka samu riba sosai ke Sadiya kin tuna lokacin da muka yi wani meeting a nan palon?" Ya faɗa yana kallon Mommy da ta yi tagumi.
GyaÉ—a kai ta yi ta ce "Tabbas na tuna kun yi meeting mai tsayi a ranar."
Wani irin daɗi ya mamaye shi ya ce "To muna magana ne akan kasuwancin, mun sake zuba kuɗi har naira miliyan ɗari mu huɗu, ni miliyan goma Jarmai miliyan goma Alhaji Tanko miliyan goma, to sauran miliyan saba'in ɗin ta Alhaji Ibrahim ce, mun haɗa mun ba shi kuɗin ya kai da kuɗin wani company da ke nan Niger na atamfofi miliyan talatin ya ce zai kai musu. To bayan kwana biyu ne labarin ɓatan shi ya bazu a gari, ranar kamar na yi hauka hankalina a tashe na dinga gwada kiran wayarsa amma sai ace a rufe take, ga shi mutanen da suke bin mu bashi sun takura mana, ni kuma a lokacin ba ni da kuɗi a ƙasa dan duk na yo oda na kuma zuba hannun jari a kamfanoni har uku. Da ƙyar muka haɗa miliyan goma ni da su Jarmai muka tura musu tare da faɗa musu halin da ake ciki sai suka daina kiranmu. Yanzu kuma sun ga labarin mutuwarsa shi ne suka ce lalle fa mu biya kuɗin nan, to yanzu al'amura duk sun dagule min shi ya sa na zo a samu a ba da miliyan ashirin ɗin nan mu tura musu kayansu...
A zabure Abdul ya ce "What?"
ÆŠaga masa hannu Abba ya yi ya dubi Alhaji Mustapha ya ce "Yanzu idan aka haÉ—a har nakun nawa kuÉ—in ya kama?"
Alhaji ya goge zufar dake keto masa ganin yadda Abdul ke masa wani irin firgotaccan kallo, baza malum-malum É—insa ya yi ya gyara ta sannan ya ce "To kuÉ—in in aka gama za su zama miliyan sittin ne cif, sannan na sa a tambayi ma'aikatan shi ko akwai wanda yake binsa kuÉ—i a sauke masa nauyi har ma da waÉ—anda muke kasuwanci duk na ce musu in suna bin shi bashi su faÉ—a a biya masa kar ya kwanta da bashi a kabari."
A fusace Salim ya juyo ya kafe su Alhaji Mustapha da wani irin kallo, huci yake saukewa yana hura hanci ya miƙe tsaye dan dama shi sam ya tsani taraiyar Abie da su Alhaji Mustapha, cikin ɓacin rai ya ce ....
*🤓Magana ake ta biyan bashi mai ya hyaru.*
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[6/20, 7:46 PM] Ummu Amjad: WhatsApp number: +966577675904
Shafi na (17)
Cikin tsananin ɓacin rai haɗi da jin haushin Alhaji Mustapha ya ce "Gaskiya Abba ban yarda da maganar nan ba a yi bincike." Ya faɗa yana hura hanci, saboda duk abin da Alhaji Mustapha ya faɗa bai gamsu da shi ba ko ɗaya.
Daddyn Aruf ya harare shi yana haÉ—e fuska ya "Wa ya ce ka sako wa mutane baki? Kenan so kake a bar É—an'uwan mu da bashi yana cikin kwancinsa?"
Sunkuyawa ya yi cikin tsananin fushi ya ɗauki wayoyinsa tare da bin hanyar fita, yana zuwa saitin su Alhaji ya aiko musu da harara sannan ya sa kai shige ɗakin Grandma yana aiyanawa a ransa tabbas sai ya bi diddigin wannan maganar dan gano gaskiya. Abba ya girgiza kai tare da gyara zama shi kan shi ya ji matukar mamakin bashin da ake bin Yayan nasa, saboda in zai yi abu sai ya rubuta ya aje ya kuma kira su ya faɗa musu ga abin da ya yi ko ba ya raye. Alhaji Mustapha yi dinga muzurai yana ƙifƙifta idanu so yake ya ji abin da Abba zai faɗa game da lamarin, Abba ya nisa yana jinjina lamarin a cikin zuciyarsa sannan ya ce "To shi kenan Alhaji in sha Allah za a tura ma kuɗin, kawo account ɗin da za a tura kuɗin, sannan kuma ina takardar shedar yadda komai ya wakana?. " Ya ƙarashe maganar yana kallon shi.
Wani irin murmishi Alhaji Mustapha ya yi wanda shi kaɗai yasan na meye ya ɗaga wata ɓakar Jaka ya zaro takardu ya miƙa wa Abba, amsa ya yi ya karanta ya ga lalle rubutun ɗan'uwan sa ne ga kuma sa hannunsa nan ga na Alhaji Mustapha da su Jarmai nan. Daddy ya amsa shi ma ya duba ya ga komai a rubutu sannan ya miƙa wa Mommy ta aje ko dubawa ba ta yi ba.
Abba ya bukaci Alhaji ya kawo akawun number É—insa a tura kuÉ—in.
Takaici ne ya hana Abdul yin magana, yana zaune duk aka yi maganar komai amma ko ƙala bai ce ba sai binsu yake da idanu ɗaya bayan ɗaya. Alhaji Mustapha kuwa duk a ɗarare suke, sam shurun Abdul firgita shi yake dan yasan halin Abdul sarai in dai ya yi shuru to da abin da zai biyo baya, hakan ya sa ƙara saita nutsuwar shi kar Abdul ya rusa masa wannan gagarumin shirin da suka kwashe shekaru suna yi yau kuma ga shi zai cika. Lumshe idanu ya yi zuciyarshi na tafasa ji yake kamar ya sa kan bindiga ya harbe su Alhaji Mustapha ko zai samu salama, so yake ya ce wani abu amma kamar wanda aka manna masa gam a baki ya kasa cewa komai, ba wai kuma dan babu abin da zai faɗa, yana da tambayoyi masu tarin yawa da yake son yi musu amma sam ya kasa cewa komai sai sauke ajiyar zuciya yake. Kallon Abba ya yi da yake yi wa Mommy magana ƙasa-ƙasa, girgiza kai ya yi yana tattaro yawu da ƙyar ya samu ya haɗiye dan makoshinsa ya bushe, da sun san su waye Alhaji Mustapha da ba su yarda sun bayar da wannan kuɗin ba a take, amma rashin sani aka ce ya fi dare duhu! Tsam ya miƙe daga zaman da ya yi shi ma ya bi bayan Salim zuwa ɗakin Grandma ta bi shi da kallo tana baki.
"Kai dai an yi ƙaton banza Abdullahi, yanzu saboda ɓakin hali ana maganar kai da wannan mai ƙirar Yarbawan za ku shige ɗaki kamar wasu mata? To ni ba ƴar banza ba ce da zan tsaya ina faɗa akan ku sai warin balaga kuke, gabaɗaya kun raina mutane ba wanda ya isa ya saka ku abu in ba kun so ba kun zama manyan kanku da kanku kenan?"
Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Alhaji Mustapha ganin mutanen da suka son ɓata nasa shiri sun bar palon, juyowa ya yi suka kallo juna shi da Jarmai a sace suka saki murmushi, saurin gyara zama ya yi yana wani kamewa ya dubi Grandma ya ce "Inna ai ki rabu da su kawai, kin san yaran nan namu 'yan zamani ne musamman in suka kai mawar aure sai an bi su a hankali sai a zauna lafiya." Ya faɗa yana murmishi.
Riƙe baki Grandma ta yi ba ta ce komai ba, Abba ya kuma cewa Alhaji Mustapha ya kawo akawun number ɗinsa.
Jiki na rawa Alhaji Mustapha ya ji maganar kuɗi ya janyo wayarsa ya miƙa wa Abba ya ce "Ga sunan akawun ɗin nawa nan sai ka ɗauka."
Jinjina kai Abba ya yi ya ɗauka ya miƙa masa wayar, miƙa wa Mommy ya yi ya ce "Matar Yaya ke kika san code ɗin account ɗin ki tura masa adadin kuɗin su."
Mommy ta amsa ba tare da ta ce komai ba ta daddana wayarta cikin abin da bai fi minti biyar ba Alhaji Mustapha ya ji ƙarar shigowar su, saurin duba wayar ya yi ya ga alert na miliyan hamsin cif. Wani irin daɗi ne ya mamaye zuciyarsa kamar ya kurma ihun daɗi ganin komai ya tafi daidai, godiya ya musu suka tashi za su tafi ya jadadda wa Abir Hafsat za ta zo mata hutu. Tana murmushi ta ɗaga masa hannu kawai ta matso kusa da Mommy su kuma suka fita har su Abba zuwa harabar gidan..
Kiran Sallar La'asar ne ya farkar da Abdul daga baccin ɓakin cikin da ya yi, buɗe idanuwansa ya yi a hankali ya sauke su a kan Grandma da ke zauna a kan darduma tana yin lazumi, miƙa ya ƙara yi yana jin jikinsa na masa wani irin mugun ciwo ga baccin bai isheshi ba sai hamma yake yi. Hannu ya kai cikin sumar kansa wadda ta ɗan hargitse ya yamutsa ta yana jin kansa ya masa mugun nauyi, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya yaye bargon da ya lullube jiki da shi ya zuro ƙafafuwansa ya zauna a bakin gadon yana kallon Grandma.