Sashe 111
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasa yarda suka yi da maganarta nurses ɗin sai faɗa mata suke ta sato jariri ne za ta ce musu jikanta ne? Ana Haka sai ga Doctor ya iso ya nemi jin ba'asin taron da suka yi suka sanar da shi ta sato ɗan mutane, kallon Asabe ya yi sai kuma ya ce duk su tafi suak wuce, ya kalli Asabe ya ja ta zuwa ɗakin da aka kwantar jaririn ya gan shi sun sa masa na'urar ƙarin numfashi. Sai da ya tambaye ta ina ta samo shi, ganin likitan na da nutsuwa ta sanar da shi abin da ya faru tana kuka, sosai hankalinsa ya yi mugun tashi ya ce zai sanar da 'yan sanda ta zauna ta kula jaririn. Godiya ta masa shi kuma ya tafi bakin aikinsa da nufin in ya gama zai shigar da rahoto, kwanan su biyar a Asibiti aka Sallame ta wannan Likita shi ya dauke ya ya kai shi gidansa y ci gaba da kula da shi, shi da kansa ya sa wa yaron suna Zaiyan saboda sunan da yake so in Allah ya ba su haihuwa su saka amma ba su samu ba kusan shekaru 10 da aure. Haka Zaiyan ya taso cikin kyakkyawar kulawa har ya kai shekaru shida suka saka shi a makaranta, Zaiyan ya taso yaro mai surutu ga shiga rai duk wanda ya zauna da shi to fa zai ji kamar ya yi ta zama da shi, haka ya dinga karatunsa cikin kwanciyar hankali. Shekarar Zaiyan 12 Doctor ya samu takardar ƙarin karatu, ya sanar da Asabe ta sa masa albarka ya ce zai saya musu gida su koma dan nasun ya musu girma, haka ta yi ta sa musu albarka suka sanar da Zaiyan tafiyar ya dinga rusa kuka sai ya bi su, da kyar aka rarrashe shi ya yi shuru matar Doctor na kuka ta saki hannun Zaiyan suka bar gidan. Doctor daret Unguwar Talakawa ya samu ya saya musu gida ɗan matsakaici, ya ba su kuɗi mai yawa sannan ya ce mata duk wani abu na karatun Zaiyan ya biya ya dage da karatu, yana kuka ya ce "Abba zan bi ka." Girgiza masa kai ya yi ya ce masa zai dawo tukun ya yarda ya tafi...
Haka suka ce gaba da rayuwa yayinda Asabe ke boye wannan jaka ta Husna dan kar Zaiyan ya gani ya tambaye ta, shi kuma ya mayar da hankali yana ta karatu..
Shekara biyu da tafiyar Doctor amma ba su taɓa jin duriyar su ba, Asabe ta kira amma ba ta samun su saboda a kashe ma ake ce mata, haka ta zuba wa sarautar Allah idanu..
Zaiyan na gama karatu ya ce shi fa aikin É—an sandan farin kaya yake so (C. V. N), Asabe ta goya masa baya har ya shiga aikin kuma aka dauke shi, haka yake kula da Asabe lokaci zuwa lokaci yakan ce mata wai ina babansa yake? Kuma ina dangin su? In ya faÉ—i haka sai ta ce masa ai babansa ya rasu tun kafin ya zo duniya, su kuma dangi ba su da shia gidan marayu suka taso ita da babansa, idan ta faÉ—a masa haka sai ya ji tausayi ya kama shi na uwar tasa ya ce mata in sha Allah zai tara kuÉ—i ya saya musu gida ya inganta rayuwarta..
Abin da yake damun Asabe yadda Zaiyan yake tambayarta wannan jakar meye a ciki? Sai ta ce masa kawai kayan tarihi ne sai ya yi shuru yans kaon jakar, hakan na tsoratar da ita dan ba so ya ga abin da yake ciki.
Bai dauki lokaci ba yana aiki ya samu ƙarin matsayi, Asabe ta taya shi murna ta sa masa albarka, shi da kansa ya saka wa kansa suna Damisa a office ɗinsu da haka ake kiran shi... "
Da sauri Abir ta kalle ta baki na rawa ta ce "Ma.. Mama k.. Kina nufin ki ce min Zaiyan shi ne Damisa?"
Jinjina mata kai ta yi sannan ta ɗaura da cewa "Kwarai kuwa Zaiyan shi ne Damisa, ƙwarewarsa a wajan aiki ya sa wannan suna ya bi shi, sosai yake zaƙulo masu lefi in ba 'yan office ɗin su ba ba wanda ya san shi ne Damisa, saboda a gida da Zaiyan yake amsawa. Sannan shi masanin computer ne dan in ya shirya binciken mutum yakan iya yi masa hacking ɗin account na social media, har sim card yana rufe wa mutum shahararre ne a wannan fannin, hakan ya sa ko barayi za su binciko inda suke shi ake nema ya bi diddigin su har ya gano inda suke.. Lokacin da ya cika shekaru 25 aka canja masa wajan aiki zuwa Yola, haka suka haɗa kayansu suka dawo Yola da zama. Tun da ya dawo yake ta zaƙulo masu lefi har ya je kan wasu shu'uman mutane wato Alhaji Mustapha da Alhaji Sadisu, tun da suka gane yana son binciko gidan gonarsu da suke sato yara ƙanana su yi safarar su zuwa ƙasar waje hankalinsu ya tashi, ranar da ya gano komai ya kai bayanan office din Ogansu ya nufo gida.. A hanyar dawowarsa wata babbar mota ta bigi motarsa ta watsar da shi can, haka aka dauke shi aka kai shi Asibiti abokan aikin sa nufi suka gidan su dan sanar da Asabe suka tarar da mummunan labari, inda suka samu ta yanke jiki ta faɗi ko shurawa ba ta yi ta tafi kenan. Sai da Zaiyan ya yi kwana goma a Asibitin sannan ya farka amma me? Gabaɗaya ya manta komai na rayuwarsa hankalin abokan aikinsa ya tashi suka nufi gidansu da shi, ba kowa a gidan suka rasa wa za su bari wanda zai kula da shi, wani maƙocin su Zaiyan mai suna Malam Amadu shi ne ya ce su kawo shi gidansa zai kula da shi. Haka suka dinga kula da shi komai sai sun kowa ya masa, ya kai shekara a haka kamar ya samu sauki saboda ya iya magana komai ya iya kawai dai memorie ne bai dawo ba, abu kamar wasa ya soma fita yana yawo a Unguwa ashe abin ya ƙara ta'azzara ciwon hauka tuburan yake. Suka mayar da shi Asibiti amma an yi gwajin duniyar nan ba a ga komai ba a kwakwalwarsa, Malam Amadu da matarsa suka shiga damuwa haka suka ci gaba da riƙe shi, wani lokacin ma a kan bola yake kwana sai ya ga dama ko in yana jin yunwa ya shigo ya ce su ba shi abinci.. Karshe ma ya koma wani kango da kwana haka zai yi ta tare mutane a bakin hanya ya tsare su da surutu kuma ba dama ka motsa in bai ba ka izini ba, yana tsaka da ciwon ne Allah ya jefo masa ke cikin rayuwarsa.. "
Kuka marar sauti Abir ke yi tana shafa kan Zaiyan, ta É—ago idanuwanta da suka yi jajur ta ce "Mama to yanzu ina wannan jakar ta mahaifyar Nury? Sannan su iyayen nasa da aka sa musu wutar mutuwa suka yi ko kuwa sun farfado kafin wutar ta kona su suka tsira?".
"Wannan Jakar tana wajan Malam Amadu, kafin Asabe ta rasu shi ta ba wa ta ce ya ajiye mata kar Zaiyan ya gani, wannan kuma ba zan ce miki komai ba game da iyayesa, iya abin da zan iya sanar da ke shi ne, ke ce za ki sada Zaiyan da ahlinsa shi É—in É—an'uwan mijin kanwarki ne Iman, iyayensa suna nan a raye ki sada shi da su Hauwa'u. " Ta faÉ—a tana zubar da hawaye..
Baki buɗe Abir ke kallon ta sai kuma ta jinjina kai ta ce "Tabbas jini ba ƙarya ba ne Mama, dan tsananin kamar da suke ta ɓaci amma ban san ta ya zan musu bayani su fahimta yaron su."
Dafa ta ta yi tare da cewa "Wannan Jakar ita ce babbar shedar da za ki nuna musu, duk da suna kama da makahaifinsa sosai amma dole sai da shedar nuna cewa shi É—ansu ne."
Gyaɗa kai ta yi ta daga baki za ta yi magana ta ɗaga mata hannu dole ta gumtse maganar da take son faɗa, sauka ta yi ƙasa ta tsaya akan kafafuwanta tana kallon Zaiyan. Miƙa ya yi ya kai hannu yana laliban fuskar Abir sai kuma ya buɗe idanuwansa, da sauri ya diro daga kan gadon ba ki na rawa ya ce. "Ma... Ma yaushe kika zo da daren nan? Ashe zan sake ganin ki Mama?"
Murmushi ta yi sannan ta ce "Ba ita ba ce."
Saurin kallon ta ya yi ta jinjina masa kai, gyara tsayuwa ta yi ta sanar da shi komai da y faru bayan ya yi accident, hawaye suka dinga bin kuncinsa yana jin wani kalar zafi, ta wani gefen ya ji sanyi jin an ce iyayensa suna raye har ma Abir ta san ɗan'uwansa. Sai da suka jima a haka sannan ta ɓace daga ɗakin.. Rufe idanu ya yi yana ta tariyo irin yadda Inna Asabe ki ririta shi, iska ya fesar ya dawo kan gadon ya kwanta yana goge hawayen da suka zubo mishi, ganin haka ya sa ta janyo shi ta rungume tana masa nasiha...
Bayan Kwana uku aka sallami Abir suka dawo gida inda Zaiyan ya tafi gidan su Baba, ya sha kuka sosai ya kuma gode musu da irin ɗawainiyar da suka yi da shi, amma bai ce musu Suhal ɗan'uwa ba ne dan shi har yanzu ya ma kasa yarda yana da iyaye bare ɗan'uwa. Jakar Baba ya ba shi inda ya ga wayoyi biyu da suke ciki ya buɗe ya ga akwai memory a ciki ya zare shi, ya sa a tasa wayar amma suka nuna basa yi sun lalace, ya ji takaici sosai ya zazzage duka kayan da yake ciki nan ya ga irin ƴar karamar walit ɗin nan ta maza, ɗauka ya yi buɗe ya ga irin ɗan ƙaramin photon nan da ake sakawa a jikin walit ɗin guda biyu na mace da na namiji. Sai a sannan ya ƙara tabbatar da cewa ba fa Inna Asabe ta haife shi ba, ya dauke photo ya adana ya mayar kayan ciki ya samu waje ya aje..