Sashe 61
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jinjina kai ya yi dan yanzu ya kawar da mamakin sa akan Alhaji, ajiyar zuciya ya sauke ya ce " Alhaji ayi hakuri ai zuwa dare ko gobe da safe za ta farka, ta yi doguwar suma ne shi ya sa da ace wasu likitocin ne da tuni sun ce ma ta rasu saboda yadda numfashinta ya É—auki, sai ka auna kafin da kyar kake ganin bugun zuciyarta shi ma ba daidai yake bugawa ba. Da zai yiyu Alhaji zan ba ka shawara in za ka bi." Ya faÉ—a yana kallon Alhaji.
"Maza ka faÉ—a min indai akan samun lafiyarta ne zan kashe kuÉ—i ko yafi miliyan goma ne."
Jinjina kai Doctor ke yi tabbas Alhaji yana ji da yarinyar nan sosai, gyara tsayuwa ya yi ya ce "Me zai hana ka fitar da ita waje in da halin yin hakan?" Ya faÉ—a yana mai É—an rusunawa kamar zai gaishe da shi.
"To shi kenan yanzu abin da za ayi zan bari goben ta farka sai ka mana komai na tafiya, dama ina so zan je kasar Istanbul ka ga sai muje can a duba min ita." Ya faÉ—a yana shafa fuskarta da ta yi wani irin fari bakinta ya bushe har fari lips É—inta suka yi kamar an sa musu gasarar koko..
Juyawa ya yi ya bar shi ya koma bakin aikin shi, shi kuwa Alhaji ya tsura mata idanu har sai da yaji ringing wayarsa sannan ya É—an janye ta daga jikinsa ya ciro wayar. Ganin Jarmai ne ke kira sai ya yi saurin É—agawa tare da karawa a kunne ya ce "Jarmai ya ake ciki? Ina fatan dai jiya duk ka yi sauran aikin nan da boka ya ba mu?"
Daga can ɓangaren Jarmai ya yi dariya ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ce "Alhaji albishirin ka."
Da sauri Alhaji ya ce "Fari tas Jarmai maza ka faÉ—a min nasan ko ma meye yana daya daga cikin samun nasarar mu.",
Tashi ya yi tsaye ya goya hannu baya ya ce "Wannan yaron da muke nema Dagus ya ce sun ga hanyar da wannan yarinyar take yawan bi, hakan ya sa suka dinga bibiyar ta har suka ga wani gida ne take zuwa inda suka tabbatar min wannan yaron yana ciki. Yanzu aiki na gama saura ita yarinyar da É—an'uwanta, suma nan ba da jimawa ba za su kawo mana kan su. " Ya yi dariyar 'yan duniya sannan ya ci gaba da magana.
"Ina faÉ—a maka Damisa mun bar jin labarin sa da alama sun kashe shi, amma dai zan tambayi Dagus naji ya ake ciki."
Dariya Alhaji ya yi yana kallon fuskar sweet girl É—in sa, wani daÉ—i ne ya mamaye shi ya ce "Ka rabu da wannan yaron Jarmai mu yi aiki mai mahimmanci wanda yake gaban mu, tun da dai mun samu jinin da ya yi daidai da nasa kawai ka bu rabu da rayuwar shi tun da dama mahaukaci ne, abin da ya dace kai ka sake komawa wajan Boka a rikita mana Abir ta kasa nutsuwa har sai ta kawo mana dukkan kadarorin mahifinta sannan ta ji nutsuwa. Shi kuma Abdul ai mun gama kama shi kawai so nake na ga kiran Alhaji Mustapha. "
Shuru Jarmai ya yi can dai ya ce "To shi kenan mu aje maganar mahaukaci a gefe, ka ga yanzu nan da shekara mai zuwa za a fara zaɓe dan haka mu tsiro da wata gidauniyar tallafi wadda za ta sa al'ummar Yobe in mun nemi takara su kaɗa mana ƙuri'a. Ba ka ce min nan da sati biyu ba ne daurin auren Abir?"
"E nan da sati biyu ne."
"E jibi ne kuma duk za mu je mu yi bake-bake akan komai mu nuna mata tsananin ƙauna a wajan taron nan, kuma a matsayin ku na abokan mahifinta ku nuna mata ƙauna a ranar dan ni ka ga uba nake a gare ta." Ya fada yana shafa tumbinsa.
Dariya Jarmai ya yi ya ce "Alhaji ba ka da mutumci Wallahi." Shi ma dariyar ya yi suka kashe. Yana kashe kiran sai ga kiran Alhaji Mustapha ya shigo suka gaisa, bayan sun É—an yi hira nan yake sanar da shi yanzu su Abba suka zo neman auren Hafsat kuma ya amince a hada da na Abir, sosai Alhaji ya yi farin ciki ganin nasarori na tunkaro su gadan-gadan sannan suka yi sallama...
An kawo lefi akwati sat shida kowacce ka buɗe cike take taf da kaya na alfarma har da su alƙabba kala-kala, su Umma su ne akan gaba sai jin dadin take tana yi wa Abir kallon za ki gani..
Ɗiyan Inna da ke kasashen waje suka dura Nigeria ranar an sha kuka a part din su Abir, Yasira na rungume da Abir cike da tausayin ta sai rarrashin ta take tana kula da ita, da kan ta ta nemo mai gyaran jiki tun daga Maiduguri ta ce a gyara Abir ciki da waje ta fito ta yi kyau sosai, har da maganin ƙiba ake ba ta dan ta dan yi kumari kafin a kaita gidan ta...
Hafsat da Daddyn ta ya faɗa mata ya sa auren ta da Abdul sai da ta buga tsalle ta rungume shi tana kukan farin ciki, dan tun da take babu namijin da take da burin mallaka sama da Abdul, ranar kasa bacci ta yi sai kiran ƙawayen ta take tana sanar da su bikin ta nan da kwana sati biyu duk tana gaiyatar su. Washegari sai ga kiran Abdul abin da ba ta taɓa tunanin zai faru ba Abdul ya kira ta a waya, nan yake sheda mata ta fitar da nako ta mata lis din komai zai turo mata kudin, ai kuwa ta yi ta masa shagwaɓa tana faɗa masa yadda take son shi a zuciyarta da matsayin sa shi ma ya sanar da ita duk matan duniya babu kamar ita, kamar ta yi hauka dan daɗi ta kira Abir suka fitar da anko kala hudu...
Yau kofar gidan su Abir cike take a Mutane tun daga farko Layin har karshe mutane ne, kama daga kan yan Niger manya da kuma abokan Suhal da shi kansa Suhal ɗin ya sha shadda gizna sai sheƙi yake irin na angwaye, sai dai kana kallon fuskarsa za ka san ba shi da nutsuwa sai dafe kai yake yana kallon wayarsa lokaci zuwa lokaci..
Bayan an gama daura aure su Abba suka shigo gida inda suka buƙaci a kira duka kowa na familyn yana son ganin su, Umma na jin haka ta rangaɗa guɗa ta zari mayafi ta nufi part ɗin Inna.. Sai da kowa ya hallara har da Hajiya mahaifiyar su Umma itama ta zo, bayan ya buɗe taro da addu'a ya kalli Abir ya ce "Mamana kin yi imani da Allah da mala'ikinsa da kitattafansa da duk
manzannin da ya aiko da ƙaddara mai kyau ko akasin haka da ranar karshe?"
Jikinta ne dauki rawa ta gyaɗa kai tana ƙara mannewa a jikin Mom Yasira. Ajiyar zuciya ya yi ya ce "An ɗaura auren Abdul da Hafsat, sannan an ɗaura auren Yarima Suhal da Iman.."
Wata irin zabura Iman da Abir suka yi a tare suka furta Kalmar "Me ka ce ABBA?"
Suka faÉ—a ta mugun kiÉ—imewa kowacce sai kallon Æ´ar'uwar ta take.
Fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya Abir ta yi tana jan numfashi ta nufi Abba, so ta yi magana amma kukan da ya ci ƙarfin ta ya hana ta yin maganar, kafin ta ƙarasa ta zube a ƙasa sumammiya. Hankali a tashe Iman da ke kusa da inda ta faɗi ta shiga jijjiga ta tana faɗin "Ƴar'uwata don Allah kar ki min haka, Wallahi ko me za ayi ba zan taɓa yarda na auri Yaya Suhal ba, ki tashi Anty Baby...!"
_Taku har kullum Maman Nusaiba_
[11/6, 10:53 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~
+966577675904
Shafi na (30)
Gabaɗaya suka yo kan ta cikin tashin hankali amma Iman ta hana kowa ya taɓa ta har Abdul, duk wanda ya yi ƙoƙarin taɓa ta sai ta kurma ihu tana nuna shi da tsaya alamar kashedi. Abba da Daddy da Daddyn Aruf suna zaune ba su tashi ba sai kallon ikon Allah suke ganin Iman ta yi bake-bake ta hana kowa zuwa wajan Abir da ta ke kwance kamar Gawa, a hankali Daddyn Aruf ya tashi ya isa tare da tsugunnawa ya kalli Iman da take gunjin kuka fuskarta ta ci kaca-kaca da majina da hawaye sai kiran sunan Abir take, numfashi ya ja cikin nuna alhini ya ce "Iman ban san ki da wannan halin ba, taya za ta suma amma ki ce ba za a taɓa ta ba?"
Ƙara ta kwalla har sai da Daddyn Aruf ya runtse idanuwansa har cikin kwanyarsa yake jin ƙaran, a haukace ta ɗago idanuwanta sun yi jajur ta ɗaura su akan na Daddyn Aruf ta saki kuka ta ce "Matuƙar kuna so na bari ku taɓa Anty Baby sai kun janye auren da kuka ɗaura min da Yaya Suhal kun ɗaura da ita, wannan wani irin tashin hankali ne nake gani ni Iman? Don Allah Uncle ka rufa min asiri ka cewa Abba ya janye kalamansa Wallahi ina son Anty Baby ba zan yarda na zama katangar da za ta raba tsakanin ta da Yaya Suhal ba." Ta ƙarashe maganar tana kama hannun Daddyn Aruf da ya kafe ta da na mujiya. Kafin ma ya yi magana ta ɗago da Abir tana bubbuga kumatunta cikin tsananin fargaba ta ce "Anty Baby ki rufa min asiri ki tashi, Wallahi ko mutuwa kika yi ba zan yarda na auri Yaya Suhal ba, duka nawa nake? Ƙarama da ni za a ce wai an min aure?" Juyowa ta yi ta kalli Abdul da hankalinsa yana kan su ta goge hawaye ta ce "Yaya idan har ka bari aka raba Anty Baby da farin cikinta to tabbas Mommy za ta yi kukan cin amanar da ta ba ka, kai ka mata alƙawarin za ka kula da ita duk abin da take so za ka mata amma kana gani za su aura min wanda take so Yaya why ba ka faɗa min ba kafin a ɗaura? Why Yaya?" Ta faɗa tana sake ɓarkewa da sabon kuka..