← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 120

Sashe 41

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji ya yi shuru yana nazari can ya ɗago ya kalli Alhaji Mustapha ya ce "Hmm wato duk ƙoƙarin da nake ba ku gani ko? Ni yanzu ba wannan ba ne ba ma abin damuwa ta nasan za a samo min inda wannan taƙadarin yaron ya ɓoye shi, duk wani motsi in na yi yana biye da ni so yake ya samu kafa ɗaya da zai kama ni da lefi amma bai san cewa wanda ya riga ka bacci dole ya riga ka tashi, na kusa kawo ƙarshen rashin kunyar shi very soon.

Jarmai ya kaÉ—a kai yana jin tsananin tsanar Abdul, a fusace ya ce "Oga ka faÉ—a mana me yake faruwa bayan neman yaron da muke?"

Gyara zama ya yi yana yin kwafa ya ce "Abu mafi girgiza hankali shi ne Damisa ya diro Nigeria, kuma zuwan da ya yi ba wai irin na baya ba ne, wannan karon da zafin sa ya dawo jiyar nan ya sauka amma ya gano sirrikan mu dayawa, kuma gaf yake da gano inda muke ban san ta wata hanya za mu ɓullowa lamarin ba. Matsala ta gaba kuma wannan shegiyar yarinyar da duk wata kadara ta Ibrahim ke hannunta wani yaro daga Niger y zo neman auren ta, kuma an amince masa a gidan ita kawai suke jira. Idan har muka bari ta bar ƙasar nan da takardun nan to tabbas wata rana za ta buɗe su har ma'adanan sirrin da duk wata ɓarnar da muke Ibrahim ya naɗi komai, in fa ba mu tashi tsaye ba akwai matsala." Ya ƙarashe maganar zufa na tsatsafo masa y yi sharkaf kamar ruwan sama ya dake shi..

Dukkan su ba wanda bai shiga tashin hankali ba musamman jin labarin Damisa ya dawo Nigeria, Jarmai ya tashi tsaye ya ya buga tebirin da ke gaban su shi kan shi ya ji mugun tsoro na shigowar Damisa gari, kallon su ya yi ya ce "To abin da za ayi kawai, mu sa a kashe shi kada mu bari wannan karon ya sake guduwa ba tare da mun aika shi can ba. Itama ya kamata wannan karon mu kwato komai daga gare ta mu kashe su daga ita har É—an'uwan nata, kai har uwarta ma mu kashe dan ita uwar ta fi yar sanin komai game da mu. Shi kuma yaron nan mu san yadda za mu sato shi. "

Murmushi Alhaji ya yi ya ce "Jarmai kenan, har yau ka kasa gane waye Damisa mutumin da ko fuskarsa mun kasa gane wata kala ce. Ko kai ka taɓa ganin fuskar Damisa babu takunkumi?"

Shuru Jarmai ya yi Alhaji Mustapha ya ce "Dole fa mu samo wata hanyar, amma Oga tun da muna da mana aiki ita mace ce mai zai hana mu nemi wani abu daga wajan Barru? kasan fa wani lokacin kan ta kawo wuta?" Gyaɗa kai Alhaji ya yi tare da cewa, "Hakan ya yi sosai zan same ta mu tattauna abin da ya biyo baya sai na sanar da ku, shi kuma Abdul na gano tarkon da zan ɗana masa ya faɗa tun da mun tura masa Juju babu abin da ya faru da shi. Tabbas wannan karon ba zai kuɓuta daga tarko na ba, har ita yarinyar duk na samu masa mafita ita ma zan sa Barru ta yi wani abu game da ita, kun ga kenan abin da ya rage masa guda biyu ne. " Kowa jinjina kai yake cike da gamsuwa da maganar Alhaji, Alhaji Mustapha ya ce" To amma wani irin tarko ne za ka yi wa Abdul? "

Dariya Alhaji ya yi yana zagaye su ya dawo ta gefen Jarmai sannan ya ce" Ba ina da 'ya ba? "

"Kwarai haka ne." Suka faɗa a tare, ya ɗaura "To ita ce makami na, Hafsat tana tsananin son Abdul amma tsoron shi da take ne ya sa ta ɓoye, dalilin shishige masa da take yi ne ya ce kar ta ƙara zuwa gidansu ya yanke ƙawancan su da Abir, yanzu kuma ita da kanta Abir ɗin ta nemi Hafsat dan haka wannan dama ce babba a gare mu dan samun abin da muke so."

"Gaskiya wannan shawara ta yi." Cewar Jarmai yana yi wa Alhaji jinjina. Dariya duk suka sa Alhaji ya kalle su ya kaikaice hular shi ya kai ta gidan tara ya ce "Ni fa gaskiya ina son ganin ƴar shila ta a kusa da ni, dan haka yanzu zan sa a kawo min ita nan na more." Dariya suka kuma sawa suna tafawa, Jarmai ya ce "Gaskiya ko ni ma ina da buƙatar hakan." Alhaji ya ce musu duk zai sa a kawo musu mata uku, ya kira waya ya ce kawo musu.

Suna nan zaune suna hira sai 'yan mata guda uku duk an rufe musu idanu da wani kyalle, ciki Alhaji ya nuna musu suka kai kowacce ɗaki ɗaya sannan suka fito suka tafi.. Dukkan su tashi suka yi kowa ya nufi ɗakin da yake mallakinsa ne in sun zo gidan, Alhaji yana shiga ya samu yarinyar zauna ganin shi ya sa ta miƙe tsaye tana kallon shi, shafa ƙasumbarsa ya yi yana ƴar dariya ya ɗauko wani turare a aljihunsa ya fesa mata a jiki. Kanta ne ya dinga juyawa ta lumshe idanu ya tafo ya rungume ta yana lumshe idanu, gani ya yi ta ƙara girma ta yi wani irin haske ko'ina na jikinta ya ciko ga zafin jikinta, a hankali ya ce "Sweet girl ba ki da lafiya ne?"

BuÉ—e idanuwanta ta yi ta sauke a kan shi, duk da ba a haiyacin ta take ba amma ba ta kasa ba shi amsar tambayar shi ba..

"Ba ni da lafiya ciki ne da ni." Da sauri ya kalle ta yana nanata kalmar ciki, kamo hananyenta y yi ya ce "Karki damu mu huta zan sa a zubar da cikin daga nan ma ake baki ƙwayoyin hana ɗaukan ciki." ƙura masa idanu ta yi ta kasa cewa komai sai kawai ta yi baya ta zube a kan gadon, dariyar 'yan duniya ya yi ya bi ta kan gadon. Tana jin sa yana bidirin shi amma ta kasa ko da motsa yatsar ta ne, so take ta kwace jikinta amma sam ta kasa sai kukan zuci da take.. Bayan y gama ya ɗauke ta ya kaita toilet da kan shi ya mata wanka shi ma ya yi suka fito. Wasu kaya ya ɗauko mata riga da wanda zuwa lokacin ta fara dawowa haiyacin ta ya ce ta sa, ba muso ta saka tana layi kamar ƴar maye sai lumshe idanu take. Waya ya yi ya sanar da likitansa ya zo ya same shi a gidan gonar shi sannan ya kashe, suna nan zaune ya ji kira ya shigo wayar shi ya ɗauka nan yake sheda masa ya zo. Hannunta ya kama suka fito haraba gidan inda suka same shi zaune a kan kujera cikin rufar da suka saba zama, kasancewar ya masa bayanin komai ya buɗe jakar da ya zo da ita ya zaro allura ba ɓata lokaci ya mata, sannan ya ba ta magani tare da miƙa mata ruwan da ya tarar a kan tebirin yana kallon ta ta shanye tas tana zubar da hawaye. Bayan ta sha ya mayar da ita ɗaki ya ce in ta ga jini ya soma zuba ta shiga toilet zai zo ya taimaka mata, ita kuwa da idanu kawai take bin shi har ya gama mata jawabi ya tafi.. Bayan kamar minti 40 ta soma jin cikinta yana murɗawa ta runtse idanu tana yarfa hannu, ta rarrafa ta shiga toilet nan jini ya ɓalle mata kamar ruwa haka yake zuba, tun tana sanin a inda take har ta fita daga haiyacin ta jini ya ci gaba da zuba. Alhaji ya leƙo ya ganta kamar gawa ya koma da sauri ya kira Likita suka zo a tare, tattaɓa ta ya yi ya ji ba ta numfashi ya kalli Alhaji ya ce "Da alama fa yarinyar nan ta mutu, dan ni ban ji tana numfashi ba."

A ruÉ—e Alhaji ya kalli Likita ya cakumi wuyan rigarsa ya ce "Kar ka bari na rasa ta dan tana da mahimmanci a wajena." Ya sake shi yana huci ya dawo kanta ya jijjiga ta yana faÉ—in "Sweet girl ki tashi mana kar ki min haka, in kika mutu a ina zan ke samun jin dadin da nake samu a gare ki?"

Girgiza kai Likita ya yi yana kallon Alhaji, wai yau Alhaji ne yake damuwa da yarinyar da ya sa a zubar mata da ciki? "Sai dai ka nemi wata dan wannan ba lalle tana da rai ba, yanzu bari na É—auke ta mu tafi Asibiti in ta mutu kuma kawai mu san yadda za ayi a rufe komai."

Ba dan Alhaji ya so ba ya bari Likita ya sunkuce ta suka fita ya saka ta a mota suka bar gidan..

Ƙarfe uku Suhal ya kira Abdul ya faɗa masa yaushe zai kai shi ya ga Zaiyan? Lokacin ya taso daga office ya faɗa masa su haɗu a makarantar su Abir zai je ya ɗauko ta itama ta gan shi ya masa kwatance sannan ya kashe.

A tare suka iso School din lokacin itama ta fito tana leƙo waje sai ta ga Abdul, da sauri ta fito ta shige motar shi tana masa barka da zuwa ya gyaɗa mata kai, ta kuma tambayar jikinshi nan ma kai ya gyaɗa mata sai ta ja bakin ta ta yi shuru. Suhal ya fito daga motar da ya hayo ya biya mai motar ya nufo su, sai a lokacin ta lura da shi ta ɗaure fuska tana turo baki, kallon ta Abdul ya yi bai ce komai ba hr Suhal ya buɗe baya ya shiga tare da yi musu Sallama. Sai a lokacin Abdul ya amsa masa ita kuma ta yi kamar ba ta ji shi ba, murmushi ya yi ya ce "Princess how are you today?"

Da kyar ta ce "fine."
Chapter 41 · 0% Book details