← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 120

Sashe 59

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta matso ta sunkuyar da kai, kallon ta ya yi sama da ƙasa ganin shigar da ta yi, riga ce da wando kayan sun ɗame ta sosai duk wani abu mai jan hankali a jikin mace sai da ya bayyana ga kanta babu ɗankwali. Tsaki ya ja ya ƙara daure fuska ya ce "Maza ki canza kayan nan ki sa na kirki kafin na canja miki kama a gurin nan."

Da sauri ta wuce É—aki tana kumbura baki, Kallon Ammi ya yi ya ce "Zai shigo ya gaishe ki ya ce a masa iso wajan ki."

Washe baki Ammi ta yi ta ce "To ka ce masa ya shigo." Juyawa ya yi ya bar part É—in ya nufi na Umma. Ammi ta raka shi da harara ta ce "Shi ya rasa ma wa zai aura sai wannan sauran cutar? To zan ga ta yadda za ta auru har ta je gidan sarauta, muna nan da ita a gidan nan har tsufan ta ba ta isa ba ta yi aure É—iyan mu na zaune ba su yi ba."

Yana isa Part É—in Umma ya sanar da ita ganin Khairat ta yi shigar mutumci bai ce komai ba ya wuce. Jan shi suka yi ya fara zuwa part É—in Ammi. Da murna ta tare shi suka gaisa ta gyara zama cikin kissa da iya bariki ta ce "Yawwa Yarima, dama ina son na maka wata tambaya in ba za ka damu ba."

Jinjina mata kai ya yi ta ci gaba, "Ka ce da ka je gida za ka yi wa Maimartaba magana azo ayi maganar auren Abir, to amma mun ji shuru har wannan lamari ya faru uwar yarinya ta rasu, ni dai ina so ka riƙe ta da amana ka ga dai marainiya ce ita ba uwa ba uba mu ne komai nata. Kar ka aure ta ka kaita Kasar ku ake wulaƙanta mana ɗiya a gidan sarauta, dan naji an ce in dai kai ba jinin sarauta ba ne ka auri ɗan sarauta sai ka zama abin tausayi mu kuma ba za mu so a wulaƙanta mana ɗiya ba marainiyar Allah. In har kasan ba za ka jajirce a kan ta ba to gaskiya kar ma magana ta yi nisa. " Ta faɗa irin ita ga ta ƙanwar Abie, har wani hade rai take tana girgiza kai..

Ƙara sunkuyar da kai Suhal ya yi ya ce "In sha Allahu Ammi ba zan ba ku kunya ba, kuma na muku alƙawarin ba zan taɓa bari Princess ta yi kukan maraicin iyaye ba ko na dangi, ni da Mamana da ƙanwata za mu kula da ita yadda ya kamata." Ya ƙarashe maganar yana miƙewa tsaye dan ya gaji da tsugunnawar da ya yi..

Washe baki Umma ta yi ta ce "To shi kenan Yarima, Allah ya maka albarka naji daÉ—in wannan bayanin naka."

Amin ya ce ya mata sallama tare da ɗauko kuɗi ɗauri biyu na rafa ya aje a kusan ƙafarta suka bar palon. Wani irin shu'umin murmushi ta yi ta ɗauke kuɗin ta kalli Fatima ta ce "Ku kalla a samarin ku wa ya taɓa ba ku ko da ɗauri ɗaya na irin wannan?" Girgiza kai suka yi suka ƙara jin tsanar Abir ganin yadda ta samu mai kuɗi kuma ɗan gidan mulki za ta aura su kuma ga su nan har yau ba wanda ya ce zai turo sai tara samarin kawai..

A part É—in Umma ma bayan sun gaisa sai da ya aje mata dauri biyu na kuÉ—i kamar yadda ya aje wa Ammi ta masa godiya sannan suka tafi. Tana ganin sun tafi ta yi ta dariya tana juya kudin ta shige É—aki, Khairat ta bi bayan ta...

Sai da su ABBA suka zo ya musu gaisuwa sannan ya ba su hakuri akan jin sa shuru da suka yi uziri ne y taso masa, ba komai suka ce nan ya sheda musu nan da wata uku zai turo zuwa lokacin Abir ta warware ta rage damuwa, ba su ja ba suka amince ya musu sallama suka nufi masauki...

Washegari ya so zuwa gidan su Baba amma ya fasa suka koma ƙasar su.

Haka kullum yake kiran ta yana kwantar mata da hankali ya yi ta mata hira yana ba ta labarin wani abu da ya gani a kasashen waje, tun ba ta yin magana har ta dangana ta hakura take É—an sakin jikin ta tana yarda su yi hira.

Da haka dai kwanci tashi har wata uku ya cika inda dangin Suhal suka zo aka yi maganar gemu da gemu suka fahimci juna aka sa biki wata ɗaya, sun so bikin ya wuce wata ɗaya amma suka roƙi alfarma akan cewar Maimartaba ne ya ce asa haka. Sosai suka ya ba da kirkin su Abba bayan an gama komai suka tafi gida cike da jin daɗin yadda aka karrama su....

_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:03 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~

+966577675904

Shafi na (29)

Da gudu Iman ta shigo palon tana faÉ—in "Anty Baby! Anty Baby ki na ina wai?"

Riƙe baki Grandma ta yi tana gyada kai kamar ƙadangaruwa, sai da Iman ta ƙaraso inda take ta gyara zama ta ce "Ke kuma sangadan ware daga ina?" Ta Yi maganar tana hararar ta. Dariya ta yi ba ta bai wa Grandma amsa ba ta nufi ɗakin Abir tana kwaɗa mata kira. A bakin gado ta same ta tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwali, hakan ya sa ta ƙaraso da sauri tana murmushi ta dafa ta. Hawaye ta gani akan fuskarta nan da nan fara'ar da ke kan fuskar Iman ta dauke, a ruɗe take tambayar ta.

"Anty Baby me ya faru kike kuka kuma?"

Goge hawayen ta yi ta ɗago ta kalli Iman ta ce "Ba na son na tafi na bar gidan nan Iman." Ta fashe da kuka tana daura kanta a kan kafaɗar Iman. Murmushi Iman ta yi tana bubbuga bayan ta cikin rarrashi ta ce "Haba Anty Baby, ke fa mace ce ya zame miki dole ki bar gidan iyayenki matsawar kin kai lokacin da za a aurar da ke, ki daina kuka ai za mu ke zuwa muna ganin ki kuma muna waya da ke har ma vidéo call za muke yi. Na tabbata Yaya Suhal zai riƙe ki da amana kamar yadda ya faɗa wa su Abba, yana da hankali da nutsuwa ga sanin darajar so. "

Tashi ta yi daga zaunan ta É—an yi taku biyu zuwa uku ta kalli Iman tana girgiza kai ta ce "Iman yanzu idan na tafi wa zai ke kula min da Zaiyan? Kuma kin ga ban gama karatuna ba za a min aure." Ta dawo ta zauna tare da rafka tagumi hannu bibiyu. Tsaki Iman ta ja jin abin da ta faÉ—a, dafa kafaÉ—arta ta yi tare da É—aure fuska irin ga uwar ta É—in nan za ta ja mata kunne har da su gyaran murya, kallon ta Abir ta yi ba ta ce komai ba ta kuma goge hawayen da suka sake zubo mata.

"Malama ki na ba ni mamaki wani lokacin, yanzu duk wannan fafutukar da Yaya Abdul yake akan Zaiyan ba ki gani ba? Duk wani abu da ya shafe shi shi yake yin komai sai dai in ya gama ya zo ya faÉ—a miki amma duk da haka wai har kike tunanin wa zai kula da shi dan kin yi aure? Wallahi kin ban mamaki Anty Baby, bai ma kamata ki yi irin wannan maganar ba sam. "

Ganin yadda ran Iman ya ɓaci sai ta ɗan yi murmushi ta ruƙo hannayenta cikin sanyin murya ta ce "Allah ya ba ki haƙuri Iman, ba wai ina nufin Yaya ba ya yin wani abu a kan Zaiyan ba ne, ina tunanin in na tafi zai ke ta tambaya ta sannan shi ma Yaya da ya yi aure zai rage zuwa inda suke, saboda abubuwa za su masa yawa shi ya sa kika ji na ce haka." Ta Yi maganar tana dan rausayar da kai kamar tana gaban Abdul..

Murmushi Iman ta yi ta ce "OK to tashi mu tafi palo ki zauna an jima su Abba za su shigo, dama na zo ne na kawo miki albishir bikin naku nan da wata É—aya ne wai Maimartaba ya ce a sa wata É—aya."

Wata irin faɗuwar gaba ce ta mata dirar mikiya har sai da ta dafe ƙirji tana zaro idanu, baki na rawa ta ce "W.. Wa. Wata ɗaya fa kika ce Iman?" Ta faɗa alamar tsoro ƙarara ya baiyana a kan fuskarta.

Gyaɗa mata kai kawai ta yi ta yi gaba ta bar ta dafe da ƙirji tana bin ta da kallo har ta ɓace wa ganin ta..

Wani irin kuka ne ya subce mata ta juya ta faÉ—a kan gado ta dinga rera kuka kamar yanzu ne aka ce mata Mom ta rasu.

Washegari ta shirya tsaf misalin karfe 10 na safe ta sa aka kaita gidan su Baba. Motarsu na yin packing ta hango Zaiyan a zaune yana kasa itace kamar wanda zai sayar sai surutu yake ta yi yana karkasawa, murmushi ta yi ta fito tare da nufo inda yake wani irin sanyi na mamaye mata zuciya.. Tana isowa ta tsugunna a gaban itacen tana Æ´ar dariya wadda rabon da ta yi ta ma manta ranar, a hankali cikin sanÉ—a ta janyo itacen da ke gefen shi tana kunshe dariyar da ta zo mata sanin halin shi.

Da sauri ya juyo ganin ana jan masa itace, karaf suka hada idanu ai kuwa ya zabura kamar an tsikare shi ya miƙe tsaye ya soma dariya yana faɗin "Shege Baba ashe gaskiya ya faɗa min shekarar da ta gabata, dama ya ce ba zai ƙara sace ki ba kina kuka sai ga shi kin zo gidana, me kike so Anty?" Ya faɗa yana zama a daf da ita ya yi tagumi hannu bibiyu ya kafe ta da idanu.
Chapter 59 · 0% Book details