← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 120

Sashe 35

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba zan taɓa cutar da shi ba, baƙar guba ce a jikinnshi nake fitar masa da ita, yanzu ta fita." Tana gama faɗin haka ta ɓace ɓat daga palon. A mugun tsorace ta dinga waigawa ko'ina à tunanin ta za ta ganta kamar dazu amma ta ga wayam.

A hankali ta tashi tsaye shi ma ya tashi ya tsaya à gaban ta, gabadaya ji ta yi ba za ta iya barin shi a gidan nan ba dan zuciyarta ba ta kwanta da ganin wannan macen ba, hannunshi ta kama ta zaunar da shi à kan kujera ta isa bakin ƙofa ta ɗauko handbag ɗinta yana biye da ita. Hannun shi ta kama tana gyara zaman mayafinta gabadaya jikinta sai rawa yake shi kuma sai surutu yake mata, bude kofar ta yi suka fito waje sai buga sauri take Allah-Allah take su fita daga cikin gidan gabadaya. Cin karo ta yi da su Baba ta ja ta tsaya tana kallon su, Baba da Inna suka haɗa baki wajan faɗin " 'Yar nan yaushe kika zo? Kuma ina za ku je ?"

Sake ɗamke hannun shi ta yi tana jin ranta na baci na barin shi da suka yi suka tafi shi daya a gidan, ajiyar zuciya ta sauke ta ɗago ta kalle su cikin bacin rai, baki ta buɗe da nufi magana sai kawai ta fashe da kuka. Sake da baki suke kallon ta suna mamaki daga tambayar ta sai kuka, Inna ta matso kusa da ita ta ce "Haba yar nan mène ne kuma na kuka ? Muje ciki kin ji." Kama hannunta Inna ta yi tana ba ta haƙuri ta ja ta suka nufi ciki, Baba ya kama hannun Zaiyan duk da ɗayan nasa hannun a cikin n'a Abir yake.

Suna shiga ciki Inna ta shiga ta dauko mata ruwa mai sanyi ta miƙa mata tana faɗin" Sha ruwan. "

Ba ta musa ba ta amsa ta sha ruwan tana sauke ajiyar zuciya, ji ta yi zafin zuciyar na sauka sauran ruwan da ta yi ta miƙa masa. Amsa ya yi ya sha ya yi lamo a gefen ta yana wasa da handbag ɗinta, Baba ta gyara zama ya dube ta ya ce "Wai me ya faru yar nan?"

Baki ta buɗe da niyar faɗa musu duk abin da ya faru amma sai ta ji ta kasa fada, ƙwalla ce ta cika mata idanu so take ta faɗa ko za ta samu sauki da firgicin da ta shiga, ƙila Baba ya taimaka mata amma bakin ya kasa furtawa sai ajiyar zuciya da take sauke wa. Lum ta ji kan ta ya yi kamar wacce hajijiya ke shirin ɗauka ta dafe kan tare da miƙewa, ji ta yi hankalin ta ya koma gida ta warci handbag ɗinta ta nufi ƙofar fita da sauri.

"Anty zan bi ki."

Ta ji ya faɗa, saurin buɗe ƙofar ta yi ta fita tana sauri kamar za ta kifa. Zaiyan shi ma ya biyo ta yana kiran sunan ta yana cewa sai ya je tare da ita amma ko kallon shi ba ta yi bare ma ta tsaya ya iso inda take. Sai Yanzu ta tuna wayarta ta zarga jaka ta fito da wayar, kamar jira ake ta fiddo sai ga kiran Ali ya shigo ta ɗaga tare tsayawa da tafiyar da take ta zo gaf da jikin get ɗin gidan ta kama ƙofar ta riƙe tana jin abin da yake faɗa.

"Hello Madam kina lafiya?"

Sauke ajiyar zuciya ta yi jin ya riƙe mata hannu, sai da ta yi kusan minti biyu tana riƙe da wayar Ali ya ji shuru ya sake yin magana, kana ta daure ta ce "Kana ina Ali? Duk ma inda kake ka zo ka ɗauke ni daga gidan nan." Ta karashe maganar murya na rawa.

"Madam gani nan zan shigo maza ki fito." Ya faɗa yana fitowa daga cikin motar ya kama get ɗin ya tura. Da sauri ta ja da baya tana zare idanu, À sukwane Ali ya shigo yana mai ɗane kunamar bindigar shi, dafe eapis ya yi dake kunnensa ya ce "Hello Oga kana kan layi ?"

Daga can ɓangaren Abdul da ke ta safa da marwa a harabar Office ɗin su ya ce "Ali ina Baby take? Ina fatan babu abin da ya same ta dai ko ?"

Gyada kai ya yi yana kallon Abir da ta yi tsuru-tsuru kamar ka ce mata kaiya ta kwasa a guje, ya ce "E Oga amma dai kamar ba a haiyacin ta take ba, tabbas akwai abin da ya firgita ta."

Maza ku fita daga gidan gaf kuke da inda suke, suna nan suna biye da ku ka kula Ali kar wani abu ya samu Baby ko shi Zaiyan É—in."

To Ali ya ce ya dubi Abir ya ce" Madam mu je gida. " Ba ta ce komai ba ta yi gaba Zaiyan na riƙe da hannunta shi kuma ya mara musu baya, a bakin motar police shida ne da motoci biyu bayan wadda ya zo da ita, abin sai ya ba wa Abir mamaki sun zagaye da motocin kowa cikin shirin ko ta kwana, ganin ta ya sa suka bude mata mota suka shige..

Suna shiga motar suka bar wajan da sauri.

Suna barin wajan sai wata jar mota ta iso ƙofar get ɗin, buɗe motar aka yi wani sangameman mutu ya fito daga motar sanye da baƙin glas ya nufi get ɗin ya soma ƙoƙarin buɗewa, gam ya ji an rufe ya buga da ƙarfi ya dawo yana hura hanci ya shige motar suka koma ta hanyar da suka fito...

Gudu sosai Ali ke yi Abdul na fada musu inda za su bi, sosai suke gudu suka shiga cikin tsakiyar gari. Sai da suka zo wata Unguwa ya ce su rage gudun suka rage, bayan sun kutsa cikin Unguwar ya kira Abir. Dauka ta yi jiki na rawa ta kara à kunne ta ce "Hello Yaya."

"Baby are you OK?"

Goge hawaye ta yi ta ce "E Yaya amma mun tafo da Zaiyan kar Baba ya ga kamar ba mu girmama shi ba."

"Baba kuma Baby? Kin ga gani nan zan zo na É—auke ki mu tafi gida."

To ta ce ta kashe kiran, juyowa ta yi ta ga ya yi bacci kawar da kanta gefe ta yi tana kallon Unguwar...

Wani get suka nufa suka yi hon aka buɗe musu suka kutsa ciki, ita dai Abir kamar wata sakare haka ta saki baki tana kallon gidan kamar ba ta taɓa ganin gida irin wannan ba, sai da aka buɗe motar sannan ta nutsu ta fito daga motar. Kallon Ali ta yi ta ce "Ali to ya yi bacci fa."

GyaÉ—a mata ya yi sannan ya ce "Oga ya ce kar a fito da shi zai iso yanzu." Ba ta kuma cewa komai ba ta ta yi shuru tana mai Kallon gidan, ji ta yi ya birge ta.

Motar Abdul ce ta yi hon aka buɗe masa ya shigo, kafin ma à gama packing ya buɗe ya fito yana yin dogon zari irin na zaratan mazaje ya nufo su, tana ganin shi da sauri ta nufe shi suna haɗewa ta faɗa jikinshi ta saki kuka. 'Hmm' Ya ja dogon numfashi yana yin hamdala da ya gan ta cikin ƙoshin lafiya, hannu ya sa ya raba ta da jikinshi ya ɗan rankwafo daidai saitin kunnenta, hucin da ya yi a saitin kunen ya sa ta buɗe ido da sauri tana tsayar da kukan.

"My Baby ke ba ki ganin akwai wasu bayan mu? Me ya faru kike kuka?" ya faɗa cikin yin ƙasa da murya in ba a gaf da su kake ba ba za ka ji mai yake faɗa ba. Goge hawayen ta yi ta ce "E ba komai, amma Yaya me ya faru na ga kasa an kawo mu nan?" Ta faɗa tana tsura masa na mujiya. Hannunta ya kama ya ɗago ya kalli su Ali da suka ƙame a wajan, gyara tsayuwar shi ya yi ya ce "Ali ku shigar da shi ciki ku kula da kyau zan je na dawo ?"

"OK Sir!" Suka faÉ—a a tare suna sara masa cikin girmamawa, shi ma sara musu ya yi kana ya juya ya shiga motar direba ya ja suka bar gidan..

Damun shi ta yi da maganar wannan gidan shi kuma ya mata shuru, ganin za ta sa masa ciwon kai ya juyo cikin nutsuwa ya dago habarta da yatsu biyu yana mata wani irin Kallo, itama kallon nashi ta yi tana narke fuska kamar za ta yi kuka,. A hankali ya kai fuskar shi daf da tata numfashinsu ya hade, baki ya kai kan kumatunta ya sumbace ta yana sauke ajiyar zuciya, sai da ya ga ta nutsu sannan ya saki fuskar ya juyo da ita suna kallon juna ya ce "Baby kin takura sai na fada miki abin da ya faru à gidan su Baba ko ?" Saurin gyaɗa masa kai ta yi da sauri, ya ci gaba "Wasu ne suka je gidan shi ne har suka sassari Baba da Inna, yanzu haka ma suna Asibiti à kwance Inna ta fi Baba raunatuwa. To sai bayan Ali ya kaiki ya aje ne muka samu labarin tun jiya da dare wajan karfe uku da rabi aka faɗo gidan, wani makocinsa ne da suka saba zuwa Masallaci tare ya ga bai je Sallah ba ya yi mamaki na rashin ganin shi. Sai da rana ta yi ya je ya ƙwanƙwasa gidan ya ji shuru sai ya tura kofar ya ga ta buɗe ya yi sallama ya ji shuru, hakan yasa ya dan leƙo cikin palon nan ya gansu kwance cikin jini. Hankali a tashe ya fita ya kiran yaranshi maza 2 suka shigo suka duba suka ga suna numfashi sai suka kwashe su zuwa Asibiti amma shi Zaiyan ba su gan shi a gidan ba. To bayan kin tafi shi makocin nasa ya kira ni ya min bayani Baba ne ya farfaɗo ya ba shi number ya kira, shi ya sa kika ji ina ce miki babu abin da ya same ki. " Ya ƙarashe maganar yana kallon ta..
Chapter 35 · 0% Book details