Sashe 85
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka sosai Iman ke yi jin halin da ƴar'uwarta ta take ciki, wai yau Abir ce a gidan haka wanda ko a mafarki ba ta yi tsammanin haka ba? Ƴar'uwarta ƴar ƙwalisa ƴar wanka marar hayaniya ga Sanyin hali da tausayin al'umma ga kuɗi duk Nigeria ana sa Abie a jerin masu kuɗin ƙasar amma ita ke rayuwa a gidan haya? Goge hawaye ta yi ta ce "In da za ki yarda zan nemi alfarma a wajan Yaya Suhal ki dawo nan ƙasar da zama, kin ga za mu zauna a gari ɗaya."
Girgiza kai Abir ta yi ta ce. "Karki damu Iman ba sai na je Niger ba anan ma ina jin daÉ—in zama da mutanen gidan, kawai ki tayani da addu'a Allah ya ba ni ikon cinye jarabawar da ya mini, ina Yaya Suhal É—in yake?"
Wayar ta miƙa masa ya ƙara a kunne cike da tausayin abar Ƙaunar tashi dan duk abin da suke faɗa ya ji, a sanyaye y ce "My Princess barka da warhaka."
Murmushi ta yi ta ce "Ka ga malam ka fa daina ce min princess ɗin nan dan ni ba ɗiyar masu rawani ba ce, ni yanzu Antynka ce." Ta faɗa tana ƴar dariyar yaƙe.
Shi kan shi yasan ba dan jin nishaÉ—i ta yi dariyar ba, ta yi kawai dan ta kawar da hirar tasu. Gaisawa suka yi tana tambayar su Mamma ya ce suna lafiya, tukun ya ce " Tsaya-tsaya Princess karki kashe ba ni abokina mu gaisa."
Murmushi ta yi tana kallon Zaiyan da tun tana yi wa Iman jawabi ya tashi ya tsare ta da idanu, miƙa masa wayar ta yi ta ce. "Ka mlamsa ku gaisa da abokinka da zai kaika London."
Maƙale kafada ya yi ya murza idanuwansa ya ce "Ni na daina kula shi ba ya tsoron Allah ya min karya." Ya faɗa yana rufe idanu irin ya yi baccin nan. Ƴar dariya ta yi ta ce "To ka dai ji bai manta maganar ku ba, idan ya huce kun gaisa wataran."
Jinjina kai ya yi ya dinga tambayarta a wacce unguwa take in wani abu ya kawo shi Nigeria ya kai mata Iman, amma fir ta ce masa kar ya damu za ta faÉ—a masa ba yau ba sai wani lokacin, ganin ma za su takura mata ta kashe wayar gabaÉ—aya...
_Maman Nusaiba ce_
[11/23, 9:35 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na (42)
Sororo ya yi da wayar jin ƙit ta kashe, Iman da ta yi zaman dirshan a tsakiyar gadon ta kafe shi da kallon ya mata ƙarin bayani, aje wayar ya yi a gefe yana furzar da askar cikin bakinsa ya ce "My Iman zan tafi wani taro wanda aka gayyaceni ni da 'yan'uwana, so kar ki fita ko'ina dan su Mamma ba sa nan sun ɗan fita su sha iska amma a cikin masarautar nan wajan yake, idan ki na so zan kaiki sai na wuce."
Tun da ya fara maganar ta kafe shi da idanu har ya dasa aya, matsowa ta yi kusa da shi a sanyaye ta ce "Yaya Suhal please ka taimaka ka mayar da ni ƙasarmu, ka ga danginka ba sa so na saboda ni ba jinin sarauta ba ce, gaskiya ni ba zan iya zama ana wulaƙantani ba, ka mayar da ni wajan iyayena kawai." Ta faɗa tana riƙe hannunsa hawaye na zarya kan kuncinta.
Shuru ya yi yana jinjina ƙarfin hali irin na Iman, haka za ta tasa shi a gaba ta yi ta kuka kamar an yi mata wahayin sa ta ce ita fa ba ta son shi ya sake ta kawai ta koma gida, lallaɓa ta yake ya mata wayo har ta daina kukan ya hana maganar, cikin satin nan kuma abin ya yi yawa kullum sai ta ce ya sake ya mayar da ita wajan iyayenta ai dama ita ba ta ce tana son shi ba.
Kuka ta sa mana tana kai masa duka sai faɗi take "Wallahi ba ka isa ba sai ka sakeni ka mayar da ni wajan dangina, ni ba zan ci amanar ƴar'uwata ba." Haka ta dinga faɗa tana tura shi baya amma ko gizo bai yi ba, ba ya jin daɗin Kalmar sakin nan da take ambata, amma ita ko a jikinta abin ma ya zame mata jiki. Ruƙo hannunta ya yi ya saita nutsuwarsa irin ba wasa ɗin nan, da kyar ya ce "Iman me ya sa ke har yanzu kin kasa gane daidai da rashin daidai wajan furta wa mijinki kalamai? Babu kyau mace ta dinga ambatar Kalmar saki wannan ba ɗabi'ar mace ta gari ba ce, ki daure mu rungumi ƙaddararmu sai ki ga Allah ya sanya mana soyayyar juna duk da ni na jima da son ki a zuciyata, ke ce dai gabaɗaya kin kasa yarda da ƙaddarar Ubangiji. Don Allah Iman ki yi haƙuri mu tabbatar da zamar a mata da miji mu gode wa Allah akan abin da ya tsara a kanmu, ki sani ba wai dan bana son Princess ba ne na ce ke zan aura, ina da nawa dalilin akan hakan kuma na sadaukar da soyayyata ne dan na ceto rayuwar princess, dan haka Ko da wasa ba zan taɓa sakin ki ba ni da ke mutu ka raba, idan ki na son zuwa Nigeria zan kaiki amma ba yanzu ba."
Kallon ka raina min hankali ta masa tare da yin kwafa tana hararar shi cike da takaicin ya sharara mata ƙarya da ya ce wai dan Anty Babynta ya yi hakan, hanci ta hura tana huci sai hawa take kamar fulawar da taji yiss. Dariya ta so ba shi amma ya gumtse dan ya nuna mata kuskuren ta, zaunar da ita ya yi a kan cinyarsa ya ɗago da fuskarta, buɗe idanu ta yi cike da masifa ta sauke su akan nasa idanuwan, ba shiri ta kawar da kai duk faɗan da take jin za ta yi masa gabaɗaya ta ji ta saduda ta sunkuyar da kai, gyara zama ya yi ya yana lumshe idanu gabaɗaya ta hana shi sukoni kallon da take masa ya sa shi shiga yanayi. Jin bai ce komai ba ta fusata ta ce "Malam ka ga kar ka wani yi min daɗin baki, in da gaske kake dan ka ceto rayuwar Anty Baby ne me ya sa ba ka aure ta ba a lokacin da ta fi kowa buƙatar ka? Saki dai dole ka sakeni naje na auri wanda nake so ehe, sai ka wani zaunar da ni kana wani tsara min magana kai ga ka sarkin iya magana ko? To ba zan yarda ba. " Ta faɗa tana murguɗa masa baki.
Girgiza kai ya yi yana jin gabaɗaya ta caza masa kai har wani ciwo kan yake masa, shigar da ita ya yi jikinsa yana fitar da wani kalar numfashi wanda ya yi sanadiyar tsoratar da Iman ta soma kiciniyar kwacewa, ƙin ba ta damar hakan ya yi dan dole ta yi lamo a jikinsa tana sauraron ta ji wata maganar zai tsara mata. Sun fi minti biyar a haka shi bai ce uffan ba itama haka dan so take ya sake ce mata wani abu ta masa tatas kuma ta takura masa dole ya sallame ta ta koma gidansu, can ta tuna da Sajida ai kuwa ta tattara duk ƙarfinta ta yakice shi daga jikinta ta diro daga kan gadon, ita sai yanzu ma ta tuno ashe fa yana da wata matar bayan ita ga shi har yau ba ta gan ta ba a gidan. Kama ƙugu ta yi tana jijjiga sai hura hanci take ta ce "Ni fa ko mai za ka faɗa ba zan taɓa yarda ba ehe, haka kawai ka wani tsare ni da surutu to ina matarka take ma wadda Anty Baby ta ba mu labarin ta? Saboda rashin adalci ba ka taɓa haɗa mu mun gaisa da juna ba ko ka kaini part ɗin ta, saboda ita ɗiyar gwal ce shi ya sa ko fitowa part ɗin Mamma ba ta yi ita ƙasatacciya ko? To Wallahi ni Iman na fi karfin kishiya ta min gani-gani dan ba zan dauki raini ba ehe, kuma in dai har kana son na tabbatar da kana da adalci to ka kira ta ta zo nan palonka mu ga juna, in ba haka ba da kaina zan gudu na koma garinmu. " Ta faɗa tana turo ɗankwali gaba..
Tun da ta fara maganar yake kallon ta cike da birgewa, indai tana yin masifa wani irin kyau take masa na musamman, shi ya sa ko tana masa rashin kunya yake rabuwa da ita ta yi ta gaji dan kanta ta bari, wani ƙayataccan murmushi ya yi ya miƙa hannu zai janyo ta ta matsa da sauri tana hararar shi.
"Alƙur'an ka taɓani sai na tara ma mutane a gidan nan." Ta ƙara matsawa.
Shammatar ta ya yi ya damƙo hannunta ya janyo sai ga ta a kanshi, ɗaure fuska ta yi irin ba wasa ɗin nan ta ce. "Malam cikani wanka ma zan yi."
Zaunar da ita ya yi a gefen shi ya rasa da wani yare zai fahimtar da ita ta gane, zuro ƙafafuwansa ya yi bakin gadon ya soma yi mata magana.
"Iman bana so ki sake furta kalmar sakin nan, nasan kin je islamiya kuma an koyar da ke komai ciki kuwa har da macen da za take cewa mijinta ya sake ta salin alin ba lefin tsaye ba na zaune, Ubangiji shi ya halitta saki a tsakanin ma'aurata amma ba ya son ayi shi, duk lokacin da aka yi saki al'arshin Ubangiji sai ya girgiza, ni kuma a tsarina ba zan taɓa rabuwa da ke har abada. Kar na kuma jin kin ce na sakeki babu kyau wannan kalmar ta fito daga bakinki a matsayinki na musulma wadda ta yi imani da Allah da ƙaddara a kowanni lokaci ta riske ki ki amsa hannu bibiyu ki gode wa Lillahi wahidulƙahar, sai ki ga ya miki sakamako da aljana mfificiya ranar gobe ƙiyama... "