← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 120

Sashe 45

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai ya yi bai ce komai ba, shi kan shi ba zai so ya mata irin haka ba amma ya zai yi? Ya ganta ne a bazata a lokacin da ya cire rai da ganin ta na har abada, sai ga shi Allah ya sa zai su ga juna, a nutse ya ce "Inna ba da ita na zo nan ba, ban taɓa tunanin ma zan sake saɗuwa da mai kama da ita ma, dan ta ɓata shekaru biyar cif mu a tunaninmu ma ta mutu ashe tana raye."

Kallon ban fahimta ba Inna ta yi wa Suhal, sai kuma ta riƙe baki ta ce "Ku ma dama a Niger ɗin ana yin kidnaping?"

Girgiza mata kai ya yi ya É—an muskuta sannan ya ce "Mu gaskiya irin wannan lamarin na sace-sace a Niger ba a yisa, ko kuma na ce a Jaharmu ba a yi, itama a nan Nigeria aka sace ta."

Abin da Abir dama take jiran ji ta É—ago ta kalli Suhal karaf suka haÉ—a idanu da Sajida ta yi saurin kawar da nata, fuskarta a gefe ta soma magana. "To amma Ya Suhal ku da kuke Niger me ya kawo Sajida Nigeria har aka sace ta?"

Nisawa ya yi sannan ya ce "Princess ƙaddara ce ta kawo ta da bin shawarar ƙawa." Ya faɗa yana tunano abin da ya faru a baya ransa na ɓaci kamar yanzu ne abin da Sajida ta aikata masa yake gani..

Nan da nan idanuwan Sajida suka cika taf da hawaye, na nadama da da-na-sanin ƙawar ta ta mamaye ta wanda a kullum take tun cikin yi da ta faɗa iftila'in nan. Goge hawaye ta yi ta kalli Abir ta ce "Ni zan faɗa miki duk abin da ya faru, da kuma soyayya ta da Suhal har ya kai ga an daura mana aure.".

Gyara zama Abir ta yi cike da zaƙuwa ta ƙagara ta ji labarin Sajida.

"Ni sunana Sajida haifaffiyar garin Niamey, Babana ɗan Niamey ne Mamana ƴar Kano. Mu biyu ne a wajan iyayenmu ni ce babba sai ƙanwata Halima. Tun da na taso nake da son tara ƙawaye a ganina in kana yin ƙawaye to kai wayayye ne kuma me class, hakan ce ta sa tun ina yar shekaru 17 na tsunduma harkar social media Wanda a nan ne na haɗu da wata a Facebook ana ce mata Bishira, cikin ƙanƙanin lokaci muka ƙulla kawance da Bishira ganin yadda take nuna min kulawa na saki jiki da ita. Wata rana na hau online na ga ta yi post ta je Abuja ita da 'yan gidansu har ta yi tagging dina a sahar, sosai suka birge ni na bi ta prvt na ce mata "Ƙawata kin yi matuƙar kyau fa."

Ina tura mata ta dawo min da amsa tare da emoji ɗin da ke nuna ta ji daɗi, nan muka dinga hira inda a nan take faɗa min cewa wasa take min da ta ce ita a Kaduna take ita ƴar Kano ce cikin gari, na ɓata rai sosai dan ni a rayuwata na tsani ƙarya, na ce mata kar ta sake min ƙarya akan abin da ya shafe ta na dauke ta ƴar'uwata take faɗa min gaskiya akan komai nata. Ganin na fusata ya sa ta ba ni haƙuri ta ce ba za ta sake ba na haƙura muka ci gaba da magana.

Ko a gari kawayena sun fi shida, kuma kowacce muna tare da ita muna chat sosai,.

Mun kai shekara da haɗuwa da Bishira sai take ce min ai ita yanzu ta koma Istagram ni ma na buɗe yanzu ba sosai za take hawa Facebook ba, a lokacin jiki na rawa na je na rubuta sunan shi a play store na sauke a waya na buɗe. Buɗe Istagram ɗina da wata ɗaya na haɗu da Suhal, ganin yana yawan rufe fuskarsa in zai ɗaura photonshi sai abin ya birge ni na dinga bibiyar duk wani post ɗin sa, naji ya shiga raina ban ankara ba na kamu da matsanancin son shi na kasa sukoni. Wasa-wasa abin ya soma saka ni tunani ga shi ni a matsayina na mace wadda aka san ta da kunya da kawaici bai kamata a ce na tunkari Suhal da maganar so ba, haka na kasance abin duniya ya isheni har sai da Mamana ta same ni wata rana a ɗaki ina ta zubar da hawaye na ciwon so, mamaki sosai ta yi da ganin ina kuka ta zauna a kusa da ni ta dafa kafaɗata na zabura sai na ga ita ce, a sanyaye ta ce da ni, "Sajida wai lafiya na ga kwana biyun nan kin koma wata iri? Me ke damun ki wai? Ki faɗa min." Rasa me za faɗa mata na yi na faɗa jikinta na saki kuka tamkar marayan da aka hana abinci, hankalin ta ya tashi ta dinga tambaya ta amma na kasa magana, ganin ta shiga tashin hankali sai na sassauta kukan nawa na soma tattaro ƙaryar da zan shirga mata. "Mama Wallahi wasu irin mafarkai nake marar kyau, da na kwanta sai na yi shi y asa duk na damu."

Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta dube ni tsaf, ta so ta ƙaryata maganar tawa amma ta ƙi yarda mu haɗa idanu, a sanyaye ta ce "Kuma shi ne duk kika tashi hankalinki? Mafarki fa ba gaskiya ba ne Sajida, amma ki dinga yin addu'a in za ki kwanta, ko kuma zan koya miki wasu addu'o'in in za ki kwanta sai na shigo na koya miki." Da to na bi ta har ta fita daga ɗakin.

Ina so na yi wa Suhal magana amma ina tsoron ya min wulaƙanci, a ganina shi ɗin ɗan masu kuɗi ne duk da a lokacin ban san ya kamannin shi yake ba, wata ranar Lahadi na ɗauri aniyar yi masa magana ta dm ɗin sa ko da ba zai kula ni ba, haka kuwa aka yi karfe goma na dare na hau online na shiga dm ɗin sa na masa Sallama tare da sheda masa ina ɗaya daga cikin friend ɗinsa. Abin mamaki ina turawa aka buɗe amma ba amsa, ban yi zuciya ba washegari ma haka na tura masa saƙon barka da safiya, nan ma ya buɗe amma ba amsa sai abin ya ƙular da ni matuƙa na ja tsaki na aje wayar.. Ina so na manta da shi amma zuciyata ta kasa na kwana ban yi ba bacci, kullum da photonsa nake kwana a ƙirjina wanda na ɗauka a Instagram ɗinsa na kai aka wanke min shi, bana son kowa ya gani shi ya sa na ɓoye shi sai zan kwanta dauko kasancewar ɗakina daban na ƙanwata daban..

Da dare na hau online na shiga Instagram ina addu'a ko zan ga saƙon Suhal, kamar a mafarki na ga saƙon shi ya shigo min, hannuna na rawa na shiga zuciyata na wani irin zillo na son ganin abin da ya fada min.

_"Wa alaikum salam. Ma sha Allah da fatan kina lafiya, lokacin da kika turo saƙon duk ba ni na buɗe ba ƙanwata ce wayar na hannunta."_

Wani irin daÉ—i naji a lokacin a raina ina cewa 'Ashe ma ba shi da girman kai irin na É—iyan masu kuÉ—i.' Da sauri na mayar masa da amsa.

"Ayya Allah sarki! Ai na ɗauka ko kaima wulaƙanta mutane gare ka, ashe ba haka ba ne."

Emoji ɗin murmushi ya turo min tare da sake turo emoji wanda ake haɗe hannu alamar afuwa, dariya na yi mai sauti muka gaisa ya ce min zai sauka babansa na kiran shi, ba dan na so ba na masa sallama ya sauka. Da dare na sake taɓo shi na ci sa'a yana kai muka gaisa ina tambayar shi ina ƙawar tasa ya ce ta yi bacci, mun yi hira ba lefi tukun muka yi sallama..

Wasa-wasa muka zama abokai har muka dawo whatsapp da yin chat, kuma har lokacin ban yi gangancin furta masa kalmar so ba, illa kawai ina nuna masa ita a aikace, ina ba shi lokacina da zarar y min magana, ina damuwa da duk abin da ya dame shi, ko ciwon kai yake sai na wuni ranar ina kiran shi a waya amma sai taƙi shiga, haka nake ta dakon son shi har muka yi kusan shekara a matsayin abokai..

Wata rana kamar a mafarki na tashi daga bacci na ga saƙon shi wanda ya sa na kurma ihu daɗi ban sani ba..

_Sajida a gaskiya na yaba da hankalinki, hakan ya sa na ji kin kwanta min à rai dan haka na ji ya kamata na gabatar miki da kaima kafin na cuci kaina, da fatan ban miki yaro ba shekara ta 26,da fatan ba wanda ya shiga gabana?"_

Saƙon da ya turo min kenan wanda ya sa na yi ta murna ina jin kamar na fi kowa sa'a a duniya, dan haka na mayar masa da amsa.

_"Yayana kenan, ai babu macen da za ka ce kana so taƙi ka sai dai in ba ta san kai ba ne, amma zan yi shawara duk abin da na yanke zan sanar da kai."_

Bayan ya É—aga ya ce kar a dauki lokaci kwana É—aya tak ya ba ni, ni kuma ina jin daÉ—i na ce masa to.

Washegari na tabbatar masa da na amince da soyayyar shi a gareni, ya yi murna sosai ya kuma ce min shi fa ba da wasa ya zo ba da aure yake sona. Ban ji wani É—ar ba na ce masa ai ni É—in ma lokacin aurena ya yi.

Haka muka dinga ba wa junanmu kulawa har ya haɗa ni da ƙawar shi Ikilima muka saba da ita, sai da ya ga mun shaƙu sosai ya sanar min da ko shi waye, ranar kasa bacci na yi jin shi ɗan gidan sarauta ne, na shiga fargaba sosai a tunanina ba za a bari ya aure ni ba..

Kwatsam sai ga shi an turo gidanmu daga masarauta ana nemawa Yarima aurena, ranar naji farin ciki sosai amma fargaba ta hana farin cikin ya bayyana, ita kanta Mama sanyi ta yi saboda zaman gidan sarauta yana cike da ƙalubale marar iyaka rashin daɗin sa ya fi jin daɗin yawa..
Chapter 45 · 0% Book details