← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 120

Sashe 102

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo kawai ta bi bayan su har suka fita, sai da Abir ta dawo suka nufi ɗakin Tasakkawato suka zauna, ƙasa hakuri ta yi ta ce "Jiddo ki yi min bayani mana kin bar ni a duhu."

A kunyace ta faÉ—a mata abin da ya faru daga lokacin ya samu lafiya, tana gamawa ta kuma rufe fuskarta ji take kamar a gaban Mommy take ta sanar da ita abin da ya faru. Hannu Tasakkawato ta daga sama ta ce "Alhamdu Lillah, na tayaki murna Jiddo da mijinki ya samu lafiya ma sha Allah."

Ita dai daga haka kasa cewa ta yi komai kanta a ƙasa, sai da ta gaji da surutu ta ga dai ba ce mata komai za ta yi ba ta tashi suka fita inda take faɗa mata ɗiyar ɗaya daga cikin ƙawayen ta ake yi wa aure, Allah kiyaye Abir ta ce ta wuce...

Bayan La'asar ta samu wasu yara biyu sun zo kitso, sai da ta duba kibiyar kitson ta rasa hakan ya sa ta sa hijabi ta nufi gidan Aisha ta aro. Ko kofar gidan ba ta ƙarasa ta ji an yi sama da ita ta faɗa cikin wani abu, ihu take son yi ta ji an rufe baki ruf....

*Maman Nusaiba ce

[12/8, 12:48 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI*

Shafi na 50

Shuru-shuru suka ji ba ta dawo ba Maman Amal da ta fito daga ɗaki riƙe da hannun Amal ta tsaya tare da riƙe baki, ganin yaran zaune dan tana shirin shiga ɗaki ta ɗan kwanta Abir ta fita, ƙarasowa ta yi ta ce "Wai Jiddo ɗin ba ta dawo ba ne? Ɗaya daga cikin su ta mike tsaye cikin nuna damuwa ta ce" Wallahi fa har yanzu ba ta dawo ba, kuma ni ina da zuwa wajan birthday ɗin ƙawata da dare, ga shi ba ta ma gama min kitso ba ballantana ayi maganar ƙunshi gara na tafi kawai dan kar na ɗauki lokaci Mamana ta ga kamar ko wani wajan na biya." Tana gama faɗin haka ta wuce abin ta, ganin haka ya sa itama ɗayar ta bi bayan ta suka wuce suna mita...

Zama Maman Amal ta yi sai ga Tasakkawato ta dawo da kaya niƙi-niƙi a cikin ledoji, da kallo ta bi ta har ta aje kayan a bakin kofar ɗakinta tana sauke numfashi, juyowa ta yi ta kalli ƙofar ɗakin Abir ta ce "Jiddo fito kar ki yi girki na kawo muku abinci har da marar dafawa ma."

Maman Amal ganin Tasakkawato ba ta kula ta ba sai ta É—an matso kusa da ita ta ce "Tasakkawato Jiddo fa tun ba yanzu ba ta fita amsar kibiya a wajan Aisha amma shuru ba ta dawo ba."

Saurin kallon ta Tasakkawato ta yi tare da dafe ƙirji ta ce "Subhanallahi! To me ya hwaru da ita? Kin ga bari na shiga gidan Aisha naji." Ba ta tsaya jin komai ba ta wuce da sauri ta sururutai.

Ko da ta je gidan Aisha ta samu ba ta ma gidan babu kowa, haka ta juyo ta dawo tana sallallami. Abu kamar wasa har bayan isha'i ba ita ba labarin ta, duk sun zauna sun yi jugum-jugum musamman Tasakkawato sai suka ji karar waya a ɗakinta, tashi Maman Amal ta yi ta shige ɗakin. Wayar ta gani a gefen katifarsu ta ɗauka tana bin sunan da ke kan screen ɗin wayar da kallo, ganin an rubuta *Abzai*, miƙa wa Tasakkawato ta yi cikin sauri ta ɗaga babu jinkiri tare da cewa "Hello wane na?"

Muryar Zaiyan ta ji yana fadin "Am so sorry Jiddo gani nan zuwa gida ina kan hanya."

Tasakkawato ta ƙara faɗin "Kai ba ita ta ba, ka yi maza ka dawo akwai matsala." Tana faɗin haka ta katse kiran,.

Suna nan zaune sai ga shi ya shigo gidan da Sallama, amsa masa suka yi Maman Amal ta saki baki tana kallon shi jin ya yi magana, ganin a halin da ake ciki sai ta haÉ—iye tambayarta ta kalle su, tsayawa ya yi a gaban Tasakkawato fuskar nan tasa ba alamar annuri ya ce "Mama ina ta ce muku za ta je?"

"Wai gidan Aisha za ta amso kibiya ta rasa tata, to shi ne fa har yau ba ta dawo ba."

Shuru ya yi yana kallon gefen suka zuba masa idanu, sai da ya É—auki lokaci a haka sannan ya É—an yi taku biyu zuwa uku ya juyo, furzar da iska bakinsa ya yi cike da tsananin jin zafin da zuciyarsa ke masa, har zai yi magana kuma ya fasa ya ciro wayarsa ya daddanna wasu numbobi ya kara a kunne. Ringing É—aya a na biyu aka dauka, shuru ya yi alamar yana sauraron abin da ake sanar da shi, sai zuwa can ya nisa ya ce "OK thank you." Daga haka ya katse kiran ya nufi É—aki yana faÉ—in "Ku kwantar da hankalinku in sha Allah zan nemo ta da kaina."

Tasakkawato ta biyo bayan shi tana fadin "Kayya! To kai da ba gari ka sani ba taya za ka iya nemo ta? Ba ma wannan ba ba ka san a wani waje take ba, kawai dai lalibe ne za ka yi a cikin duhu."

Bai ce mata komai ba ya shige É—aki ya bar su a tsaye suna maida yanda aka yi..

Jar mota sabuwa dal ce ta yi packing a wani gida, wanda kafin ma ka shiga za kake juyo kiɗa na tashi. Fito da ita suka yi idanuwanta a rufe suka nufi ciki da ita, sosai 'yan mata da samarin ke cashewa a cikin wannan gida, Wasu na shan giya, wasu na rungume da samarinsu, wasu kuma sun rungume mata 'yan'uwan su suna kissing ɗin juna, Wasu kuma suna gefe suna kallon masu rawa ana musu liƙi. Wani keɓantaccan ɗaki aka kai ta suka cire mata kyallen da suka rufe mata ido, da sauri ta bude idanuwanta tana kallon inda take, gane abin da ya faru da ita sai kawai ta fashe da kuka tana bin wanda suk kawo ta da kallo, su kuma suka juya suka bar ɗakin.. Tana nan zaune sai ga wata budurwa tashigo ɗakin tare da zama a kusan da ita, saurin matsawa Abin ta yi ta bin da kallo ganin yadda take mata wani kalar kallo. Dariya budurwar ta yi ta sake matsowa tare da dafa kafaɗarta cikin salo irin nasu na 'yan bariki ta soma faɗin "Welcome back my girl, bari ni na samu kasona kafin Oga ya samu isowa kar ya dauke ki ban samu abin da nake so ba." Ta faɗa tana jan Hijabin da ke jikin ta ta cire shi, saurin yin baya ta yi ta kuma biyo ta baki na rawa ta ce "K.. Ke me za ki yi min?"

Dariya kawai ta yi ta damki hannuwanta ta kama rigar ta ja da ƙarfi har sai da kan dinkin ya yake kaɗan, a zabure ta mike tana nuna ta da hannu rai a matuƙar ɓace ta ce "Wallahi kin yi kaɗan ki ga jikina, banza shashasha."

Itama mikewa ta yi cikin zafin nama ta nufe ta da nufin ta kama ta, ai kuwa ta kwasa a guje za ta fita a É—akin ta yi saurin tare kofar ta rufe, ganin haka sai ta koma can É—aya gefen tana haki tare da cewa "Ki fita ki ba ni waje kafin na illata ki."

Kallon ba ki da aikin yi ta mata tana nufo ta, ganin haka ya sa Abir ta tsaye tare da dakewa jin wani ƙarfin gwiwa ya zo mata, tana isowa ta nemi ta kama ta ita kuma ta goce suka kama kunce. Sun ɗauki lokaci a haka Allah ya ba ta rana ta ɗago ta yi saurin kai hannunta ta damki wuyan, nan da nan ta zazzaro maganai waje saboda ta mata ruko ba na wasa ba, sai da ta ga ta soma sakin jiki ta sake ta sai ga ta can ta zube a ƙasa tana haki, nuna ta ta yi da hannu ta ce "Ni za ki nuna wa ke cikakkiyar ƴar iska ce? To kin yi kuskur... Ba Ta ƙarasa yin maganar ba sakamakon jin an bude kofar, saurin juyowa ta yi suka yi ido hudu da shi cikin shigar shi da yaran Turai. Tsaki ta ja tana riƙe ƙugu ganin wanda ya sato ta a karo na biyu, wani kalar kallo da take masa wanda shi kansa har abin ya ba shi mamaki ya zauna a kujerar da ke gefen su, kwafa ta yi ta ce "Wai kai wani kalar jahili ne? Ka taɓa ganin an yi so dole? Ko ana aure kan aure ne?"

Murmushi ya yi yana kallon ta, ya gyara zama ya ce "My love ai duk wanda ya aure ki ya yi banza, yanzu haka ma da madaura aure na zo za a É—aura mana aure sannan mu yi party mu tare a gidanmu, ke kin san kalar son da nake miki kuwa?"

Banza ta mishi ta matsa ta É—auki hijabinta da sauri ta saka, za ta zauna ta ga wasu mutane sanye da manyan kaya su huÉ—u sun shigo É—akin sai washe baki suke, wajan zama ya nuna musu suka zauna ya nuna musu Abir tare da cewa. " Ita ce amaryar tawa. "

Washe baki suka yi kowa na fadin "Gaskya ranka ya daɗe ka yi dacen mata wannan zuƙeƙiyar balarabiyar."

Saurin katse su ya yi ta hanyar É—aga musu hannu, waya ya dauka ya kira sai ga mata biyu sun shigo ya nuna musu budurwar nan suka yi waje da ita. Zama suk yi mutum biyu suka ce sune iyayen Abir, biyu kuma na Big boy suka fiddo sadaki suka ba da su kuma suka masa, É—aga hannu suka yi a tare suka ce "An É—aura auren big boy da amaryarsa princess Abir mun sheda Aure ya É—auru."
Chapter 102 · 0% Book details