Sashe 99
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aliyyah tayi wani irin tsoro na kamata, ta kara rungume Yaranta tana me fatan Allah ya rabata da kaidin Ayrah kafin wannan lokacin. Amma ina bata samu sauki daga Ayrah ba domin rashin mutunci da rashin arziki take kafta mata. Yadda take kuka ya dagula lissafin Maina baki aya, ya riko hannunta yana leka fuskarta. "Kiyi hakuri kin ji!" D'ago kai tayi ta zuba mishi jajjayen idanunta kafin ta ce mishi. "Ban san yadda zan gaya maka ba." Harshensa ya saka yana lashe hwayen da yake zuba mata yana murmushi. "Waye ya gaya miki baki san abin da zaki gaya min ba. Maza gaya min." "Mutuwa xan yi!" Ta fada tana toshe bakinta, dariya ya saka tare da jan kumatunta. "Waye zai yi gadin duniya yan matana!" "Nima mutuwar zan yi tare da yar budurwata mu tafi tare abij mu!" Girgiza kai tayi domin ta lura yadda ya dauki lamarin da sauki ba kamar yadda take ji ba. "Mutuwa xan yi na gaya maka ba abin wasa a cikin maganata." "Tow na ji!" Daga haka ya mike zai fita ta riko hannunshi. "Tow me zan miki tunda mutuwa zaki yi?" "Kayi hakuri ban san maganata zata dame ka ba, kayi hakuri." "Ni ban san me yasa kike ba ni hakuri ba, an yi miki laifi kin buge da bada hakuri!" Gyada kai tayi tana me fa in." Kawai bana son idan bana tare da kai, kayi kewa ne shi yasa nake baka hakuri!" Jan kumatunta ya yi a karo na biyu ya ce mata. "Bar maganar nan, ban san halin da Malik da sauran dangin suke ciki. Waye ya rasu?" "Baban Uncle Ammar!" Rufe bakinshi yayi yana me zaro idanu. "Waye ya kashe shi Malik ne?" Girgiza kai tayi tana fa in. "Ya kare iyalinsa ne daga cikin mutuncin Hamidah suka kashe shi." "Wayyo Allah Ammar, Wayyo Allah taya zan gaya mishi Mahaifinsa ya rasu?" Kallonshi take kafin ta ce mishi. "Kayi shiru mu koma Baihak ya samu ya binne gawar domin an hana ayi mata sutura!" "Bafa inda xaki!!" "Tow akan me? Gaskiya xan bika!" "Tow Allah ya baki sa'a ai dama kin rena ni." Daga haka ya fita a dakin idanunta ya cika da kwalla, ita matsalarta da Maina son kai. Ya cika son kanshi dayawa. Lokacin da ya fita ya xauna suna masu kallonshi, "Salahudeen zamu tafi Baihak da Ammar ka zauna anan" ware idanu Salahudeen yayi kafin ya ce mishi. "Ba fa zaman da zan yi tafiyar nan tare za mu yi shi." Kallonshi Maina yake kafin ya gyara zaman shi. "Kada ka fara b'ata lokacinka matata da Yarana suna hannun Hamidah taya kake tunanin zan zauna anan taya?" Shiru Maina yayi kafin ya ce mishi. "Alright muje;" daga haka suka fara shirin tafiyar, har suka gama Layla bata yarda sun hadu ba, asalima kin fitowa tayi tana daki zaune kyam kamar wata mara gaskiya. D'aga labulen yayi ya zuba mata idanu, kafin ya gyara murya ya dan zauna kusa da ita. "Kiyi hakuri ki kula min da gidan kin ji." "Har yaushe zaka auka kafin ka dawo? Hamidah ba kai take hari ba, nice take hari ka je da ni ka ji!" Ta fada tana me kwantar da kanta a kafadarshi. "Zan dawo in sha Allah!" Girgiza kai tayi tana fa in. "Zata rike ka ne." Duk yadda Layla taso fahimtar da shi, amma yaki asalima ba wai ya kasa fahimta ba ne a'a rayuwar Malik yake tunawa dole ya kai musu auki. Gefe guda Aliyyah da Yaranshi. Haka ya barta a dame, sai da ya tabbatar Ummimi ta bata magani sannan suka bar garin. Sun dauki hanya wurin karfe daya na rana, basu shiga Baihak ba sai karfe biyu na dare. Kai tsaye masarautar suka nufa, tun kafin su shiga fadar ake gayawa jami'an tsaron gasu nan. A lokacin da suka isa gari cikin fadar an mamayesu don haka kai tsaye bangaren Queen Hamidah akan wuce da su. Wacce dama suna tare da Tirsila ce. Mikewa tayi tana fa in. "Barka da zuwa Sarkinmu maganin kukanmu!" Ta fada tana murmushi. "Ina Malik?" "Kai daga zuwa sai tambayar mutumin nan da ya gurbata kanshi da zunubi!!" Ya fada tana murmushi. "Wacce irin magana ce haka?" A fusace Salahudeen yayi tambayar. Dakatar da shi Maina yayi, "Kyale dan banza yayi min rashin mutunci. Yawwa yanxu ku huta gobe sai mu san abin yi!" "Godiya muke!" Inji Maina yana me juyawa suka bar bangaren. "Me yasa kika sauka akan shirinmu?" "Idan na ce zan yaki Maina, yana da goyan bayan yarinyar nan kuma shakkar lamarinta kuke. Amma idan na biyo ya baya dole zan yi kome a nutse na kawar da ita babu me zargina tunda ina da wukar da xan gama da ita." Takawa Tirsila tayi tana fa in. "Kamar ya? Taya?" "Ba zan fa a ba lokaci ne zai nuna kanshi! Sannan idan kun duba abin da ya faru, na saka an bar su Malik da kowa domin aikina yayi yadda nake so, zuwa yanzu barazana nayi musu, idan har na cigaba da rike su zasu saka zargin akwai abin da nake nima yanzu haka na saka Falwa ya goge min abin da ya faru a gidan Abu Ammar, sannan yan majalisar Malik zasu juyawa Malik baya. Yadda xan saka a bankado shirin da nayi akanshi. Ina son danshi da na raba tsawon shekaru ya dauki alhakin jinin mahaifinsa yadda daga baya zan juyawa Yaron baya. Ko Falwa?" Sai yanzu Tirsila ta yarda da cewa cin amana a jinin masarautar yake. A saninta duk abin da Malik yayi Queen Hamidah ta saka shi amma zuwa yanzu tana shirin juya masa baya. "tow idan ya ce ba shi ba ne ya kashe Abu Ammar fa?" "Ba ma zai samu damar bude bakinshi ba, zai amsa ne akan shi ya kashe Abu Ammar da yan mata arba'in da uku, yana tsafi da su. Daga nan babu me zargin Queen Hamidah!" Komawa kan kujerarta tayi tana murmushin mugunta da keta yadda ranta yake so. Zuwa yanzu aikin ya ya tafi yadda take so bata san kuma me zai biyo baya ba. A hankali suke takawa "Maina me yasa!" "Shiiii!" Ya fada yana me basu Umarnin har bangarenshi, ya samu Aliyyah da Yaranta suna cure wuri guda. "Papa!" Da gudu Nuri darling ta isa gabanshi. "Tsoro muke ji ka kai mu wurin Mami Layla!" "Babu abin da zai faru ba gani ba!" Kuka ta saka tana kara rike shi. "Ya isa!" "Ammar ku shiga wancan dakin amma na doke ku!" Ya ja bakin shi kamar ya ja zip. Abin ya basu mamaki, haka suka shiga dakin, Maina ya ja Aliyyah da Yara dakin suka kwanta yayi alola ya gabatar da sallah nafilla sannan ya jima yana addu'a, jin shashekar kuka yasa shi juyawa Aliyyah ce take kuka. "Me kuma ya faru?" Cikin shashekar kuka ta ce mishi. " kawai ka sake ni tunda bani da amfani a wurinka!" "Shine bukatar ki?" "Eh!" Ta fada a hasale, "Tow shi kenan!" Daga haka ya wuce dogon kujera ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. Washi gari da kanshi ya fita wajen masarautar ya hado abin karyawa ya zo ya girka aka ci ya kai har bangaren Malik, da bai da Lafiya tun lokacin da ya ji labarin Mutuwar Abu Ammar, ya ji kamar gefen zuciyarshi bata amfani kamar yadda ya dace. "Muhammad me ya dawo da kai?" "Halin da kake ciki, ya anyi suturar Abu Ammar!" "A'a je ka kira min shi!" "Tow Abba!" Ya juya ya fita, lokacin da ya isa ya samu Ammar zai tafi kiran Queen Hamidah. "Kai Ina zaka?" "Wai Hamidah take kirana!" "Muje kiran Abba!" Ba musu ya bi bayan Maina har wurin Malik sai da ya musu nasiha kafin ya gaya mishi rasuwar mahaifinsa. Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Hamidah tana kirana bari na ji me zata ce min!" "Ku je da Muhammad!" "Eh dama haka ne!" Dakyar ya mike yana ji kamar zai fadi. A hankali ya fashe da kuka, har jikinshi yana rawa kowa yasan yadda Ammar yaje kaunar Mahaifinsa. Rungume shi Maina yayi yana jin kwalla na cika mishi idanu. "Ya isa muje muji me zata ce!" Haka ya hadiye kukan suka isa bangaren Queen Hamidah, tana ganin Maina ta ce mishi. "Ko zaka bamu wuri ne?" Ba a tab'a mishi irin wannan tambayar ba. Ya juya tare da barin parlour. Dake lissafinta yana tafiya daidai ta gama zagaye kome kafin ya kullawa Malik sharri, shi dai Ammar bai ce kome ba sai hawaye da yake zuba mishi har ta gama ya fito daga cikin parlour. Maina yana son tambayar Ammar amma ya kasa sake ranshi ya tambaye shi sai da Ammar in ne ya gaya masa. Gyada kai yayi yana fa in. "Me ka fahimta a tsakaninsu biyun?" "Abin da zan fahimta shine wanda zan ji a bakin yan gidanmu!" Haka suka nufi bangarorin dabam. Kowa da abin da yake damunshi. Maina ya koma wurin iyalinsa yayinda Ammar ya nufi gidansu ya samu ana ta kokarin isa fada a nime izinin suturar Abu Ammar, haka ya tsaya kai da fata, kafin can Maina yazo suka yi koma aka dauko gawar aka sallace kafin aka kaita makwancinta, har da Malik yana rike da abokinsa tun na Yarinta, ana gama binne Abu Ammar sai ga hukumar bincike sun iso makabarta babu wani zance suka wuce da Malik. Abin ya d'aga hankalin Maina amma don kada haka ya zama point din da za ayi amfani da shi wurin cutar da Malik da shi sai ya share kamar bai dame shi ba, Ammar in ne ma yayi ta magana ya ajiye batun mutuwa ya nufi inda aka kai Malik. Sai dai kash duk inda ake tsammanin Malik yana wurin babu labarinsa. A wannan lokacin hankalin kowa ya tashi. An nime Malik sama da kasa babu labarinsa haka yasa hankalin ita kanta Queen Hamidah ya tashi domin bata san waye yasa aka kama Malik ba. Sannan duk yadda taso nazarin abun ya ci tura haka yasa ta shiga tashin hankali dole Malik ya amshi laifin da ba na shi ba. Idan babu Malik waye zai amshi kazamtar da tayi? Ajiyar zuciya ta sauke tana fa in. "Kowaye ya saka aka dauke Malik ba a kyauta min