Sashe 72
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abin mamaki ya bashi domin bai zaci haka daga gare ta ba. Kukanta ya dame shi don haka ya isa bakin kofar ya saka spare key ya bude dakin. Hangota yayi a can bakin gado tana ta shashekar kuka. "Me aka miki?" "Kawai ka tafi bana son ganinka!" Shiru yayi yana kallon yadda take kuka, "Na miki wani abu ne?" Bata kula shi ba, ganin ya zauna kusa da ita ta matsa can, ai kuwa take ya fahimci lallai akwai matsala. Don haka ya juya tare da barin dakin ya bata lokaci tayi kukanta. Har lokacin da tayi barci ya zo ya d'auketa zuwa dakinshi. Sannan bai kuma bukatar kome daga gare ta ba, haka yasa tayi barci sai bayan yayi Sallah da ya saba ya kwanta. Sai da barci me nauyi ya dauke shi. Hilda ta tawo kanta ta shige ya cikin kunnenta. Ai kuwa bude idanu Layla tayi tana mika tare da kallon Maina da yake barci, matsawa tayi wurinshi ta kwanta, a hankali tayi ta kunna mishi network, cikin barci ya fahimci ya fara daukar chaji, bai san lokacin da ya bude idanu ba, ya zuba mata idanu ta cire kayan jikinta ta watsar, yadda take mishi abubuwa yasan Layla dai ba zata yi ba, d'ago kanta yayi tare da kallonta a cikin duhu,ido biyu suka yi bai fahimci kome ba, sai da ya kunna hasken dakin ya ga gashin kanta ratsin shudi. "Me ya kawo ki?" Kallon shi tayi daidai tana kara rungumarshi. Janye ta yayi ya kura mata idanu. "Tambayarki nake?" "Wai kai meye matsalarka? Mace kake so gani nan!" "Ita nake so ba aljanu ba!" Ya fada tare da ture ta, sai da ta fa i mikewa tayi tare da bin bangon dakin tana tafiya kamar kaguwa ta nufe shi a guje. Cafke gashin kanta yayi ya shiga mata addu'a, sai da ya ga ta fara laushi ya ce mata. "dama kece kika hautsina mata lissafi? Fita kafin na baki mamaki." A hankali Layla tayi wani irin sanyi, kamar zata fadi ya rungumeta. Sannan ya nufi gadon da ita ya kwantar da ita. Kwana yayi zaune yana nazarin yadda zai magance matsalar Layla, da asuba ya kwanta.-A gaban Sultanah Dilshah Khatoon Prince Auta ya nutsu yana sosa kai, harara ta watsa mishi. "Bana ciki da munafunci, meke tafe da kai?" "Yarinyar nan Layla nake son ki tsaya a bani aurenta." "Ban gane ba?" Nan ya mata bayani, kallonshi tayi kafin ta ce mishi. "Ka hakura da ita, ka nimo wata matar kawai!" "Tow me yasa Hajja!" "Saboda kawai bana da ra'ayin ka aure ta!" "A'a hajja wannan ba hujja ba ce gaya min dalili! Ina sonta zan kare ta, kuma zan bata kariya har da rayuwata zan bata kariya!" "Ba xaka iya ba domin Layla ba rabonka ba ce ka nemo matarka!" "Hajja amma da Salahudeen ne ko Maina zaki tsaya musu amma.me yasa ba zaki tsaya min ba? Na girma da hantarar mutane saboda kawai Malik ya yanta Uwata da take baiwar Ummimi sai zunubinsu ya shafe ni? Me yasa ba za ayi min adalci na Maraya da bai da uwa ba?" "Ka rena rikon da Khamilah ta maka kenan?" Kamar zai yi kuka ya girgiza mata kai. "A'a Hajja amma kuma baki nuna min kauna kamar yadda kike nunawa sauran!" "Ni ban ki ka ba, amma Layla ka hakura da ita idan akwai wacce ta maka Ni mai tsaya maka ne!" "Ni bana son kowacce mace Layla nake so!" "Kace me? Tow ka sani Layla tayi maka nisa sannan idan ka nace kace Layla ce zaka yi wasa da rayuwarka ce don Allah Yarona ka hakura da ita!" "Tow akan.me?" Yq fada hawaye na zuba mishi. "Akan Layla matar Maina ce!" Rike kirjinshi yayi da yaji wani abu ya cake shi kamar zai huda zuciyarshi. Hawaye ne ya zuba mishi cikin karfin hali ya ce mata. "Hajja me yasa kika min haka? Me nayi miki da zafi haka? Hajja kafin Maina ya ganta na ce miki ina sonta, Hajja don Ni ba jikanki ba ne? Ko don ba Ummimi ba ce ta haife shi." Girgiza kai tayi tana fa in. "Wallahi ba haka ba ne, akan me zai saka na maka haka? Wallahi ban yi domin cutar maka ba, akan me zan maka haka don Allah kada ka kulla ce ni, ban yi haka don na cutar da kai ba!" Abin tausayi ita kuka Auta kuka haka yasa. ** Tunda ta iso Baihak take sintiri take don ganin Malik, amma yace kada a barta domin bai da lokacinta, kuma bai da lafiya. Haka yasa bakinciki ya kama Ayrah kamar tayi hauka, domin tana son lallai ta bawa Malik labarin matar Maina, don ta haka ne zata ha awa kowa hankali ganin Malik ya hana ta ganshi kawai sai ta nufi cikin gidan wurin Queen Hamidah. Yadda ta isa wurinta da Jawad tana kara tulawa Queen Hamidah kasa tare da nuna mata kaf duniya babu ita as Mother in-law. Murmushi Queen take, kafin ta kare mata kallo ta ce mata. "Meke tafe dake?" Gyara zama tayi cikin natsuwa ta ce mata. "Mother kin san Maina yayi aure?" A wani irin zabure Queen Hamidah ta mike....... Ayi hakuri Allah ya nufa mun dawo. Afwa.... [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu Da kuke bidar kari shin ba na baku labarin yadda nake lallaba wayata bane? Ko so kuke nayi abinda zai janyo min magana da ita A kyaleta mu lallaba juna yawwa* _______________42 Baki aya ta kasa nutsuwa, idanunta na kan Maina da yake ta fama da wani kallon Layla, sai dai lokacin da aka tashi taron ne Layla dasu Deenah suna tabin danginsu suna gaishe su, har Layla suka iso wurinsu Aliyyah. Cikin nutsewa ya gaida Aliyyah. Murmushin yake tayi mata tare da amsa mata tana fa in. "Allah ya sanya alkhairi!" "Didin Nuri darling, kin yi kyau!" "Na gode Princess Sainah!" "Didi kin yi kyau!" Inji Nuri darling, daukarta tayi suka cigaba da zaga mutane. Har aka fara watsewa sannan Maina ya ce su tafi, sam lissafinsa bai kawo bin sa Aliyyah zata yi ba, sai da suka dauki hanyar Apartment din Layla ya fahimci Aliyyah da Ayrah binsa suke bai so ba amma haka ya share koda suka iso gidan, sake baki da hanci Lady Ayrah tayi. Ita kuwa Layla tsamo-tsamo take nuna musu hanyar gidan, kin tsayawa Maina yayi ya bar apartment din, har cikin gidan. Ashe ya shirya mata yar karamar liyafa ne, sai da ta bude kofar suna shiga balloon ya fashe tare da sake wasu yan kyalikyali, an rubuta *Congratulations My ballerina!* Wani mugun sanyi jikin Aliyyah yayi tana ta kallon yarinyar da ta kasa nutsuwa. "Ke Uban waye ya kama miki gidan nan?" Kallon Ayrah tayi jikinta yana kara sanyi, ha iye yawu Layla tayi. "Don ubanki waye ya kama miki wannan gidan?" Idanunta ne ya cika da kwalla. "Tow ina ruwanki da wanda ya kama mata? Meye matsalarki da ita ne?" Wucewa cikin dakin Layla Ayrah tayi bata saurari abin da Aliyyah take fada ba, ta shiga binciken kayanta. Layla kamar tayi kuka. Duk ta kasa tsayawa a wuri guda. Shiga dakin Aliyyah tayi tana me fisgo Ayrah ta tsinka mata mari da yasa ta jijjiga. "Ke jahilar ina ce?" Janyo wani box da Ummimi ta bawa Layla tayi sai ga sarka me daraja a cikin ya fado duk suka zube. "Me ya kawo wannan hannunta? Ko har yanzu baki dauki haske ba ne? Mijinki ya ajiyeta tun bikin Bahiyyah na samu labarin uwar Mijinki ta bata ke me ta tab'a baki?" Sake dauke ta da Mari tayi tana fa in. "Ba zaki kara yin tasiri a kaina ba, idan ma turmi da tabarya na ga Maina da ita nasani ba zai tab'a wuce kaddaranshi ba ne ita wawuya wacce ta kasa zaune a nata dakin." Sannan ta fito da ita ta watsa waje. Zuciyar Aliyyah kamar zai buga, tana kallon Layla da ta sunkuyar da kai. "Sainah da Sanah ku kwana anan, har da Nuri." Sannan ta fita. "Na so na gaya miki!" "Na tambaye ki ne?" Daga haka suka bar gidan, Allah kadai ya kai Aliyyah gida amma tabbas akwai tashin hankali, tana shiga parlour ta ajiye Banafsha, ta zauna tare da aukar wayarta, kiran Jasy tayi bugu aya ta auka. "Princess Liyyah ya kike?" "Jasy!" Sai ta fashe da kuka, dakyar take mata bayani ta rasa yadda zata mata bayani, sai da tayi kukan ya ishe ta sannan ta gaya mata. Murmushi Jasy tayi tana fadin. "Baki tab'a burge ni irin na yau ba, da kika ki yarda da maganar Ayrah Yes Maina yayi aure kuma ban ga wani abin tashin hankali ba, domin ya sanarwar Ummina da Umminki, sannan Maina bai da niyyar cutar dake domin kece kika mika hannunshi da yin auren, kin tuna lokacin da kika hanata zama tare da iskancin da Sanah tayi mata? Tow lokacin kakarsa ta nata ikon a yanzu haka ko Malik bai san da Layla ba,baya tsoron Malik ko Baihak ya fi tsoron idan kika samu labarin ya zaki auka, Aliyyah kishi halal ne amma ki koyawa zuciyarki yadda zaki sarrafa kishinki shine matsalar, Maina yana son kasancewa da dukkanku matansa amma baya son hankalinki ya tashi, kina da damar zama da Layla gida daya ko akasin haka, amma masu iya magana sun ce kazamta da idanunka basu gani ba tsafta ce, sannan wasu sunce da nisa gara kusa ko ba kome wasu abubuwan zasu ragu, zabi ne gare ki." "Jasy yaushe kika soma cin amana?" "Ni ban ci amanarki ba, asalima kece kika bamu damar cin amanarki tun daga lokacin da Ayrah ta ingiza ki na dawo rakiyarki amma yau da kika nuna mata baki damu da alakar Maina da Layla ba, haka ya nuna mata ta rasa Maina har abada,ki sani ba sex ba ne rayuwar Maina yana bukatar kulawa idan Layla Yarinya ce ke ai ba yarinya b ce sai ki mike tsaye ki rike Mijinki koda akwai wani abu zai miki sauki!" Wani irin kuka Aliyyah ta sake tana jin zafi. "Kiyi kukanki wallahi, sannan ina kara baki hakuri yanxu ya dace ki gano darajarki a wurinsa!" "Me