Sashe 96
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wuta. Kanshi a kasa bai ce kome ba har suka gama a hankali yake tafiya Ammar da Salahudeen suna bin bayanshi. Jikinshi a sake zamewa yayi zai fadi Salahudeen ya riko shi, bibiyu yake ganinsu lumshe idanu yayi ya bude akan su, rike shi suka yi zuwa bangarenshi yana shiga yaga duhu ya mamaye mishi idanun, daga nan bai kuma sanin waye akanshi ba. "Layla" bude idanu tayi tana niman me kiranta. "Gani nan a jikin madubi." Kallon gefenta tayi tana me mikewa ta kalli matar. "Mijinki yana ta damuna, yanzu ya fadi bai san waye a kanshi ba." Da sauri ta isa jikin Madubin. "Tal kin ce ba zaki cutar da shi ba, me kika mishi?" Ta fada rude. "A'a zargi kanki dai ai ni gangan jikinki na dauki aron shi laifi ne haka?" "Amma!!" "Kin ganshi bani nayi sanadin cusa mishi damuwa ba, kece da ahalinsa da suka gaza mishi kamar yadda zuri'arki suka kasance wasu angarorin fa." "Tow me yasa? Me yasa ni na fasa?" Wani bakin hayaki ne ya daure jikinta baki aya me zafi da radadi. "Tal me kike bukata?" "Kiyi shiru ki girmama ni!" " ba zan tab'a girmama azzalumai ba, ki kyale min Maina babu ruwanshi!" "Ba xan kyale shi ba sai na makantar da Yar shi na kuma cusawa Matarshi bakincikin da bata san ranar rabuwa da shi ba Yaranta kuwa na saka musu bakin jini na har abada." Fashe da kuka Layla tayi tana fa in.."Na roke kada ki musu haka, na yarda ki dauki jikina ki rike jikin amma.kada ki musu haka babu ruwansu." Ta fada tana zubewa akan gwiwarta tana kuka. "Kika ce me?" "Na yafe fansar da xan dauka idan don nice na yafe musu, kada ki cutar da kowa na bar miki jikin na bar shi amma na hadaki da Ubangiji Maina kada ki cutar da shi!" Murmushi Tal tayi tana fa in. "Bar min jikinki yana nufin mutuwarki ce!" D'ago kai tayi tana kallon tal hawaye na zuba mata, "Na sani na san zan tafi na bar sh. Shi yasa bana son na cusa mishi damuwa kiyi hakuri kada ki cutar da shi." "Wacece irin so kike mishi?" "Nima ban san lokacin da na fara ba, amma nasan amsar ita ce mutuwa ta na fara kauna!" Daukewa Madubin yayi Tal ta tafi ta cigaba da kuka cikin dubu mara iyaka. Wasa gaske al'amarin yana wuce tunanin duk me tunani, a cikin kwana guda mutanen Fada sun kasa shawo kan Maina, yayinda ran Hamidah yake kara b'aci dole aka sallame ta, ta gayyaci Tirsila da Falwa. "Babu wata hanyar da za a rufe lamarin nan?" Girgixa kai Falwa yayi Tirsila ta ce mata. "Akwai hanya biyu!" Ya saka hannu a cikin jakarta wuka ce ta tsafi ta ajiye a gaban Queen Hamidah. Sai sarkan Rihanna. "Gasu nan wannan sarkan zamu sakawa gangan jikin Kalfana shi zai janyo Layla ta hadu da Kalfana wannan wukar a bawa Kalfana da shi zata kashe Layla amma ta wacce hanya haka zai faru?" Baki aya kansu yayi murfin kwano. " ya kamata a nimo mana wata hanya amma wannan hanyar tayi amfani amma taya Layla zata fito?" Inji Queen Hamidah. "Ba gani nan ba" tattara nutsuwarsu suka yi akan shi sannan ya gyara murya ya ce musu zamu fito da Rihanna ko nace Kalfana a jikinta tare da kwadaita mata girma da lafiyar jikin Layla idan yaso idan ta fita ta kashe Layla ta zauna a gangan jikinta haka zamu gaya mata ta samu sabon jikin da zata rayu!" Kallonshi Queen Hamidah tayi tana fa in. "Ka min bayani dalla-dalla!" Yadda ta nutsu yasa shi mata bayani amma wanda zai fito da Layla a wannan lokacin shine aiki. "Jininshi ya haura sosai,ya kamata a kwantar mishi da hankali, ba wai a ana d'aga mishi hankali ba." Kallon Salahudeen Ammar yayi kafin ya cewa likitan. "In sha Allah!" Ya mika musu takarda sannan ya ha a kayansa ya bar gidan, har lokacin Maina yana barci. Shigowa parlour Aliyyah tayi tana me kallonsu. "Abban Khalil meke damunshi ne?" Ta tambayi Salahudeen, shi kuwa ya ce mata. "Layla yake bukata!" Shiru tana kallon Ammar da ya gaya mata. Dariya yayi kafin ya gyara zaman shi da kyau. Hade rai yayi kamar bashi yayi dariya ba, ya ce mata. "Dake dabba ce ke mara hankali kika hada shi da abin da yake so, ga Maina nan ki kwadanta shi ki cinye. Layla ta bar raguwarku ga Mijinki nan ki saka shi farin ciki. Wallahi kika sake wani abu ya samu Maina sai na hukuntaki yadda zan boye ki har karshen rayuwarki ke" ya bude mata idanu. "Maina da Haisam suke da sauki kaf masarautar nan wallahi kika kara yin wani hauka akan Layla sa kai na yanke kanki na binne je ki tambayi tarihin masarautar nan wawuya jaka taya zaki zama sarauniya bayan baki iya figure something out ba" tas Ammar ya mata tijara ya kuma dakatar da ita zuwa ganin Maina. --- An samu tsawon sati guda da faruwar lamarin, abin kawai sai aka sake samun bulowar wani irin annoba. Wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, kai tsaye aka fassara haka da cewa Layla ce tayi haka domin kashe mutane. Kafin wani lokaci labarin ya fita har mutane sun fara zanga-zanga. Lallai a fito da Layla a kashe ta kamar yadda ake gudanarwa a cikin masarautar sai dai kowa yasan wannan ba abu me sauki bane don haka suka fara tilastawa Malik lallai yayi murabus. Shi kuwa yayi banza da su. Ga Maina da aka boye faruwar al'amarin a gare shi. A kwana na takwas aka wayi gari da tashin hankalin da yafi na ranar da ta cika na bakwai, domin kuwa kana hango mutum kafin ka isa gare shi ya fadi ya zama gawa. Karfi da yaji aka saka dokar hana fita ko ina, domin wata irinyar iska mara dadin shaka yake kad'awa. Kallon Salahudeen yayi wanda ya dawo da iyalansa gidan. "Babu hanyar da zaku bar ni na tafi na ganta?" "Wajen akwai hatsari ne!" "Yafi wanda nake ciki? Matata ce fa Please ku bar ni na mutu a hannunta." "Zata cutar da kai yanxu ta fara kashe kowa ma!" "A'a Laylatuna ba zata kashe kowa ba. Ku bar ni na tafi!" Duk yadda suka so hana shi amma yaki lallai zai tafi murmushi Ummimi tayi tana shafa kanshi ta ce. "Fada a kan so gaskiya ne imma ka mutu, amma kada ka rasa soyayyarka, imma ka rayu ka rasa soyayyarka abu daya zan gaya maka ka dawo da Matarka ta dawo ka gaya mata muna yadda nake kewarta. Jeka Allah ya maka albarka ya dawo da kai lafiya." "A'a Ummimi! Yana da rayuwa muna da Yara da shi akan Layla ba zan rasa uban Yarana ba......... ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500N ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [9/26, 8:27 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________65 Da mamaki suke kallonta, "kika ce kina da Yarana da ni? Me yasa kika saka yarmu a tsakaninmu? Me yasa?" Ya daka mata tsawa da sai da ta zauna dabas. "Da kina da hankali ba zaki muzantawa Layla ba, akan me? Tayi hakuri dake ta shanye duk abin da kike mata sai da kika shiga tsakanina da ita me yasa? Ita din rayuwata ce, na zata bukatatta na sauke himilin bukatatta akanta sai na fahimci ita din ko yayya take ina kaunar tarayyata. Ce miki aka yi jikinta da wani abu nake bukata da zan barta a yashe? Tow bari ki ji ba zan tab'a dawowa ba sai da ita." A hankali y juya yana me kallon Sanah da take zaro idanu. "Karfi da yaji kin lalata min tarbiyyar yarinyata, kin mai da ita sak ke Allah yana ganinki" daga haka ya juya ga Ummimi. "Koda ban dawo ba, labarin mutuwata ya iso ki, kada ki sake ta bar gidan nan koda abin cikinta ne ta haifa ta bar muku. Ita kuma wancan ki saka idanun akanta idan na dawo zan nime ko bawa ne acikin masarautar nan zan bashi ita ba zan bari tayi rayuwa like other princess ba, ta rasu kamar baiwa itama ta ji yadda kowa yake ji." "Wallahi ba xan yarda ba!" Inji Aliyyah, mika mishi bututun sha ar iska Auta yayi yana fa in. "Allah ya baka sa'a da nasara!" Daga haka ya fita yana murmushi. Haka ya fita babu kowa a masarautar Baihak, kamar anyi shara. A yadda yake tafiya ban da ya mika ragamar rayuwarshi ga Layla ba, tow kuwa babu abinda zai fidda shi daga cikin gida. Amma tafiya yake babu tsoro ko tashin hankali. Tun kafin ya isa kofar gidan, aka bude kofar shi wadannan duwatsu ne sun yi sahu sahu, bude mishi hanya suka yi, suna masu dukawa alamar suna gaishe shi. Lokacin da ita isa entry na gidan aka bude kofar ya shiga ya same ta zaune a kujeran parlour da aka kawata shi kamar wata sarauniya. Cire bututun yayi ya zuba mata idanun. "Wacce irin so kake mata? Bayan kasan baka da lafiya ka fito? Sannan haka bai maka ba, baka ga an sake iskar guba ba ne?" Jan center table din parlour yayi ya zuba mata idanu yana murmushi yana nuna mata bututun. "Na saka kariya!" "Baka tsoron na kashe ka ne?" "Tambayarki na farko da kika ce wacce irin soyayya nake mata, ita rayuwa ta ce, a kowani dakikar da agogo ya buga bugun da zuciyata take hade yake da nata. Ki bar mamakin nazo nan kiyi tunanin me zai kawo ni! Batun zaki kashe ni bai taso domin nasan ba zaki iya ba!" Ya fada yana sake matsawa kusa da ita, riko hannunta yayi. "Laifin me muka yi kike bukatar lallai sai mun mutu? Akwai kananan yara!" Murmushi tayi sannan ta ce mishi. "Bani na sakar da iskar guba ba, ni ma yanzu haka fita xan yi da tawaga na!" "Tow idan nake ba ce waye?" "Ka nimo su da kanka!" Ta fada tana murmushi. Hannunshi ya kai gefen fuskarta. "nayi kewar Layla ki fita!" "Itama tayi kewarka ba xan fita ba!" Ta fada tana murmushi. "Me kike so?" "Kwayar idanun Yarka Husainah!"