Sashe 9
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Duffur black humra* *sandal humra* *white humra* *body milk* *misik humra* *soulmateng humra* *creem kulecca* *basilin kulecca* *makhmariyya kulecca* *turaran wunana* *farce* *Hawi* *halud* *sandal oud* *oud flaxs* *Sandal flaxs* *oud kajiji* *Gabgab* *sandal coconut* *oud Al'arab* *sandal balls* *kindi kayi* *and more.....* *gamasu siyan daya ko sari kunemeni ta Wannan lambar* 09018535968 *muna maraba dakowa saikinzo* _________________ Fashewa da dariya, tayi har tana zama kasa saboda yadda ta ga ana wasan tsare da macijin, haba an raba su sun ki ji gashi daga zuwanta ta raba su. Zuba mata duka aka yi a baya ta daka tsalle tana zare idanu. "Saniya!" Shan mur tayi tana fa in. "Ke dai tur dake, kin zauna kina saka mutane magana, yaushe zaki yi hankali?" "Sai ranar da kika sayo min!" Kwafa Sanaya tayi ya wuce abinta, bin bayan Sanaya tayi tana fa in. "Kada ki manta ni fa albarkan Uwargijiya ce, irin wannan dukar mutum xao iya tab'ewa." Juyawa Sanaya tayi tana fa in. "Tabbas rayuwar nan ba a bakin kome yake, don haka kafin na tab'e sai na tabbatar bakya numfashi." Dariya Layla tayi tana fa in. "Duk da ban san lokacin da Uwargijiya ta bada rayuwarta ba, sai dai nayi miki alkawarin baki rayuwata." "Matsa ki bani wuri,ke da baki san muhimmancin rayuwar ba,taya zaki bawa wani rayuwarki? Yanzu idan naceki fita daga Wagaduwada zaki iya? Idan har da gaske zaki bani rayuwarki tow daga yau ki fita a Wagaduwada kada wani yasan inda kike!" "Sanaya babu wata alfarma ce? Barina Wagaduwada kamar barin ruhina cikin gangan jikina ne, Kaka Jami tana nan raye duk inda a shiga zata zakulo ni, sai dai idan zaki kashe ni babu kome na amince." "Kin rantse da wa?" Juyawa tayi tare da kallon majami'an tace mata."na rantse da majami'ance." "Mtsew!" Sanaya tayi tsaki domin ta lura mahaukaciya Layla ta maida ta. "Sanaya tun muna Yara ba fa haka muke ba, me yasa kika sauya?" "Au kin girma ne ashe?" "Eh tow,duk da ban zama me abu a kirji ba, na san dai yadda muke da!" Ta fa a tana kallon Sanaya. Ita kanta Sanaya tana jin babu dad'i. Amma sai ta dake ta ce mata. "Ki mutu haka zai gyara ala armu!" "Eh tow, idan na mutu yau kece zaki fara bi na. Ke ni fa mutuwata ba sauki domin ni gamayya ce idan zan fadi sai na tattaro abokan tafiya, yo da za a tambaye ni waye nake son ya raka ni idan xan mutu, kece zan nuna musu." "Mtsew mahaukaci!" Inji Sanaya, "sai dai mahaukata dai!" Layla ta fa a mata, cikin fushi Sanaya ta kaiwa Layla duka, ji tayi kamar an d'agata da kasa, an buga ta can saboda karfin surar da aka mata baki aya taji kamar ta mutu ne ko ta suma ne oho, cikin wani irin azaba ta d'ago kai da idanunta dishi-dishi tana kallon Layla da take tsaye babu abinda ya dame ta, sai dai ba Layla ta gani ba, wasu irin hayaki uku ne a saman kan Layla biyu farare ne, daya kuma bakinkirin ne, ja da baya tayi lokacin da Layla ta mika mata hannu. Ja da baya tayi domin bakar inuwar tayo kanta, tana iya hango kwayar idanunta light green, da sauri ta kwala ihu. "Tirsila!" Tana me rufe kanta. "Eh yau naga iskanci! Tow ba gani a kusa dake ba, miko min hannunki!" Layla ta fada mata. Jin dumin da yake kusantota ne yasa, ta mike tare da artawa a guje, tana ihu. "Shashasha ji yadda take gudu kamar zata bar Wagaduwada a kar." D'aga kafadarta tayi tare da nufar hanyar gida. Tana shiga ta samu ana ta fama da Sanaya, wacce ta firgice har ta fita hayacinta, kuma da tazo magana bakinta ya kasa budewa. "Au nan kika tawo? Tow sannu kin wani kama ihu kamar wata yar jaririya." "Me ya faru da Sanaya?" Kaka Jami ta tambayeta. Cikin ko in kula ta ce mata, d'aga hannu tayi zata dake ni, kawai naga anyi sama da ita an buga da kasa, yo tana wasa da wakiliyar Wagaduwada ce fa, ni fa ba a tab'a ni a kwana lafiya." Kura mata idanu Tirsila tayi na wani lokaci kafin ta ce mata. "Me kika mata ta suma haka?" Tura baki tayi gaba tana fa in. "Me zan mata kuma? Na gaya miki dukana zata yi shi ne aka yi sama da ita, na rantse da Wagaduwada ban mata kome ba." Yadda tayi rantsuwar har da dafe kanta, yasa suka gamsu bata mata kome ba. Amma ran Tirsila ya b'aci. "Zan kaita fadar rauhanan!" "Me kike nufi?" "Haeda!" Da sauri ta fito tana, me risinawa Kaka Jami ta ce mata. "Bari na kai Sanaya fadar rauhanan mu dawo ki kula da Wannan mara jin maganar." Tirsila ta auki Sanaya, Kaka Jami ta bude kofar shiga fadar rauhanan. Murmushi Kalya tayi tana fa in. " A duk lokacin da aka nufi Layla da sharri sama da haka zai faru, na gaya muku matukar inuwar Hilda yana raye ba zata bari a tab'a ta ba. Hmmm haihuwa da makiyi ba abin ka dauka ka bawa masoyi ba!" Shafa mata jar ruwa tayi ta bude idanu tare da kwala ihu, tana arin gudu. "Ai kin sha kada ki kara nufarta da sunan duka, koda wasa ita ba abar zalinta ba ne." Wannan kalmar ta Kalya ya b'ata ran Tirsila har sai da idanunta ya cika da kwalla. Domin bata jin zata yafewa Jamimah, yadda ta ha a Layla da abubuwan cigaba amma ta ki bata koda damar da itama zata bawa Jikarta. Shi ne ta bawa Yar tsintuwa wacce zuriarta suka guje su. Wannan ya kara kintsa zuciyar Tirsila yadda zata dauki fansa kamar ba gobe. Haka aka gama bawa Sanaya magani suka bar fadar. Washi gari. Duk yadda Tirsila taso sanin me ya faru, Sanaya ta manta. Sai take ganin kamar da gayya taki gaya mata."Baki da gobe, sam baki da wata nasara." "Ina da ita mana, kece baki nutsu a kan sanin inda gobe na yake ba." A zabure Tirsila ta yi kanta. "ina da gobe, idan kika ajiye yakin da kike rura shi, Layla ba abar ki b'ace ni nasan abin da na gani amma idan kika nace sai mun yake ta, zaki yi nasara kuma zaki fadi." "Kin san shirina kenan." "Shirinki kuskure ne da cin amana, kamar mutum ya juya ne ka dabb'a mishi wuka a baya,kada kiyi sanadin haka." "Ki yarda ni." "Ba zan yarda dake ba, amma ki sani ko yayya kika cutar da Layla zai zama wani abu da Wagaduwada ba zata yafe miki ba." Kallon yar shekaru goma sha ukun gabanta take, "kina min bincike kenan!" Tirsila ta fa " Ko aya." Daga haka suka yi shiru. --- Zaune take gaban ruwa tana hango yadda kifaye suke tsalle da linkaya. "Shugabana." Wani dan tatsitsin kifi yazo gabanta. Kura mishi idanu tayi, " me kake so?" Juyi yayi tare da ninkayaw ya dawo gabanta. "Naji dadi kamar yadda kika ji maganata " shiru tayi tana kallon shi amma kuma da bata da wannan baiwar taya aka yi yanzu take iya jin maganar dabobin. Ja da baya tayi ta ce . "Kai me kake nufi!" " "Ni sunana Qinmu, ki shigo na kai ki nahiyarmu." Da baya ta juya tare da kallon babu kowa ta ce mishi. "A'a Kaka Jami zata nime ni." "Ba zata nime ki ba, muje!" Dake bata jin magana, shiga ruwan zata taji an yi waje da ita, tare da kai takobi bakin ruwan, guguwa ce ta tashi me karfi, sai ga ruwan yayi rimi, can kuwa sai ga katon maradin tsohon rauhani me siffar kifi." "Barra ina ruwanka da yarinyar nan? Nazo tafiya da ita ne a bisa umarnin da aka bani." "Kasan ba zan barka ka tafi da wata bil adama ba, tunda babu abin da ta maka ke wuce muje " suka juya zasu tafi ai kuwa Qinmu ya taso da gudu,. A fusace mutumin ya juya tare da fa in. "Shimmo kaggara!" Take jan karfen.wuta ya nad'e aljanin kifi. Tsoro ya hanata kallon mutumin, tana gaba yana baya, wani irin sanyi taji a hankali ta juya babu shi babu labarinsa. Kamar bai tab'a wanzuwa ba, da ta kalkala da mugun gudu. Gida ta nufa, bata tsaya ba sai dakin Kaka Jami. Tare da niman mafaka. "Ke bana son hauka daga ina kike?" "Kaka boye ni yau naga Aljanin kifi, tare da wani wai barra!" Mikewa Kaka Jami tayi ta ce mata. "Ke waye ya gaya miki labarinsu." "Na rantse da Wagaduwada na ganshi wani me takobi, har ya fadi wasu kalamai ya daure aljanin kifi da karfen wuta. Shimmo kaggara!" Rufe mata baki Kaka Jami tayi. "Dole ta nisanta Layla da Wagaduwada domin kuwa abubuwa suka cigaba da faruwa daga ita har Layla ba zasu tsira ba. Taya aka yi Layla ta bude Qinmu? Bayan yana rufe? Tow ya aka yi Sadauki Barra ya bayyana a gare ta, bayan kowa tasan wa annan sun tafi a kan tafarkin kare al'ummar Wagaduwada. Hawaye ne ya zubo mata. Tabbas Tirsila tasan da wannan abin Layla zata shiga uku . A bangaren Tirsila tafiyar kwana uku tayi, duk da Sanaya bata so ta tafi ta barta ba, amma ta tafi,kuma bata gaya mata inda ta tafi ba. *Baihak* Hannunshi goye a bayanshi, sai Safa da Marwa yake, ya zuba Princess Khamilah "Ni ban isa ki gaya min Maina zai bar Baihak ba kenan?" Cikin karfin hali ta ce mishi. "Na ga kaima baka damu da sanin halin da yake ciki ba, kuma ya rigada ya yanke hukuncin ba zan mishi tilas ya zauna ba, don Allah kada ka mai da lamarin babban al'amari mana." Ta fa a kamar xata yi kuka. Shigowar Bahira tare da zubewa akan gwiwarta ta ce. "your Highness Concubine Ayrah tayi b'ari." Hannu ya d'aga mata tare da cewa. "You can go, Allah ya bata lafiya." Sannan ya juya ga Maman Maina. "Kika ce kada na maida abin babba?" "Amma dai idan da kana son Maina ba zaka raba shi da abin da yake so ba, saboda bukatarka na rayuwa gashi nan ita ba ga tsuntsu ba, ita ba ga tarko ba." "Khamilah kin zo nan ne ki min rashin kunya?"