← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 115

Sashe 76

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi haka yasa baki aya ya sussuce ya rasa inda yake mishi dadi, Aliyyah tasan Maina ciki da wajenshi amma wani abu da ta kasa kebance shi ga Maina soyayyar shi na daban ne a ranta haka kishinsa sai dai yadda yake girmama lamarinta da sha'aninta yasa take daukar shawara Jasy na dauke kai akan duk abin da zai yi, sannan kwarin gwiwa da ya bata na girmama lamarinta ba abin watsarwa ba ne. Haka suka kwana washi gari tana yadda yake rawan kai a ban aki domin har gyaran fuska yayi ya cire kome na fuskar shi sannan ya gyara kanshi sosai, fita tayi ta bar shi yana ta kyale kyale kamar wani mace, koda suka zo karyawa ya ji kamshin abincin har da tafarnuwa ka an ya ci yana fa in. "Bani tea kawai!" Hada mishi tea din tayi ya sha sannan ya tashi. A nutse taci abincin ta amma ranta babu dad'i, har ta gama yara suka gama suka kwashe kayan fa aka b'ata dakinta ta nufa, tana shiga taji ranta ya b'aci sosai. Jasy ta kira kamar zata yi kuka ta ce mata. "Tow ya xanyi?" Murmushi Jasy tayi tana fa in. "Sarauniyar Baihak guda, take fa in ya zata yi fa? Comon ki dauke kai duk da akwai ciwo amma ki daina kallon abin da yake yi, shi ba don ya b'ata miki yake yi ba, zuciyarki ce da shaidan yake tunziraki kada ki damu da yinsa sannan tsakani da Allah bai tozartaki ba taya zaki dauki hanyar tozarta kanki kowacce mace tasan when namiji yayi add second one dole yayi rawan kai akanta. Sannan idan duniya da gaskiya tashin hankali da b'acin rai ba naki ba ne, haka kawai sama da shekaru goma sha yana wuri aya ai kin mishi adalci ya matsa gefe guda, don Allah ki daina d'aga hankalinki. Maina daya ne sannan abin da kike damuwa akai daya ne meye na tashin hankali don Allah." "Jasy da ciwo fa!" Yes da ciwo mana, amma kiyi koyi da Ummu Hadiyya mana." "Wacece ita Jasy da kike yabonta haka?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. "Wata baiwar Allah ce muka hadu a saudiya lokacin aikin hajji wallahi." "Hmm shine kike misali da ita." Yar dariya Jasy tayi tana fa in. "Ke dai kiyi hakuri kiyi koyi da halinta babu abin da ba zai wuce ba a wannan rayuwar sai ikon Allah kada kiyi tunanin cewa Allah baya tare dake yana sane da lamarinki, sannan matu ar ba Maina ba ne ya wulakantaki don Allah kada ki damu ki ce zaki sha shi a damuwa, Aliyyah wallahi mata da yawa basu samu girmamawar da kika samu ba, Maina yana girmama ki koda ace bayan sonki ya mutunta darajarki, gaskiya Mijinki yana da matukar kirki kada ki lalata tarbiyyar da ya daura kanshi akai, ke da Mijinki baya dauko mata baya cin mutuncinki baya tozartaki baya miki kome, akwai matan da da zaran mijinsu ya hango wata mace basu da sukuni, saboda cin mutunci da cin zarafi kiyi hakuri kin ji My kawa akwai alkhairi a tare da layla." Duk inda zata shiga tana ganin darajar Jasy sannan babu wanda yake gaya mata gaskiya kamarta, "Jasy tow me zan yi?" "Jama'a Princess Aliyyah tana tambayata, ke mace ce kiyi tunanin abin da zaki yi." "Tow bari na hada kayan Nuri darling da take ta damun mu zata Layla!" "Kada ki damu Yaranki nata ne, tunda Maina ya haife su sannan ita fa kika ce ta taimaka da kakar Maina ta kawo abin da zai cutar da su, ke dole yarinyar nan ta kama zuciyar Crown Prince. " "Daga dan wannan abin!" Aliyyah ta fada a dan fusace, "Mai ne da wukar, Yan mata na gaya miki gaskiya kuma ta kama zuciyar shi wallahi kawai muyi ta addu'a Ubangiji ya hade kanku, kuyi ta d'aga mishi kafa yana zuba muku sandar girma!" "Amma dai ke yar iska ne!" "A'a yar guguwa dai, ina son na tuna miki ina gefenki, don Allah kada ki yi abin da zai bata mishi rai yana na da kirki da zan samu yar budurwa ce da bana bashi aurenta. "Jasy Allah yana ganin ki." "Bana son hassada!" "Sai kiyi Kuma!" Anan Aliyyah take kara gaya mata batun komawa Baihak, shiru Jasy tayi kafin ta ce mata. "Allah Sarki Ubangiji yasa ku tare lafiya, kuma da yace zai kyautatta miki kada wani abu ya saka kiyi abin da za su janyo miki reni kinji!" "In sha Allah, na gode sosai da samunki a gefe na!" "Kada ki damu kin ji!" Da wannan suka yi sallama. Ta mike ta hada kayan Nuri darling, sannan ta fita da shi har lokacin yana parlour Banafsha tana jikinshi tana wasa shi kuma yana waya, daga yadda yaran suka nutsu babu hayaniya ta nemi wuri ta zauna. "Tow amma dole sai mun hada kome na kafin mu tawo, tunda Ummimi ta ce mu dawo baki daya!" "Allah ya maka albarka komawa Baihak shine mafita, zamanka a wani wuri ba mafita ba ne, kada ka zama ragon maza me gudu kan yakinsa, Malik ya kira ni akan Layla kuma abin da muka tattauna akai ya ce ka koma ayi bikin sannan ka cigaba da aikinka da ka bari bayan nan zaka cigaba da kula da sha'anin Fada!" "Kawu ni bana son mulki don Allah kace mishi kada ya." "An riga da an baka Magajin garin Baihak, don Allah kada ka kawo wani abu mara dadi akai, kayi hakuri Allah ya maka albarka!" "Amin Ya Allah!" Daga haka suka yi sallama da shi, ya ajiye wayar. "Batun Baihak ne?" "Hmmm" ya fada yana mikewa. "Gashi nan kayanta ne a gaida Maminki!" A hankali ya bata one side hug tare da cewa. "Thanks!" "Mun gode!" Daga haka suka bar gidan, wata sai da ta zauna ta fahimci Layla ta kama wani gefe na zuciyar Maina, amma kuma gara da ta samu Jasy a gefen ta. * Kallon Ayrah Malik yake cikin fushi da takaici ya ce mata. "Allah kika sake na kara jin kin shiga harkokin Maina da iyalinsa sai na batar da iyayenki don na fahimci baki da hankali, ban dake jahila ce taya zaki raba hankalinki gida biyu kin manta Maina daga jikina ya fita ne? Wai me kike bukata ne?" Tura baki tai tana fadin "Da nasan haka xan samu wallahi da ban yarda na zo a kwarakwarah ka ba haka kawai ka raba ni da masoyina!" Murmushi yayi sannan ya ce mata "kwadayinki da na iyayenki ya janyo miki Maina jini na ne baki iska saka ni kishi da shi ba, amma zan nuna miki yadda zaki yi hankali domin daga yau Jawad zai koma wurin Uwar Maina wacce ta koyawa Maina hakuri da juri da sanin ya kamata su sakarya shashsasha." "Wallahi babu me raba ni da d'ana na rantse Allah, lallai ma na sha wahala a dauki d'ana a kaiwa wata banzan tsohuwa." Tass ya wanka mata mari yana nuna mata yatsa, "fita min daga turakata. Abin da Khamila tayi har abada uwarki ba zata yi ba, kai ko Uwar da ya haife ni ba zata yi hakurin da tayi ba zuwa yanzu Khamila tafi arfin cin mutuncin kowa in sha Allah!" "Malik Marina kayi?" "Ko zaki rama ne?" Ja da baya tayi tana zare idanu because Malik ba karamin giant Man ba ne zai iya kwallo da ita, kuma ko Ummimi da Lady Hidaya da sauran kwarakwarorinsa babu wacce ta tab'a mishi rashin kunyar Ayrah don Ubanta. Wannan renin hankalin yayi yawa, domin kuwa ya tsani had'a wuri. Da tada fitina. A cikin kwanakin ya saka aka tashi wani bangare na masarauta aka daura ginin da ko a tarihi ba a tab'a yinsa ba, domin Ammar da Salahudeen suka dauko masu aiki daga England, suka fara ginin. Duk da Ummimi wani bangare na zuciyarta yana gargadinta, amma ganin yadda hankalin Malik yake kan Maina kamar zuwa yanzu hankalinsa ya dawo jikinshi, kuma yadda take bata labarin Maina tana mamaki domin tasan bai tab'a zama ya ce mata waye Maina ba, haka yasa baki aya take jin damuwa da kuma jin kwarin gwiwa. Lokacin da Ayrah ta gunsawa Hamidah ginin da akewa Maina hauka ce bata yi ba, domin kuwa kasa zama tayi ta nufi bangaren Malik da wutar masifa yadda take shiga ba nan take fita ba, karshe tayi kasa da murya cikin rarrashi ta ce mishi. "Abin da kake yi kuskure ne, kasan Khamila da Maina zasu iya juyewa su koma niman rayuwarka....... Dam-dam. #Mai_Dambu [9/3, 9:16 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: *LAST EMPRESS* Mai_Dambu ________47 Bude idanu yayi tare da cewa. "Niman rayuwata?" "Yes rayuwarka zasu nima tunda kowa yasan baka yinsu yanzu kuma ka janyo su jikinka, sannan wannan barnan dukiya da kake yi bai dace ba, akwai Ibrahim da Haisam da kuma Salahudeen me kake nufi ga Jawad wannan adalci ne!" Kasa yayi da kanshi baya tunanin Maina zai cutar dashi ko da kuwa yana gargaran mutuwa ne yasan abinda Maina zai yi ya kuma san abin da ba zai yi ba, Maina baya cikin mutane masu zarmewa da son abin duniya kai baki aya Yaran Khamila basu da wannan zarmewan domin ita Khamila nagartacciyar mace ce da duniyarta bai rufe mata idanun ba, sannan idan akwai abin da yake hangowa dawowar Maina a gefenshi kamar kariya ce, amma kuma bai san me Uwarshi ta hango ba, "shi kenan Mama!" Ya fada da sanyin murya, murmushi Hamidah ta sake tana fa in. " a dakatar da ginin tunda yana da gidansa a Era estate!" Girgiza yayi yana fa in. "Kin san kowa yasan ina ginin nan domin Maina ne, idan aka gano na ajiye ginin mutuncina zai zube ki bari nayi kawai." Don kada ya ga zakewarta yasa ta ce mishi. "Shi kenan ai!" Sannan ta bar bangaren shi, abin ya dame shi me yasa take kin shi da Maina sai yanzu ta tuna da yadda take ta salwatar da cikin Matar Maina, amma a lokacin giyar mulki yana kwasarshi. Sunkuyar da kai yayi har Ummimi ta shigo da maganinsa da abinci domin zuwa yanzu ya hakura da cin abincin kowa gudun kada a cutar da shi, "Malik akwai matsala ne?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya labarta mata
Chapter 76 · 0% Book details