← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 115

Sashe 1

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data Normal Default Paragraph Font Normal Table No List [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu _Gargadi ban yarda a tab'a min wani angare na wannan labarin ba, duk wanda yayi haka zai fuskanci fushi da b'acin rai a kiyayye_ *28/5/2024* 7:39am ________________1 Garin Wagaduwada. Kasancewar gari ne da aka kewaye shi cikin alasuman tsafi, gari ne me cike da ni'ima da albarka ta ko ina, garin ba wani can babban gari ba ne, amma kuma sai ya kasance a gefe gefen garin akwai kananun auyuka da suke iya shigowa, kasancewar alasuman tsafin bai shafe su ba, bugu da kari babu wanda ya isa ta bar garin saboda tsoron kada ka rasa rayuwarka, sai dai a haka wasu masu taurin kai suna iya fita daga garin domin zuwa cirani da kuma fita niman abin duniya wanda idan har kana garin babu abin da zaka nima ka rasa. Masana da masu ilimin tarihi sun tabbatar da cewa, an katange al'ummar garin ne, a kala shakaru sama da dubu daya da darirrika, saboda rushewar andulus shakaru dubu daya da dari hudu da wani abu, sannan aka yi ta kame matsafa da suka shiga kasashen da masana ilimin kimiyya aka kashe su. Don kiristoci da suka kwace andulus sunyi imanin cewa matsafa da masana ilimin kimiyya zasu iya dawo musu da abubuwan da suka kora. Haka yasa ake kama kame duk wani matsafi da masu ilimin kimiyya da masu bada maganin gargajiya, abin da ya bawa al'ummar wada wasu nauyin kabilar libo ne sun kasance kamar Indiyawa ne da sirkin bakaken fata, sannan akwai daidaikun turawa a cikinsu, musamman wad'anda suka fito kananun auyuka, haka yasa a lokacin shugabar tawagar Wada ta jagoranci gudun hijira bayan tayi amfani da alkaluman tsafi. Suka zo wannan garin, a lokacin da suka dauko hanya. An kai labari har fadar Sarkin Andulus akan an samu wasu tawagar matsafa da masana ilimin kimiyya sun bai kasar. Cikin fushi ya bada umarnin a rubuta sakon ga kowani sarki na nahiyar har zuwa sauran nahiyoyin akan al'ummar shi sun yi gudun hijira kada su sake su barsu masauki, idan haka ta faru tow tabbas za ayi yakin kare dangi domin ta shirya manyan rundunoni na yaki, kamar yadda ya shafe Muslunci a kasar andulus da wasu wuraren tabbas haka zai shafe sauran nahiyoyin, sanin cewa tabbas haka zai iya faruwa yasa duk inda sako ya isa aka bazama nimansu. Haka ba karamin jefa wasu asashen cikin tashin hankali yayi ba, domin kowa yana tsoron rayuwarshi da fitinar da zata afko mishi musamman ta yaki. Haka yasa aka saka idanu akan masu shigowa kowani angare na kasashen duniya. Wada da al'ummarta, da suka yi gudun hijira kuwa. Sanin cewa za a iya nimansu yasa taki yarda ta nufi wata alkarya sai suka kasance suna bin dazuzzuka da sahara, a haka dai suka isa garin Wagadu gari ne da yake a tsakanin manyan duwatsu da suke can gabas da Baihak. A lokacin da suka iso abin da Wada ta fara shine kafa garin ta hanyar saka al'ummarta zama da maboya, sai dai kamar shuka tayi a makarwa domin akwai wasu daga cikin mutanen Baihak da suka kasance masu bibiyar lamarin sihiri da tsafi, don haka basu yi kasa a gwiwa ba. Suka shaidawa Sarkin na lokacin tare da bashi tabbacin idan aka samu alaka da ba in hauren zasu sami biyar bukata, Kingdom din zata zama mafi girman Kingdom a nahiyar baki aya. Haka yasa Sarkin lokacin ya kara kwadatuwa da al'amarin. Don haka suka tashi mutane aka je cikin sirri, aka tattauna da Wada. Wacce tsoron kada a koreta yasa ta amince da al awarin zasu bar musu wannan land in da suke, aka amince bayan nan sai da aka kwashe kimanin kwanaki ana abu kafin daga baya Wada ta fahimci ai ba haka abin yake ba. Wada tana da wasu yara da take rike da su. Yayinda da daya ta kasance mai baiwar hangen nesa da hango abin da zai faru, daya kuma tana da baiwar iya sarrafa tsari Wa annan Yaran sune mafi soyuwa a zukatar Wada, sai kuma aka samu akasin da za a fara aikin Masarautar Baihak yaran ta tura ba tare da tayi wani tunani ba, Yaran sun kasance Yan mata. Daga ranar da suka isa masarautar ba a kuma jin duriyarsu ba, sai kawo musu hari da aka yi, domin sun tabbatar da cewa matu ar Wada tana raye zata bibiye Yaran, Hanna da Rihanna. Anyi yaki na tsawon kwanaki ashirin, sai da ya zama an kashe rabi da wani abu na al'ummar kafin aka samu yakin ya tsaya, bayan Wada ta jagoranci katange garin da alasuman tsafin da tayi. Tana gama wannan aikin da ya dauke ta tsawon kwanaki ashirin a tsaye, haka ta musu a tsaye rike da kayan tsafinta da kome. Bayan mutuwarta yasa yakin yayi sanyi babu me shiga garin babu me fita garin idan ka fita aka san waye kai za a kashe ka. Domin an rigada an bada umarnin kisar. Zamani yana ta tafi an cigaba rikon garin ya kasance zuri'ar Wada sune suke rike da garin, wadanda suka kasance matsafa sosai sai dai zuriar sun kashi gida biyu, akwai matsafansu akwai mahangansu, wa anda basu da wata ala a da tsafi su Baiwarsu ce, sannan sun yi imanin za a haifi wacce take da jini biyu a tare da ita, sai dai har kimanin shekaru dubu daya da wani abu babu al'amar haka. BLACK MOON. _Ana mata lakabi da daren addara, wanda daren ya kan iya sauya addara mai kyau ko mara kyau, ga al'umma garin wagaduwada. Suna durkushe gaban Uwargijiya Wada, sai addu'a suke, kawunansu a sunkuye cikin tsannanin kad'uwa da tashin hankali, basu fasa Addu'ar ba har har sai da garin ya fara wani irin haske wanda yake fita daga cikin Majami'an, yana haskaka ilahirin garin baki aya "Dum suka ji saukar abu wanda ya haifar da d'ago kawunansu baki aya. Farar tsuntsuwa ce jikinta yana zuba da jini, sake tsumar bakinta tayi, a hankali wani farar takarda ya fad'o, tsuntsuwa ce ta shiga zagwayewa har ta murmushe a iska ya tafi da ita.. takawa daya daga cikin malaman Majami'an yayi ya isa gaban kushin tsumar. Jaririya ya gani ya auki takardan ya bu *Sako daga dan uwanku Zafir , ku rufe duk wani mahangar yarinyar ku tabbatar kun nisanta jinta da ganinta ga wata duniyar domin haka zai samar muku da salama! Nayi danasanin barinku amma ita addara mace ce da ciki ba a san me zata haifa gobe ba ku kula min da ita duk sunan da kuka saka mata nasan zai zama Alkhairi a gareta laifina da baiwata ya janyo na rasa zuri'ata na rokeku da abin bauta Wada a kada a bude mata jinta da ganinta* Dan uwanku Zafir... _Bayan shekaru goma sha hudu_ Tsoho ne tukuf yake tafiya a hankali, yadda yake tafiyar zaka dauka ya shekara dari a duniya, duk inda ya wuce sai ya bangaje mutane, babu wanda ya kula shi, kasancewar mutane ne masu matu ar girmama tsofin cikinsu. Sai da yayi tafiya me nisa kafin ya isa wani wurin da Yara suka taru, suna ganin shi suka saka ihu, "Layla!!!" Cire kayan tayi ta watsar tare da zuba musu dukkan lalitar da ta sane a jikin mutane, ihu suka yi suna fa in. "Uwargijiya Wada ta albarkace ki, Layla da me zamu saka miki?" Murmushi tayi wanda ya fito da lubar da dimple point dinta guda biyu ta ce. "A'a nayi muku ne ba sai kun saka min ba." Zuba kudadden suka yi baki daya, sulallar zinari ce da azurfa sai tagula. Kasawa suka fara ta ce musu. "Kai ku tsaya, waye babu abinci a gidansu?" Mikewa daya yayi ta ce mishi. "Ambi dauki wancan zinarin!" Kwasa yayi yana kallonta. "Na sallame ka!" Da gudu ya bar wurin, "Yu'isan dauki wancan kace min babanka bai da lafiya ko? Kwashe wancan!" Ta nuna mishi. "Tata dauki wannan kai kashewa zaka yi,sannan kana da kayan Abincin domin kakan tana da abinci, tow maza kowa ya watse." Uwargijiya Wada ta albarkace ki!" Duk suka watsa, murmushi tayi ta fito lungun tana gyara gashinta da ya sauka har gadon bayanta. Sai da ta tufke shi sannan ta dauki hanya kowa ya hangota zaka ga yana matsawa, ita kuwa sai dariya take cikin shakiyanci, idan ta ga abu dauka take babu wanda yake hanata. Tun daga nesa ranta ya bata wannan taron na mutanen ko sun kawowa Kaka Jami ziyara, ko kuma taron mutanen da tayiwa sane. "Ina ruwana wanda ya ce su ajiye dukiya jukunansu." Har ta isa kofar gidansu,bishiya ta fara hawa tana kallon yadda Kaka Jami take sauraron malamin majami'a, yadda ya karkace kai yana zuba mata sharri ga kanshi har wani sheki yake tsabar ya sha askin kwalkwabo. Cizon bakinta tayi tana fa in. "Har ni zaka ciwa amanata? Dole na sauko na tare ka domin sharri irin wannan yana kashe aure." Shiru tsohuwa Jamimah tayi tana jin abin da Malamin majami'a ya ke fa "Ranki shi da e, ya kamata ayiwa tufkar hanci, kafin Layla ta fa a tsinuwar Uwar gijiya." Gyara zama tsohuwa Jamimah tayi tana kara kallon Malamin majami'a da son jin karin bayani. "Wato Ranki shi da e, Layla ba karamin barna takewa Uwargijiya ba, ta'adinta yayi shuran da ba zan iya furtawa ba, saboda girmanki da kunyarki da al'umma suke ji." Lumshe idanun tayi ta bude akanshi kafin ganin har lokacin bata ce kome ba, ya kuma sake karkace baki ya ce mata. "Kin ga wadannan mutanen, sane yau Layla tayi musu domin ta kwashe musu yan kudaddensu." Ratsa cikin mutanen tayi, ganin kaka Jami yasa ta juyawa zata bar wurin ta saka sandar tsafinta ta janyota ta watsar da ita can. Mikewa tayi tana karkad'e jikinta. "Ranki shi da e hatta kayan k'awan Uwargijiya Layla ta kwashe su ko ina take kaiwa babu wanda ya sani!" Ware idanu tayi tare da kallon shi cikin subutar baki ta ce. "Lallai malamin majami'a ka cika babban munafiki! Ita uwar gijiyan ce ta gaya maka na sace mata kayan adonta? Kaka Jami, na rantse da Dutsen me tsarki na
Chapter 1 · 0% Book details