Sashe 23
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zata mutu don tana hango yadda za a rataye ta, amma tana son wannan fansar ya zama mafi kyau da armashi ga ahalinsu baki aya.. haka abubuwan suka cigaba da tabarbarwa, Niman Layla suke ba dare ba rana, sannan Falwa ya kara bincike babu yadda za ayi ya gano Layla don haka ya bar ashin asa ya samu Hamidah ya gaya mata abin da yake shirin faruwa idan kuma tana son kada wani abu ya faru a bazama niman Layla. Haka kuwa ta kira Malam ta gaya mishi, kamar ya tashi sama don farinciki. Don haka suka koma Wagaduwada ko Layla ta dawo, babu kowa a gidansu Layla. Majami'a suka nufa inda suka samu Malamin Majami'a yana koyarwa. "Kai Layla bata dawo ba ne?" Suka daka musu tsawa,"A'a bata dawo ba" "Idan kuka samu labarinta ku ce lallai tazo baihak Kakarta tana jiranta!" Gyada kai Malamin majami'a yayi, yana jin tausayin shu'umar yarinyar da tasa shi ha'ula'i. Suna tafiya daya daga cikin daliban ya ce. "Malamin majami'a, yanzu kariyar da muke da shi an rushe shi kenan?" "Babu ita, sai dai Uwargijiya tana gani zata kawo mana mafita!" "Malam Ravi zai iya samo Layla kuwa?" Shiru yayi na wani lokaci kafin ya ce musu. "Wannan lamarin Uwargijiya ce." Tun bayan faruwar al'amarin, Ravi ya tafi niman Layla,kuma yayi al awarin zai dawo da ita. Lamarin Haeda kuwa, ta fada wani gari ne da yake Kudancin Baihak, koda yake mutanen garin, rabinsu arna ne haka yasa bata wani sha wahalar samun tarb'a ba, sannan suma sun koka mata yadda al'ummarsu suke shan matukar wahala a hannun masarautar Baihak ba, tayi tur da Baihak sannan suka gaya mata babu abinda zata iya, domin baihak ta kama Jamimah. Kuma suna niman Layla ruwa ajalo, abin da zata yi ta nimo musu Layla suma. Domin yarinyar Goddess ce. Jinsu tayi kawai amma tasan duk inda Layla take, tana cikin tsaro da aminci, koda zata samu Layla zata d'auketa ne subar Baihak. *** Scotland. A jiya Ammar ya shigo garin, don haka tun safe Maina da kanshi yake ta hidima a kitchen, yana yi yana kallon Ammar da yake ta cin abincin shi a nutse duk da bai fito ya gaya masa ba, amma yasan magana ce ta kawo shi ne muhimmanci. Cire afro din yayi ya koma gefe ya wanke hannunshi, sannan ya jera abincin a ture ya dauka, ya nufi dakin Yaranshi da suke ta shirin makaranta. "Babys food is ready!" Ya ajyew musu. "Thank you Papa!" "Tanyu fafa!" Dariya suka saka suna kallon Nuriyya, sauka suka yi kowa ya zauna suka sakawa Nur nata sannan suka saka nasu, ya.juya ya bar dakin. Falon ya dawo ya had'a oolong tea yana sha yana kallon Ammar da har lokacin fuskar shi a daure take tam. Hayaniyarsu Sanah ya sasu kallonsu. "Ba zaku yi a hankali ba;" inji Mamarsu. "ok Mom" suka fito tana rike da hannun Nur. "Prince zan tafi asibitin!" "A dawo Lafiya!" Ya fa a yana kallon Ammar. Duk da ya kagu ya ji labarin abin da ya faru, amma kuma baya son zallmar ta fito kan fuskarshi. Ajiye mug din tea din yayi zai mike Ammar ya ce mishi. "Ina zaka?" Banza yayi mishi, shi zai gwada Shan kamshi? Ha iye b'acin rai yayi ya wuce ko amsa bai bashi ba, can sai gashi sanye da kayan office. "Bana son bura Uba, taya zaka tafi bayan nazo da damuwa ne?" "Sannu Malik!" Ya fa a yana saka safarshi. "Baihak tana cikin bala'i" ya fa a yana kallon Maina. "Allah ya kyauta!" "Ban gane ba;" d'ago fararen idanunshi yayi ya zuba masa kafin ta tab'e baki yana fa in. "Me zance sama da haka?" "Maina bala'in ya wuce tunanin ka." Kafada ya d'aga cikin ko in kula ya ce. "Oho muku!" "Dole kace oho mana, ka manta Baihak aka haife ka, aka rene ka tow bari na gaya maka wani abu Queen da Malik sun kai hari wani kauye niman wata yarinyar da aka ce zata rusa mulkin Baihak." *Ko ka kashe ni, ka kashe mu Malik zata zo kuma zata rusa ka* komawa yayi ya zauna yana kallon Ammar, "what do you expect me to do?" Girgiza Ammar yayi sannan ya ce mishi. "Mu koma Baihak!" "Ba zan iya komawa ba!" "Please! Kana da ahali a can kuma suna bu atarka!" " I know amma ni ina son nutsuwa a nan" "Malik da Uwarshi, sun kamo daya daga cikin mutanen garin kakar Yarinyar kuma nan da kwanaki kasheta zasu yi." "Kyale su, zunubinsu shine ajalinsu!" "Maina me yasa baka da emotions ne akan danginka." "Na zabi na zauna ni da Yarana, bana son rigima ka koma inda ka fito!" "Amma!" "Please idan ba akan kanka zaka bani labari ba, ajiye Baihak." Ya fa a yana nufar dakinshi ya cire kayan ya dawo falon, ya kunna tv ya daura daya akan aya. "Matar Salahudeen ta haihu wancan satin!" "Ya gaya min." "Bahiyyah tana nan kuwa?" "Eh tana school!" "Babu maganar aure ko?" "Eh har yanzu bata samu miji ba!" "Allah ya kawo!" "Amin Ya Allah!" Daga haka suka cigaba da kallon cinikin da ake tsakanin kungiyar kwallon kafa na England da sauran na kasashen nahiyar turai. "Hmmm dama akan ko kana bukatar mace ce a kawo." Banza yayi mishi ya cigaba da kallonshi. "Maina!" "A'a lim, kai zanci Ubanka, tashi ka bar min gidana?" Ya fa a a sanyayye. "Tab babu inda zanje dan uban mutum! Kuma ai wanzamin da ya mana kaciya bai yi karya ba, ya ce kai mace daya ko biyu zaka ri e su ne kawai amma mata hudu da Kwarkwarah biyar ya dace da kai!" Takaici yasa Maina ya bar mishi falon. Kwanan shi goma ya koma Baihak, duk da ba wani abu bane tsakaninsu fada ne,akan lallai Maina ya kara aure. Shi kuma baya jin a ranshi zai kara auren. Baihak. Tura mata abu suka yi gabanta, "kina cewa ba zamu iya ba, idan kin isa ki hana mu ga Layla din mun kamo!" Dariya ta saka tana tab'a kan yarinyar, "koda bani da idanun, kamshin Layla kamar na fure ce, sannan ba zan tab'a yarda ku same ta nan kusa ba, kun zata zaku iya wautar da ni ne? Wannan ba Layla ba ce! Kuna da sauran lokaci ku nimo Layla." Haka kuwa suka fita suna mamakin, yadda ta iya gano cewa ba ita ba ce don haka aka yi ta niman Layla, tsawon wata hudu, babu Layla babu labarinta, in fact ma har sun fara gajiya da niman da nimanta. A nan gidan tsoho Salis, sanye take da riga da wando sai rawani. Yau zata fara fita kasuwa ko nace waje, bata ta a fita koda bakin kofar gidan ba sai yau. Don haka ta saka riga da wando kamar yadda Sajida ta saka haka itama ta saka, sun yi masu burun-burun, sannan suka dauki kwandon kifin suka fito kowacce ta daura akanta, idanunta ne ya cika da kwalla, yau ita ce dauke da talla. Duk da ta bawa Tsoho Salis kudinta ya ce babu abinda zai yi dashi, ta ajiye zai mata amfani.. "layla sunanki daga yau Lala kuma kina sake muryanki kamar ta maza kada a tarfo ki!" "Hmm!" Abinda ta fa a kenan, suka fita a hankali suka isa bakin hanya bata tab'a ganin mashin ba, wato da yaji kar'ar shi watsar da kifin tayi tare da makale Sajida. "To ai kin zubda kifin!" Mujahid da Mujitafa suka kwashe da dariya suna nuna ta. "Babu abun da zai miki ai babur ce." Haka ta sake Sajida ta kwashe kifin suka nufi wurin yan kifi, suka baza a kwandon. Sai dai a wurin sayar da kifin akwai manyan masu kawo musu matsala, koda za a a sayi nasu Layla zasu dauke kwastomar, sai da na kowa ya kare sannan aka fara sayan nasu lokacin har ya fara niman lalacewa. Haka suka dawo babu cinikin kirki, Washi gari ma haka suka musu, kallonsu take a ranar na uku da Tsoho Salis zai tafi kamo kifin ta ce mishi. "Kaka zan bika!" "A'a zauna yanzun zan dawo!" "Muje dai!" Ta dauki komar kifin fita, tana shafa komar tana murmushi, suna isa suka hau jirgi sai can tsakiyar tekun, inda tsoho Salis ya watsa burgin, can ya fara ja ya ce mata. "Jikata mai damu bakin ga Murmushi tayi ta saka hannunta a cikin ruwan don.baya gani, ya bata baya take jirgin ya fara baya, har bakin ga a suka sauka, tare da jan komar sai ga shi sun kamo manya-manyan kifaye, har da ragon ruwa, sai da suka cika buhu biyu suka kawo gida dakyar. Suna zuwa suka samu kowa ya shirya, diban nata tayi tana fa "Yau kifin mu zai kare kafin rana tayi tsakiya!" Wato kafin sha biyu kenan, "idan dai su Deena da Salwa suna nan ba zai kare ba." "Na gaya miki kifin mu zai riga na kowa karewa!" Daga haka suka dauki kifin, suka fita. Suna isa kasuwar aka fara musu dariya don an san kwantai suke sayarwa kuma kifinsu kanana ne,. Haka yasa ake ta musu ba a, sai dai dariyar su ta tsaya ne lokacin da Layla ta sauke kwandonta. Kowa ya zuba mata idanu, "Yaku masu sayan kifi, yau nazo muku da ragon ruwa ba zan sayarwa kowa ba sai me dinari dubu aya" ai fa kamar wacce ta kirasu, sai gashi ganin an mata ca ta kada baki ta ce musu. "Na fasa dinari goma!" "Na saya a dinari dubu goma sha biyu!" "Ba zan sayar ba;" "Ashirin!" "Naki me saya shine da riba!" "Talatin da biyar!" "Ba zan sayar ba, kowa ya saya ya samu araha!" "Dinari dubu hamsin!" "Ko gezau!" "Dinari dubu dari!" "Halo dai naki!" "Dubu dari biyu!" "Ciniki ya fa a!" Aka kirga mata kudin ta sayar musu, bata san waye ba ita dai ta sayar ne, yana amsa suka ja mashin aguje abinsu, sannan ta sayar da na Sajida, ta kalli sauran abokai kasuwar. "Yau ko hmm?" Ta wuce tana musu murmushi Dama al awari tayi matukar nata ya kare, tow suma yau kwantai zasu tafi da shi. Suna isa gida suka nufi gidan Hajar, tana ganinsu ta fara murmushi. "Yau da farinciki a fuskar Laylatul khair!" Murmushi tayi tana