← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 115

Sashe 106

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tafi masallaci suka dawo sannan aka cigaba koda Malik ya zo da kanshi ya saka Maina a gaba suka tafi bangaren Ummimi suka karya nasiha yake mishi akan ya amshi kaddaran Layla " Idan Allah ya nufa Layla zata mike sai ka ga kamar ba ita take kwance nan ba, kayi hakuri duk tsanani yana tare da sauki!" Nasiha sosai yayi mishi sannan ya bar shi ya wuce bangaren Ayrah ya samu tana zaune wata ragwajab da ita. A hankali ya mika mata hannu ta kalle shi sannan ta kauda kai tana fa in. "Bar shi kawai!" Zama yayi ya ce mata. "Ina ga kina da yanci yanzu amma maganar gaskiya ba zan baki Jawad ba, ki tafi ko ina kike so ga wannan ki yi rayuwarki yadda kik e so, and idan ba ziyara ba tow bana bukatar ganinki a masarautar nan kin fahimta!" A hankali ya jingina bayanshi da kujeran parlour ya ciro wayarshi ya kira Salahudeen ya kawo mishi abin da ba shi ajiya. Can sai gashi da wasu akwatina har uku ya ajiye a gabanta. "Shi wannan kyauta ce na baki, akwai takardun filaye guda uku da estate guda biyu, da kamfanonin hudu da shaguna uku, ki duba duk da sunanki na bu e. Nayi haka ne da na kwantar miki da hankali, sannan bana bukatar wani magana ki dauki kayan nan ki tafi da su, Allah ya baki miji na gari kamar yadda iyayenki suke fata. Na roke ki da kada ki dawo masarautar nan sai dai ko ziyaran Jawad wanda a shekara sau daya nake bukatar ganinki. Shima idan lokacin yayi Salahudeen zai tuntube ki da haka, na gama dake Salahudeen dauki Jawad ka kaiwa Mahaifiyarka!" "Tow Abba!" "A'a kada ka raba ni!" "Shiiiiiii! Ki min shiru na miki yadda kike so, Jawad ba shine damuwarki ba, tunda kika iya hada kai kika zalunci wasu a matsayinki na Kwarkwarata tow zaki iya kashe wani ma, ki tafi bana son Magana kin ji ko!" Girgiza kai tayi tana wani irin kuka na danasani mara amfani ga dukiya amma bai da amfani, ciro wasu key guda uku yayi na mota ya ce . "Sun isa tun wancan satin aka kai miki jiya suka dawo da keys in." "Malik!" "Kiyi yadda nace Allah ya baki miji na gari!" Ayrah bata kawo rabuwa da Malik cikin sauki ba. Domin a tunaninta Malik zai kasance a rayuwarta sai gashi lokaci guda Malik ya juya mata baya, tayi kuka kamar ranta zai fita har zuwa yamma da ta je ta samu Anna, wacce ita ce Mahaifiyarshi amma Hamidah tai mata karfen kafa, zama tayi ta fashe da kuka. Murmushi Anna tayi tana wasa da Jawad da Ummimi ta turo mata shi. "Anna don Allah ki yafe min ki ce Malam ya mai dani koda ba zai bukaci kome a gare ni ba na amince." "Kiyi yadda ya ce idan da rabon zaku zauna Allah zai shiga lamarin, kada ki matsa Layla sai ya dawo da ke." Wani irin kuka ne ya kwace mata, gyada kai take kawai sannan ta wuce bangaren Ummimi tayi ta bata hakuri Ummimi ta ce mata. "Kada ki damu tunda ya ce ki je in sha Allah zai nime ki!" Ba haka ta so ba. Amma tabbas tayi rashi na har abada, A bangaren Aliyyah kuwa bata tab'a kawowa Laluran Sanah zai zama haka ba, yarinyar baki aya bata da lafiya bata zama bata san waye a kanta ba, kome yi mata take tayi kuka tayi danasanin takurawa Layla yau gashi tana ji tana gani haka yarta zata rayu domin duk wani mataki na taimakawa babu wanda basu yi amma kamar an shiga cusa babu lamari cigaba yanayin ma sai amari yake. Tayiwa Maina magana ya ce mata. "Ki cigaba nima mata magani, ga Layla a kwance nima ta ita nake " "Baban twins wani irin magana ne haka? Kana ganin halin da take ciki ka fadi haka? Matar da zaka iya sauyata zaka samo wata ita Yarka zaka iya sauya ta ne? Gaskiya ba zan yarda ba ka ajiye wata can ka tsaya mana yarinyar da kowa yasan mutuwa zata yi tunda sun yi imani da shirka ne." "Duk da ita kafira ce, amma ai tayi kokarin bada rayuwarta ne domin ki da ace bata yi wani abu ba tow ba makawa da labarin da ake yanzu zaman makokin ki ne, wallahi kada ki tinzura ni!" "Idan na tunziraka me zaka yi?" Tsaki yayi ya barta a wurin tana ta mita, haka yana ji yana gani Aliyyah tayi ta hada shi da mutane akan ya watsar da lamarinta da Yarta, ya rungume lamarin Layla. Duk da babu wanda yaji dadin abin da Aliyyah tayi amma don a kashe fitinar kowa ya bashi laifi kasa magana yayi, domin gani yake kamar da gayya suka bashi laifi ita kuma suka goya mata baya. Haka ya nufi bangarensu ya zauna tana ganinshi. Wani irin renin hankalin shine bai isa ya fita ba tayi ta kiranshi kenan a waya ina yake wasa wasa jinyar Layla sai da Aliyyah ta shiga tsakanin Maina da shi abin ya d'aga mishi hankali domin fakewa tai da Sanah da ita kanta, suka taso shi a gaba ya rasa inda zai saka rayuwarshi. Har tsawon kwanaki uku babu canji a kan Layla. Domin kuwa duk wani hanyar da za abu ta farfa o babu al'amari ya sa suka yanke shawarar mai da ita asibiti, abin tausayi a ranar da aka kaita a ranar likitar da ta amshe ta ta duba lafiyar cikin jikinta wani hukuncin Allah cikin lafiyarshi lau, abin da ya kara saka Ummimi kuka da tausaukn Layla shine yadda cikin ana scanning kamar jira yake fara harbawa domin cikin ya shiga wata hudu da sati uku, don ya taso sai da aka yi scanning din Maina ya fahimci ashe cikin yana girma duk da bata cikin hayacinta. "Yanzu Doctor me kike ganin za ayi akan cikin?" Murmushi tayi tana fa in. "kai haba ba kome Allah da ya bata shi zai raya shi mu namu tagazawa ne, za a cigaba da saka mata ruwan abinci me gina jiki tare da iskar da zai na taimaka Babyn." "Mun gode sosai Doctor!" Haka ya fito jiki a mace ya zauna a lokacin ya lura da yadda kowa yake kallonshi. "Lafiya?" "Aliyyah ta ce Sanah tana can tana suma baki aya ta d'agawa Ummimi hankali an je auko su da tare a Ummimi wai ta kiraka baka dauki wayar ba daga baya ta gane ja bar wayar a gida." "Ammar ina jin kamar zan mutu very soon, Ammar ina ga zan bada rayuwata ne matu ar Layla da abin cikinta zasu rayu. Zan tafi na gaji nayi kokari nayi adalci Aliyyah bata fahimta ba, idan bana raye ina ga zata fi gane abin nake domin samar da xaman lafiya nake. " shiru suka yi kafin Ammar ya ce mishi. "Ina ga zan nima musu takardan komawa asar iyayenta tayi jinyar Sanah din sauran Yaran su zauna a tare da Ummimi, batun gaskiya babu zancen sadaukarwa." Kimanin mako biyu kenan Kayla tana durkushe ba ci ba sha don ko an kawo mata abincin bata amsa, Mahaifinta da kanshi ya kawo abincin amma taki ta kula, hakan yasa shi fara jin lallai akwai wani abu da yake ranta don haka wayewar gari da ta cika kwanaki sha shida ya tawo har inda take ya ce mata. "Me yasa kika bukaci jefa raywarmu cikin hatsari?" "Saboda mu jinsin Junnu muna da al awari su ma jinsin bil adam suna da kaso masu amana da al awari amma na zabi haka ne domin yarinyar bata da kowa sai Allah." Sai kuma ta rufe bakinta da hannu. "Kin fara sha'awar musulunci ne? Na san dake muka yaki rundunar muslmai shekaru dari da hamsin baya yau kece me kiran Allah mutanen gabar?" Kallonshi tayi bata da mafita sai ta ce mishi. "Nayi Imani da babu abin bautawa da gaskiya sai Allah bauta da shirya tsafi da bokanci duk shirka ne da sabawa Allah, amma nasan tunda jininta ya tab'a sundukin nan ba zata kai labari ba." "Kai dakaru ki tafi da ita ku gana mata azaba nan da wata daya zan saurare ta." Haka suka ja Kalya duk yadda taso ta mishi bayani idanunshi ya rufe, duk da son da yake mata haka bai hana shi ya hukuntatta ba. Tunda aka kawo Sanah babu wani cigaba domin ciwon bai da alaka da asibiti amma Aliyyah gani take kamar bakinciki ake musu kudin da ake kashewa Layla ai bata ajiyewa Maina kome ba da za a zauna ana kashe mata ku i haka, da dare tana zaune a dakin ta cika fam ta batse Ayrah ta shigo dakin duk fuskarta nan ta kod'e saboda tashin hankali da rabuwa da Malik da danta sai yanzu take jin a ranta ashe tana son Malik kawai rashin hankali ne yasa bata gane haka ba. "Me ya kawo ki?" ",Nazo na gaya miki ne kiyi a hankali da rayuwa, domin Mazan Baihak basu sauka akan kalamansu, matu ar kika sake Maina ta kawo miki kyauta da har ki mutu babu wanda zai iya baki tun lokacin ki fara kuka, domin nayi matukar nadamar abin da nayi ta aikatawa basu kula iskancin mace amma daga ranar da suka ce a baki kyautar alfarma daga ranar sun rabu dake kenan har da Yaranki kun rabu idan Maina yana da adalci ne zai ce kina zuwa ganin Yaranki duk shekara!" Ya goge hawayen da ya zubo mata. "malik ya mallaka min abubuwa dayawa amma ya raba ni da abu me daraja ya raba ni da Jawad." Ta fada tana dukar kirjinta, "nayi imanin cewa a koda yaushe sarakuna suna iya tara mata dubu amma mace daya da suke kauna, idan kika ga haka mafi alkhairi ki kwantar da hankalinki, Malik ya tara mata dayawa amma macen da yafi kauna Ummimi ce. Har yau bata tab'a hauka da sunan kishi ba. She know her place!" Ta fada tana kuka kafin ta mike tana fa in. "Kiyi hakuri mu koma friend kamar baya, na yarda da ke ga Jawad ki saka min idanun akanshi, don Allah kada kiyi abin da zai saka Jawad ya rasa ki kamar yadda yarasa ni don
Chapter 106 · 0% Book details