← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 115

Sashe 77

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yadda suka yi da Hamidah dariya tayi tana fa in. "Akan me xan kashe ka? Bayan ba ni na halicce kaba, ka fahimci wani abu mulki baya tsarin Muhammad shi harkan gabanshi ya ishe shi Malam!" Kallonta yake da mamaki. "Kamar ya baya da ra'ayi akan sarauta ne?" "Eh Maina bai tab'a sha'awar mulki ba, hatta Salahudeen bayi da ra'ayi akan mulki me ra'ayin kenan Auta kai ko Ibrahim bai da sha'awa akan mulki sunan ka haifi yara ne amma baka san halin su." "Tow me Ibrahim yake so?" Murmushi tayi tana bashi magani. "Ka gano da kanka!" "Ban gane ba?" Ya fada yana tsareta da idanun. "Eh Ibrahim bai da ra'ayin mulki tu n yana yaro, mahaifiyar shi take son haka, Ibrahim bai da zimmar zama a cikin gidan shi yafi Maina kin gidan ma, yana zaune ne saboda Mahaifiyarsa. Ka bashi damar zama cikin mutane gamagari da basu da sukuni sosai." Tsaki yayi ya ce mata. "Taya xan bashi damar zama cikin talakawa? Jinin sarauta ke yawo a jikinshi." "Ai shi kenan!" Ta fada, tabbas Ibrahim bai da ra'ayin gidan yana zaune ne saboda, amma babu yadda ya iya yafi ganewa ya shiga cikin gari wurin talakawa yayi ta hidima dasu idan ya ga kyawawan Mata yayi ta binsu yana cewa ya samu mace. Sam Malik bai yi na'am da shi ba ta share zancen, bayan ta gama a hanyar ta na komawa bangarenta ta hango Lady Hidaya da Ibrahim, "Ummimi ya mai jiki?" "Alhamdulillahi kai ake jira a nad'a rikon kwarya kafin Malik ya warware!" Wani tsalle yayi ya koma can gefe yana fa in. " Da wani yayi wannan maganar da yau sai dai gyatumas ta haifi wani b dai shi ba, Allah ya min tsari da mulkin Baihak wanda naji ana bautar aljanu ko gaba ake da aljanu bayan nasan ba mutunci ne da ni ba, naje na taka diyoyin aljanu su shanye min kafafuna waye ya sani ko garin takama irin na Malik da wancan mayyar tsohuwar suka taka kan Dan aljanu aka sumar da shi." Murmushi Ummimi tayi tana fa in. "Allah ya shirya min kai sufi!" Haka take kiran shi duk lokacin Da ya bata dariya. Uwarshi kuwa ta cika ta batse dama akan batun ginin Maina ta sako shi gaba ya gayawa Malik zai yi aure shima a yanka mishi filin a fara mishi gini, koda suka shiga wurin Malik sun same shi ya nutsu yana shan tea , sai da ya gama cikin siyasa da kwantar da kai Lady Hidaya ta gabatar da abin ya kawo ta. Kallon Ibrahim yayi kafin ya ce mishi. "kai yanzu ka nutsu da zaka yi aure?" A hankali ya dubi Malik ya ce mishi. "Shi Maina da ya ajiye mata biyu, fina yayi da nutsuwa ne?" Shiru Malik yayi yasan kaf Yaranshi babu dan takife irin Ibrahim, "da sauran ka kenan?" Kumbura baki yayi yana huci kamar kububuwa. "Ke danki bai nutsu ba!" "Kuma wallahi sai na yiwa yan mata uku cikin shege yadda zaka aurar da ni!" Dariya ce ta kwacewa Malik domin ya bashi matukar dariya. "Idan kayi musu ma.ba xan aurar da kai ba sai kayi hankali?" A fusace ya mike zai fita uwar ta rike shi. "dawo ka zauna!" Cikin wani hali da basu saba gani daga Malik ba ya ce mishi. "halo dai baka girma ba, domin namiji me hankali baya abun da kake yi." Jikin Brahma ne ya dauki rawa cikin takaici yake cizon pink lips dinsa. "Idan baki da abin fada zaku iya tafiya, kai da aure sai dai ku ga ana yi domin baka nutsu ba;" "ai shima Maina ba nutsuwa ce da shi ba, kiri-kiri kana fifuta Yaran Khamila da sauran Yaranka." "Idan ban fifuta Yaran Khamila ba me xan yi? Ke ba zaki iya hakurin da tayi ba." Ai kuwa kasa motsi tayi domin bata kawo Malik zai fadi wani abu akan Ummimi ba, sai da tayi magana ya ce mata..'Babu ruwan ki da ita amma idan kuma kina son magana Bismillah zaki ji sai ya ishe ki!" Sanin cewa Malik zai iya mata babu dad'i da kalamansa yasa ta kamo danta suka fita, da idanun ya bisu baki aya sun hana shi sakat kamar ya bar garin yake ji, amma haka ya daure idan ya tafi ma zai dawo domin Maina, yadda yake jin Maina na ne daban ne. Don haka bayan fitarsu ya kira masu tsaron kofar yace kada a kuma barin wasu su shigo matu ar ba Abu Ammar ba ne, don haka ya kira Abu Ammar. A daren suka zauna suna tattaunawa. Kallon Malik Abu Ammar yayi ya ce mishi. "Kamar nayi kuka da kace kana son Maina ya dawo kusa da kai, haka yana nufin ka dawo kan koyarwa Annabi Muhammad SAW,, yanzu me kake so?" "Zan cire hannuna akan kome da ya shafi Maina zan na tura maka duk abin da ake bukata, kai da Yaranka kuyi kome. Ina tsoron kada laifin da na aikata wanda bai ji ba bai gani ba ya biya, ina na tsoron kada sanadin cusa kaina ga Maina ya samu matsala domin zuwa yanzu kamar akwai wasu abubuwa da yake arin shiga tsakanina da shi abin da za ayi aikin ya koma hannunka kuyi duk abin ku ke ganin ya dace." Ajiyar zuciya Abu Ammar yayi yana fa in. "In sha Allah zan yi yadda kace!" Lumshe idanu Malik yayi yana fa in. "Na riga da nayi kuskure shi yake bibiyata don Allah kai da Galadima ku tsaya a gefen Maina, sannan ga wannan takardan kada ku warware su sai ranar da wani abu ya fito ku warware shi ga al'umma su sani." Kallon Malik yayi a rikice ya ce mishi. "Kada ka bani tsoro mana. Wallahi ka saka zuciyata yankewa." Murmushi Malik yayi ya ce mishi. "Ka tafi kada dare yayi maka!" Duk yadda Abu Ammar yaso Malik yayi magana yaki magana asalima shiru yayi yana kallon wani wurin na daban. Haka Abu Ammar ya fita ya barshi a wurin. Midnight kowa na barci amma banda Queen Hamidah da ta nufi cave, tana shiga ta zube a gaban Falwa. "Falwa gaya min abin da zai faru Malik ya warware daga kome a da can sai yayi shawara da ni,. yanzu kuwa kome kai tsaye yake yi wai meke shirin faruwa?" "Gorunfa!" Fitowa dodon yayi yana nishi, kafin ya kad'a kanshi yayi tare da cewa. "Zuwa yanzu ya dace ki fahimci, Maina zai dawo kamar yadda kika ce yazo ayi bikinsu," sake buga bindinshi yayi da kasa yana kallon wutar tsafi da take ci." "Me kake nufi?" "Hamidah ta gayyato karshen ta ne!" "Kamar ya?" Inji Queen Hamidah, "Ku nimo kabarin Rihanna ko kuma Maina yana shigowa kome yazo karshe domin kuwa karshenki nake hangowa mara kyau da muni." A matu ar bu ace da son sanin meke shirin faruwa da ita. "Kai karya ne!" Inji Falwa, juyawa yayi yana fa in. "Ku nimo kabarin Rihanna shine xai dakatar da haka." "Tow a ina zamu iya gano kabarin Rihanna!" "Ku je gidan tarihin Baihak anan tsohuwar kurkuku yake anan suka kashe ta." "Gorunfana ka taimaka kada wani abu ya faru!" "Babu abin da zai faru matu ar kika samu kabarin." A hankali ta sauke ajiyar zuciya, kafin ta juya ta fita tana jin kamar matsalarta ya kare domin kuwa, sai dai kuma da sauri ta dawo tana fa in. "Ya xan yi da Malik?" "Babu abinda zamu iya domin Maina ya karya duk abin da yake jikinshi!" Kamar tayi kuka ta ce . "Amma anyi dan iskan Yaro yanzu ya zan yi kenan?" "Akwai mafita.......... #Mai_Dambu [9/4, 9:16 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ________48 "Kamar yadda ya b'ata min sai na rama, ku san tanadin da zamu yi mishi kafin yazo!" Daga haka ta bar cave din, washi gari da karfe biyu Tirsila ta iso wurin Queen Hamidah, "Barkanki da hutawa." "Yawwa Tirsila! Me ke tafe dake?" Gyara zama Tirsila tayi tana me kallon Queen Hamidah. "Dama akan batun Sanaya da Maina ne, ban ji kin ce kome ba." Murmushi tayi tana fa in. "Kada ki damu ina kan bakata sannan kuma ki kara bincike akan matar da ya aura domin zai dawo ayi bikinsu.", da sauri Tirsila ta d'ago kanta tana fa in. "Kika ce me? Aure yayi a can?" Ranta yayi mugun sosawa domin ita Tirsila tana shirin kafin Sanaya ta shiga zata kashe matar Maina na cikin gida, sai ga wani mugun labari wai yayi aure kamar zata yi kuka ta ce mata. "Gaskiya labarin nan bai min dadi ba, da nasan da Labarin nan da na rufawa kaina asiri." "Kada ki karaya mana nace ki nimo mana wacece ita domin Falwa da Gorunfa sun kasa samo wacce ita, don haka maza ki binciko mana wacece ya aura." "Shi kenan ranki shi dade an gama duk abin da kika ce!" Daga haka tayi mata sallama, sai dai koda ta koma gida kasa zama tayi duk Sanaya tana kallonta, "Kaka me ya faru ne?" Kamar zata yi kuka ta ce mata. " Yau nake jin wai Maina yayi aure, ni da nake shirin kashe matarshi ashe ya min shigar sauri." Ware idanu Sanaya tayi tana fa in. "Kawai sai ki kashe mishi mata saboda ra'ayin kanki habawa ba akyauta ba gara da yayi auren baki kai da cutar da shi ba!" "Kina nufin gara da haka ya faru kenan?" "Yes da ace kin samu nasarar kashe ta kin mishi asarar da ba zai manta ba, sannan aka zo aka gano ki ba kyale ki zasu ba, domin Mutanen nan babu amana a ransu!" "Mtsee fita ki bani wuri!" Kyale ta Sanaya tayi tana me wucewa dakinta, ta rufe ko kofar. Madubin dakinta ta shafa tana kallon Layla da take rike da Nuri darling, ga Maina a bayanta ya zuba hannunshi baki aya kan cikinta, sannan ya zuro wuyarshi kafadarta. "Please Layla kada ki hukunta shi da laifin da bashi yayi ba, bai cancanci fuska biyu ba!" A fada tana tawayen tausayin kansu. D'ago kai Layla tayi tana murmushi zaka dauka Sanaya take kallo, shafe madubin tayi tana me fashe da kuka, Yes Layla ba zata tab'a barin kowa ba. Sai ta rama sai ta auki fansarta. A hankali Malik
Chapter 77 · 0% Book details