← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 115

Sashe 56

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saka mata abin hannun da Layla tace a saka mata, sai yake ganin kamar rikicin da sauki, amma kwana biyu nan idan ta tuna Layla tayi ta kiran Didina kenan, gyara mata kwanciyarta yayi ya fita ya barsu. Dakinshi ya nufa ya samu Aliyyah tana barci, ajiyar zuciya ya sauke ya nufi ban daki yayi Alola sannan ya fito ya gabatar da sallah daren da ya saba, kallon Aliyyah yayi tunda suka dawo take rigimar zata dawo da Sanah, bai ki ba amma yarinyar ne tarbiyyar da Aliyyah take daurata yana tsoron kada a samu matsala. Yaso ya turata Baihak amma yasan wa Hamidah ya turawa, domin tafi Aliyyah illa gara ya ganta a gabanshi. Har asuba ya tashe tayi sallah ya tashi Sainah ma sannan ya nufi waje wannan karon gidan da aka bashi da ma'aikata sosai, akwai drive akwai me girki wata yar kasar Jamus, sai kula da gidan domin kawai jin dadinsa da walwala. Tun hudu ya e jin motsin masu girki da aikace-aikacen gidan, wanka yayi ya fito yana tsane kanshi ya kalli Banafsha da take barci yarinyar kamar bata yi jinya ba, kusan shekara take nima. Kallonshi Aliyyah tayi tana me isa gabanshi ta amshi towel din da yake hannunshi tana taya shi goge jikinshi. "My hot chocolate, yau nq ganka kamar ba kai ba" dan karamin murmushi yayi yana kallon kanshi a madubi. Gama goge jiki tayi tana me lakatar mai zata shafa mishi yayi.maza ya amsa yana fa in "yau na hutar dake!" Daga haka ya cigaba da shafa mai, komawa tayi saman gadon ta zauna tana me tagumi. Juyawa yayi ta dauke kai, yasan matsalarta amma shi yanzu ba wannan ne matsalar shi ba, yarinyar da ya kai makaranta ya ajiye bai kuma bin bayanta ba, "Kiyiwa Jasy magana a turo Sanah!" Gyara zama tayi tana fa in. "Ai na gayawa musu tare zamu zo!" Juyawa yayi yana kallonta. "Ni ba zan samu zuwa ba!" "Shi kenan tayi ta zama kawai!" Juyawa yayi yana kallon yadda ta dauke kai. Yasan abinda take bukata, kallon agogon dakin yayi, kuma laifinshi ne da ya kwana dakinsu Nuri darling. Nufar gadon yayi bayan ya mike ya janyota jikinshi kuka ta saka mishi. "Haka kawai ka bar na kwana ni daya yanxu kuma!" Rufe mata baki yayi a hankali ya shiga bin ta a nutse da yanayinsa me matukar sanyi da zafi, yanayin da yake kara haukatta, domin ji take kamar zata yi hauka. Sai da ya murzata sosai sannan ya sauke nauyin da yake kanshi, ya nufi ban daki yayi wankan tsarki ya dawo ya shirya yana kallon yadda take murmushi. "Please Papan Twins muje da kai!" "A'a ki je kawai!" "Amma!" "Bana son musu." "Shi kenan!" Ta fada tana kauda kanta. Bai damu ba ya shirya ya fita yanxu ba da bane, wurin aikinshi nan sabon wuri ne, Teemi kadai zata iya taimaka mishi yanzu tana can Scotland bata dawo ba, kuma da alamu na zata dawo ba, haka yasa shi mai da hankalinshi kan aikinsa. D'aga kai yayi yaga Nuri darling da me kula da ita, ta shirya ta amma taki sabawa da matar, domin Aliyyah fir taki yarda da budurwa shi yasa ta dauki Matar aure don kada a sake samun matsalar irin na Layla. Sannan abin haushi matar Kirista ce, duk da Maina yasan Layla kafira ce amma bai tab'a jin tsana ko tsangwama akanta ba, domin bata da akida sai tsafi, sauran kuwa akidarsu tana da wahalar sha'ani. Beside sai ya zubawa Aliyyah idanu shi bai da wanda zai iya cewa ga laifinta domin bai ga laifinta ba, tayi duk yadda take so. Gyara jakanta take tana fa in. "Papa na makara fa, darling sai na dawo." Ta sumbaci goshin Nuri darling, shi kuma ya shafa kanta. "Allah ya muku albarka!" "Amin Papa, yaushe zamu kaiwa Layla ziyara!" "She need some respect!" "Tow sister Layla!" "Good girl! Next week!" Ta fita da gudu, "Bye Papa! Bye Nuriyya!" Ta fita da gudu don motar makaranta yana ta mata horn, tana fita ta shiga tana fa in. "Sorry sir!" Girgza mata kai yayi. "Have your sit!" Ta tafi ta zauna bayan ta gaida wanda ta samu a ciki. "Eh ance babanta shine crown Prince na garinsu she's princess!" Murmushi tayi tana kallon gefen hanya, "twins ne yar uwarta bata nan, amma zata dawo makotan mu ne." Inji wani yaro da yake bayanta, bata juya ba domin tasan darajar gidansu Papa ne yake bibiyarta, sunkuyar da kai tayi tana bu e jakarta ta dauki abin da zata dauka ta duba sannan ta d'ago kai. "Hi!" Ya mika mata hannu, "Ni muslima ce!" Ta fada da murmushi a fuskarta, "sunana Adnan!" "Nice to meet, Sainah Hatim!" Ta fada tana kallonshi. Sun dan yi hira har suka isa makarantar, daukar mata jaka yayi suka fita tare, bata ce kome ba har suka shiga makarantar, shi ya wuce ajinsu ita kuma ta wuce nasu, tun daga ranar Sainah ta samu abokin tafiya kuma abokin karatu, lokacin da Maina ya ganshi sai da yayi ta bincikar shi don yaron tsoro ne ya kama shi, murmushi Maina yayi ya ce mishi. "Duk ranar da naji ka tab'a ko hannun Yata sai na yanke hannunka!" "Ba zam tab'a ri e ba kuwa Papa!" Ya fa a a tsorace. - Sanaya da tun ranar da suka hadu da Layla abin ya tsaya mata a rai, kallon Tirsila tayi da take ta cin abincinta hankali kwance. Haka yasa Sanaya ta ce mata. "Kin san Layla tana raye?" Kwarewa tayi tana tari,Sanaya ta mika mata ruwa. "kin razana ne ko? Na zata kin san tana raye ne, hmmm!" "Ban gane ba tambayana kike ko kuma kin ganta ne?" Mikewa Sanaya tayi zata fita, "Tana raye kuma zata dawo, yaushe zata dawo? Da waye zata fara? Shine ban sani ba " "Sanaya ki gaya min gaskiya Layla tana raye ne?" Tirsila ta tambaye ta idanunta jajjur, "Hmm! Eh ya rage naki da sauran da kuka hada kai kuka cutar da ita!" Tana fadar haka ta bar gidan, ita ba zata ara mata haske ba, su nimeta domin tasan ta sake ta fadi wani abu taci amanar Layla ce kuma Layla jininta ce, a hankali. -Yau ma jikinta a sanyayye ta nufi aji bayan sun gama normal class da suke na Ballerina, tana kallo Deenah da ta nutsu a jikin laptop tana aiki. "Layla Muhammad Hatim!" Juyawa tayi tana kallon security in. "Kina da baki!" A matu ar farinciki ta juya da gudu, "Layla!" Ina ta fita da gudu, ta nufi stairs na makarantar tana sauka don farinciki hada bibiyu take, Office din principle ta nufa, sai da ta nutsu kafin ta yi knocking aka ce ta shiga, bude kofar tayi da Nuriyya tayi arba, "Nuri darling!" Ya fada da karfi, tare da isa gaban yarinyar ta rungume ta, ta mike "baby I miss you!" "Didina!" Ta fada kamar zata yi kuka, itama haka. Bai juya ya kalle ta ba amma yasan tabbas ta samu nutsuwar da yake bukata ya ganta da shi. "Hmm! Wato Nuri darling kike sani!" Sainah ta fada tana tura baki. "Oh kiyi hakuri my twins." Ta nufe ta tana rungumarta. "Sir na gaya maka bata da matsalar kome ai." Juyawa tayi wurin da Maina yake zaune ta gaishe shi a hankali, bai juya ba ya amsa tare da mikawa principle din hannu ya ce mishi. "Mu dan fita da ita!" "Ba kome, amma ka amshi get pass dinta." "Okay" daga haka suka fita, har harabar makarantar, ta koma sama ta kira kawayenta ta gaya musu yan gidan sun zo, ai kuwa sai ga Yaran abinka da sabin balaga, kansu hayaki yake sai lokacin ya lura da kayan jikita ba uniform ba ne, a dan sake ya amasa gaisuwarsu, sannan ta rike hannun Nuri darling Deenah ta riko hannun Sainah suka tafi hostle dinsu, kaya ta sauya. Suna hira sama-sama, har suka shirya. Deenah ta rako su Deenah irin yaran na ne masu bala'in sa ido, ba zaka fahimci haka ba sai ka zauna da ita a yadda take kallon ilahirin Maina da yadda yake bin Layla da idanu, yasata murmushi. Har suka tafi a ranar yawo suka yi ta yi, sannan ya kaita ta ga gidansu ta ga gidan santin gidan take tana fa in. "Nuri darling wannan gidan yafi na Scotland kyau da girma. Sainah gidan yayi kyau gaskiya wanda ya zana gidan ya san me yake yi,kuma gidan ya dace da Papanku!" Yana jinta sai yayi fuska bai ce kome ba sai dare ya cewa Sainah. "Ki ce ta fito na kaita makarantar!" "Papa zamu bi ka!" "A'a dare yayi!" "Tow sai ka dawo!" Haka ta kirata suka fito tare, har wurin motar suka rakata suka yi sallama, ba karamin dadi ta ji ba, haka suka tafi. Suna tafiya daga shi har ita babu me wani motsin kirki, "Baki sake ciwon cikin ba ne?" Shiru tayi ta kasa amsawa domin kunya da take ji, har ya cire rai zata amsa sai yaji ta ce. "Eh ban sake ba!" Shi kama yayi kamar bai ji ta ba, dan leka shi tayi taga sam bai wani nuna alamar yaji ba. "Eh ban" "naji ai!" Ya fa a da sauri ta kifa kanta a cinyarta. Bai kaita makarantar ba sai da ya tsaya ya mata sayayya sannan ya wuce da ita. Lokacin da suka isa makarantar ya ce mata. "Nu drive dinki ne?" Girgiza kai tayi ya ce. "Oya dawo nan!" Da sauri ta fita daga baya ta dawo gaba. Tunda ta shiga yake kallon yadda ta nutsu. "Da fatan babu matsala ko?" Gyada kai tayi tana wasa da hannunta, shiru suka yi can ya ce mata. " Bana ce bana son ganinki da kayan da." D'ago kai tayi kamar zata yi kuka ta ce mishi. "Ina class din Ballerina ne, kayan rawan ne kayi hakuri, zan fita a class din." Kallon yadda take magna ne a nutse. "Ko need ki yi haka, kawai kina suturtta kanki ne." Gyada kai tayi. Juyawa yayi ya dauki kayan da ya saya mata, ya daura mata su a kan cinyarta. Kasa d'ago kai tayi a hankali ta ce mishi. "Thank you.....!" Shafa kanta yayi yana fa in. "Allah ya ba i sa'a, na
Chapter 56 · 0% Book details