Sashe 85
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauko ta ce mishi. "Ya jikinta?" Kallon aya yayi mata ya ce. "Alhamdulillahi!" Fitowar Ummimi da tayi ya ce. "Ummimi abinci nake son nayiwa Yara da Layla!" "Ka bada umarnin ka kawai ayi mana!" "A'a bari nayi dai!" Ya wuce kitchen din tare da Banafsha, ya zaunar da ita. Yana aiki yarinyar tana mishi surutu, har ya gama sannan ya jera suka nufi waje ya saka na Yaran a dinning room ya wuce waje. "har ka gama?" "Eh Ummimi!" Yana dauke da Banafsha suka nufi bangaren shi har lokacin barci take, daidai wurin kanta ya ajiye tiren abincin babu b'ata lokaci kamshin abincin ya cika mata hanci ta bu e idanunta a hankali tana hamma. ".Maza tashi ki ci!" Nufar ban daki yayi ya dauko mata brush da toothpaste, da ruwa ta wanke bakinta ya maida har da robar ruwan. Ya dawo ya fara cin abincin sannan ya fara bata, yana rarrashinta a hankali yana bata labari har ta koshi sannan ya fita da kayan, ita kuma ta wuce ban daki ta sake wanka tana fitowa, shima ya shiga wanka ko da ya fito ya samu bata dakin, can wurin Ummimi ta wuce. Ta samu tana waya da Bahiyya da take hanya. Cikin nutsuwa ta gaida Ummimi sannan ta wuce inda take jin muryan Nuri darling, duk da Ummimi tana mata magana ta jira girgiza kai tayi tana fa in. "A'a bari na ganta!" Tana shiga dakin ta samu wasu bayi biyu suna saka mata kaya ne. "Barka da safiya Gimbiya Layla!" "Kuje zan kula da ita!" "Ranki ya dade, Gimbiya Aliyyah ta!' "Ku je nace." Haka ta shirya yarinyar tass, sannan suka fito parlour Ummimi anan suka samu su Aliyyah tana karyawa. "Ina kwana Mum!" Ta gaida ta. "Lafiya ya jikinki?" "Da sauki sosai?" " Bari na kaiwa Malik abinci sai nazo muje ku gaida shi." "Tow ki dawo lafiya!" "Allah yasa!" Ta fita bayi na dauke da abincin a bayan. Kamar jira Aliyyah take ta fita tana murmushi tacewa Layla. "Duk da ciwo bai hanaki daukar nauyin miji ba!" Da sauri Layla ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kai tana wasa da hannun. Kamar zata yi kuka ta cewa Aliyyah. "Kin ga irin wannan basu dace da kunnen Nuri ba don haka kiyi hakuri ki daina fada!" Watsa mata harara tayi tana fa in. "Zaki koya min yadda ake tarbiyyar Yara ne?" Girgiza kai tayi tana fa in. "Ba zan koya miki ba, amma nasan dai babu kyau abin da kike fada ko don gidan da suke." "Ki ce har kin san dadin namiji!" "Mum please wannan ba mutunci ba ne!" "Shin yasa kike ciwon karya!" "Ki bari!" "Naji na bari amma ke mayya ce? Idan ba mayya ba ce taya Ahalinsa zasu karbe ki bayan basu tabbatar da cewa ke cikakkiyar mace ce ba, wanda aka yayyata jinin daren farkonta. Sai dai bikin tarewa da ciki waye sani ko ba dan Maina ba ne." Rufe mata baki Layla tayi tana girgixa kai."akan me yasa kike jifana da irin wadannan kalaman? Da ace ina son Mijinki da na gallabi rayuwarki ni ba Mijinki ba ne.." "Layla!" Ya daka mata tsawa. "Kika ce bakya sona?" Akan ce magana zarar bunu ce, idan ta fito bata maiduwa.."Eh Pap..!" Buge mata baki yayi sai da bakin ya fashe ya dan tashi ka an. "Ki godewa Allah bana duka da yau sai na saka gefen fuskarki amsa yatsuna, ki je kiyi duk yadda kike gara da kika fada min haka a gaban matata kin kyauta min." Daga haka ya wuce ya barsu Maina bai ji makircin Aliyyah ba, amma yaji kalaman Layla baki aya. Haka yasa shi fusata sosai har da fushi. Ita kuwa zama tayi tana kallon Aliyyah da take murmushi. Tab'a goshinta tayi ta ce mata. "Kafin kiyi magana ki fara nazarinsu.!" Daga haka ta barta a wurin. Koda ta gaji da zama ta lallaba ta wuce bangaren shi, yana ganinta ya hade rai. "Kwashe kayan ki, ki koma wurin Ummimi! Matar da take sona zata dawo nan da zama babu amfanin zama da wanda baya sonka." Kanta na mata wani irin ciwo idan tace zata yi magana amai zata yi shi yasa ta lallaba kanta, ta wuce ta ja akwatinta bata kula shi ba. Ta koma dakin Bahiya ta zauna. Sai bayan awa biyu ummimi ta dawo suka nufi bangaren Malik suka gaida shi, sun samu Auta da Salahudeen. Maina yana can Ammar da ya shigo ya gaya mishi ai yaga sun tafi wurin Malik, duk da ranshi a b'ace yake mikewa yayi ya bi bayansu ya ce Ammar ya jira shi. Haka ta tafi don kishi ya samu dakin kuwa da Yan uwansa maza. Cikin wani basarwa da hade rai ya zauna yana gaida Malik. "Matarka bata da lafiya ne?" Kallon fuskar Layla yayi da yayi ja alamar tayi kuka saman idanunta ya tashi. "Waye ya san mata!" Ya fada a hankali. "Kul ka tambaye ta, kada ka saka ta fara gurbataccen tunani su mata bibiyar lamarinsu ake idan ba haka ba zaka haifar da tarzoma a gidanka da kananun shekarunka. Ka zama Adali tunda babu baiwa a cikinsu matanka ne kada ka haifar da kiyayar da zata kai su ga hallaka." "In sha Allah!" "Layltu Qadr ko Laylatu Nur ce?" "Ai duka zata amsa." "Allah ya baku zaman lafiya, za ayi bikin ku nan da sati me zuwa za a fara dai daga gobe juma'a har zuwa wata juma'a." "Allah ya baka lafiya da nisan kwana, godiya suke!' "inji Ummimi. Daga nan suka baro bangaren Malik suka wuce na Ummimi, kallon yadda pink abayar da ta saka me shap ya fito da surarta yasa shi kasa hakuri ya fisgota suna sha ar numfashin juna ya ce mata. Janye idanunta tayi tana me sunkuyar da kanta. "Kada na kara ganinki da wannan kayan , na gaya miki kin wani je kin zauna kowa na kallon kirjinki da cikinki!" D'ago kai tayi ta kalle shi kafin ta sunkuyar da kai tana me jin shi bata ce kome ba. Tsaki yayi ya tafi bangaren shi duk yadda Ammar yaso yaji meke faruwa tsakaninsu amma yayi gum don baya son Ammar ya fara tunanin mai ya hau kan kaza. Har dare tana dakinta bata yarda ta fita ba, washi gari Bahiyya tazo haka ya rage mata damuwar Maina da tun a daren jiya ya kwashi Yaranshi da Matarshi suka tafi yawo sai wurin sha daya suka dawo, yunwa ya hanata barci shima da yake ya kasa danne zuciyarshi koda ya kawo Yaran dakinta ya kawo Nuri ya ganta zaune kamar mayya tana cin abinci me zafi da ta dumama. Ajiye yarinyar yayi ya ajiye mata abin da ya kawo amma ko kallo bata ishe shi ba, "Na gode!" Ta fada every calm kamar bata jin zafin abin da yake mata. Juyawa yayi ya kalleta sannan ta fita abin shi. Cikin dare tana barci yunwa ya sake farka da ita a lokacin ta ganshi tsaye a kofar dakin yana kallonta. Saukowa tayi ta nufi inda ya ajiye ko leda cikin fushi ya shigo dakin ya fauce leda. Kallonshi tayi kamar zata yi magana sai fasa ta wuce shi zuwa kitchen. Kunna gas tayi ta fara kokarin dafa noodle, yana zuwa ya kashe gas in. Kallonshi tayi kafin ta juya firgi ta shiga diban fruit, ta cika wani roba ta fita. Ta koma dakin ta zauna a tsakiyar gado ta fara cin apple da berries. Ranshi ya b'aci haka ya saka abin da ya kawo a firgi sannan ya kashe gas in kome ya dawo kanshi yaji kamar bai kyauta ba, ba ita aya ba ce. Don haka ya tsaya ya mata warm din abincin da yazo da shi, koda ya zo da shi ya samu ta cinye kome har ta shiga ban daki shiru shiru bata fito ba, ta saka shi nufar ban dakin yana jin yadda take shashekar kuka. Bude kofar yayi ya ganta durkushe tana kuka kamar ranta zai fita. "Idan kin gama ki zo ga abincinki." D'ago jajjayen Idanunta tayi ta kura mishi. "Na gode!" Ta fada tana me wanke fuskarta ta dawo dakin ta kwanta. Shi ya zata cin abincin zata yi sai yaga sam haka bai dame ta ba. Haka ta koma barci ya lullube su. Shi ne washi gari Bahiyya ta iso. Amma kuma ta lura a fusace yake da ita a yan kwanakin da aka fara hidimar bikin sai dai taji labarin an ganshi ya gabatar da Aliyyah a matsayin Uwargida, itama Aliyyah Iyayenta da Jasy sun iso. Ganin yadda ana bikin Layla bata gaban Maina sai Aliyyah da Yaranta domin yadda take kulawa da shi a gaban kowa sai ya baka mamaki shima kuma haka, sai dai abin da Aliyyah bata sani ba, Maina karfin hali ne kawai amma zuciyar shi yana wurin Layla. "Ummimi Wai meke faruwa ne tsakanin Ya Maina da Layla? Na kasa gane duk fitar da ake na bikin tana kwance shi.yana can da Matarshi akwai adalci a cikin wannan lamarin?" "Wallahi na mishi magana amma ya ce wai tana da ciki zata je tayi ta amai, inji Aliyyah shin yasa ta fita a madadinta." "Wannan son kai ne, sarina William yar kwallon tables tennis ciki bai hanata buga wasa ba, sannan yar kasar misara da ta lashe gasar Olympy tana da tsohon ciki ina cikin Layla zai hanata fita jama'a Ina cikin ya fito? Gaskiya rashin adalci da mu mata mukewa junan mu ya fara bani haushin don yarinyar bata da galihu sai a kyaleta." "A'a ba haka ba ne!" "Haka ne mana!" Dakin Layla Bahiyya ta shiga ta same ta zaune tana waya. "Kun kusa kenan?" "Tow sai kin shigo!" Kashe wayar tayi ta kalli Bahiyya. "Maman yan uku!" A fusace ta ce mata. "Tashi me kwalliya zata zo maza tashi a miki." Murmushi tayi me sanyi ta ce mata. "A'a bana son kamshin hoda a mai yake sakani!" Ta fada ne don Bahiyya ta kyaleta. "Amma!" "Please ki bar maganar Allah ya sauke ki lafiya Matar nan, kwanan nan babbar kungiyar kwallon kafa zasu sayi mijinki da mahaukatan kudi ina gaya miki" "Me yasa?" Murmushi tayi tana fa in. "Sultan yana bu atar space ne kuma ai nice mai lefi da na iya da harshe na