Sashe 8
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yarda su hada shimfida, amma ita kanta tasan Maina Jarumi ne, kuma sadauki ne me dakawa mace gumba a hannu bisa shimfida. Idanushi ya bude kan agogon ban dakin, da ya buga karfe goma sha biyu da minti ashirin. A gurguje ya fito tare da gyara jikinshi, ya nufi wurin wayar shi, ya dauka. Ammar Wazir ya binciko a hankali ya shiga kan kiran. "Amma dai Maina kai dan iska ne!" "Sai dai guguwa!" Ya fa a a takaice, "me xan maka a wannan daren?" "Karfe sha aya ina jiran ka!" Ya fa a kai tsaye. "Kutumar uban can! Maina me ka mai dani? Ni bawanka ne? Maina tsaya tukun zan zage ka wallahi." "Na nawa kuma?" Ya tambaye shi, cikin ko in kula. "Maina Allah ya isa min, yadda kake cutatta Allah ya bi min kadina!" "Bana son African time" Cikin ihu da hargagi Ammar ya danno ashar, tare da kashe wayar. Murmushi yayi tare da ajiyewa wayar bayan ya saka a airplane mode. Kashe wutar dakin yayi, sannan ya nufi closet inshi ya duba kayan barci mara nauyi, me taushi da laushi. Ya saka ya fito yana kallon yadda lokaci yake tafiya. Ban daki ya nufa yayi Alola sannan ya shimfida abin sallah, Yaranshi ya tuna ya nufi kofar dakin, ya fita dogon korridon shi ya nufa yana tasbihi, har ya isa dakin Yaran, Sainah ya samu zaune tana kallon window inkinsu. "Husaina!" Ya kira sunanta a hankali kallonshi tayi ta sauko da sauri ya fa a jikinshi. "Papa!" Mikewa yayi da ita, yana shafa bayanta. "Is okay gani nan!" "Papa!" Ajiyeta yayi ya nufi window ya rufe bakinsa dauke da sunan Allah, sannan ya tofa ayatul kursiyu, ya dawo ya rakata ban daki ya saka tayi Alola sannan ya dawo da ita dakin, ta kwanta ya dauki abin sallahsu ya shimfida, ya fara jeru sallah nafilla, tare da karanto manyan surorin Alqur'ani, Maina ta nan bangaren babu wanda ya isa ya ce ya kai shi, domin yana da kokari da kwazo akan kadaita Allah shi daya, shi yasa kowa yake ganin kamar yana yamar asalinsa. Wannan tsayuwar daren ya shagaltar da shi da zancen zasu shiga Palace, don sai karfe biyu da rabi ya idar, sannan ya wuce dakinshi. Dare ya raba aosai domin ana niman biyu da rabi, tafe take tare da wasu daga cikin amintattun bayinta guda biyu. Suna rike da fitilar kwai, daga yadda take tafiyar zaka fahimci gaggawa a tafiyar. Wani tsohon kofa aka bude musu, suka shiga a hankali suka nufi cikin gidan wanda yake tsohuwar fada ce. Wata kofa ce ta bude da kanta, kofar a kasa yake, a hankali matakala ya bude. Me dauke da fitilar tayi gaba,tana biye da ita. Har karkashin ramin. "Hmmmmmm! Hmmmmmm!! Hmmmmmm!!! Hamidah! Zan sha jini!" Tsayawa suka yi, a gaban wani kogon rami, arar sarka ne ya shiga kusanto su. A hankali wani irin halitta me kai uku ya bayyana a gabansu, kai aya ne yake magana kai biyu idanunsu a rufe. "Gorunfa!" "Hamidah!" "Tana bibiyarku ko? Ku bani jini na sha" kura mishi idanu tayi ta isa gabanshi. "Ina Falwan?" Gashi can a bayanki " juyawa suka yi, suka hango shi zaune akan iska. "Hamidah!" Zubewa tayi tana me daura hannunta akan gwiwarta."Na samu labarin Matar Maina tana da ciki " A hankali ya shiga saukowa daga saman, ya zauna akan wani dutse. "Maina ba zai lamunta ba,na gaya miki tun farko ai." "Wannan ba matsala ba ne,zan ji da shi." Shiru yayi ya ce mata, "Muna niman jinin danyen budurwa." Shiru tayi kafin ta ce mishi. "Ta ina zamu samu?" "Kiyi tunanin yadda zaki samo, domin ba zata daina binku ba, sai kun samo wata macen kun bata. Shi kuma gorunfa zan tura shi ya shanye cikin." Murmushi tayi tana juyawa ga gorunfan, ta nufi kanshi tana shafawa, "kayi aiki me kyau, Ayrah ma ciki ne da ita. Na sadaukar da shi ga gorunfana." Bude idanu sauran kayukan suka yi, bakinsu yana fitar da wani ba in ruwa. "Falwa ya zanyi da Maina?" Nufar gorunfan yayi ya saka wani abu ya huda fatarsa, bakin jini ya sirto kwalba yasa ya tara, sai da ya diba kafin ya isa bayan halittar ya kai hannu bayan shi yana shafa shi a hankali, fitar da wani irin abu yayi kamar bindi kamar karin kunama, ya shiga shafi bayan abin. Yana shafa bindin har ya cire karin ya shiga matsawa, halittar ya shiga wani irin gurnani, yana juya kanshi tare da fa in. "shugaba!!!" Yake fa a da arfi, wani irin ruwa ne yake diga ruwan rawaya, me kauri da wari. "Shugaba!" "Na gode gorunfana." "Yarinyar tana raye bata mutu ba!" "Wacce yarinya?" Inji Dowager Hamidah ta fada kamar zata kifa. "Zuri'arsu tana boye a wani dausayi. Rundunarta suna bibiyarta." "Falwa!" "Kada ki damu Uwardakina! Matu ar muna raye zan kare masarautar nan har fitar numfashina, zan kuma tsannanta bincike har sai na nimo wacece ita. Kafin nan ina son ko sani rundunarta suna bibiyar rayuwar Maina. Don haka dole ne ki tilasta mishi ya amshi kujeran Babanshi, shima Babanshi ki tilasta mishi sauka, domin idan haka bai faru ba, babu wanda ya isa dakatar da kome." "Falwa bana son Khamilah ta rab'i Maina, ina son na cigaba da kula da Uban da d'an, yadda babu wanda ya isa min iko da zuriata. Ina son nayi rayuwa kamar na kakata ta biyar, Queen Nabila Bint Muhammad." "My Queen zaki yi yadda kike so, a zuba a cikin turaren kamshi a gyara gidan lallai Maina zai zo, ni kuma zan tabbatar da daga yau zuwa gobe labarin jinin da Gorunfa zai sha zai tabbata, ita kuma a bamu budurwa mu sadaukar mata da ita, kafin faduwar ranar gobe." "An gama Falwa!" Ta fada, tare da amsar kwalbar ta mikawa, Bahira kwalbar suka fita a cikin ramin, Falwa yana karanto wasu kalmomin tsafi. "Namu Amida butsu!!!!" Har suka bar cikin fadar suka nufi cikin masarautar, tare da takewar masu tsaron lafiyarta. Wani irin iska me cakud'e da kura ya kaure musu hanya. Dariya aka fara mata. "Sai na dau fansata......" Kafin kurar ta b'ace suka shige da gudu, suna shiga bangarenta aka saka duk wani abun kariya. Tsayawa tayi tana kallon Bahira. "Babu bakin bayi ne?" "Ranki shi da e, akwai amma yan gudun hijira ne." "A Nimo kyakkyawar gaske wacce zata auke kome, a kawai Mutallab ya kwana da ita zuwa daren gobe a kaiwa Falwa." "An gama my Queen." Har zata fita ta ce mata. "Ina fatan Court lady bata fahimci sakon da take kawai gidan Maina ba ko?" "Eh ranki shi da e, tunda ai ba a hannunta nake bata ba, Princess Khamilah take bata." "Yayi kyau, Ayrah kuma Falwa zai ji da ita.... #Monday #Mai_Dambu [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s *MASU NIMA DAGA FARKO DON ALLAH GA LINK NAN SU SHIGA ZASU SAMU* ________________5 _Wai kun dage akan Queen Hamidah ko? Ni bance kome ba, amma tar take kallonku atow wannan pagen naku ne yan grp na Last Empress da fitilar hikayar Mai_Dambu Much love Omo jiya I see love a comments dinku ana zuba sharafi akan Dowager har bakin haure ba a barsu a baya ba sun juyawa Hamidah baya_ *MAN'S COLLECTION* *gidan Kamshi da gyaran jiki da maganin mata* *Ina uwargida da amarya da masu shirin gyara,shunkuna neman inda zaki samu ingantattun turaruka masu kama jiki da gida Wanda tundaga get za'a fara jiyo kamshin gidanki?* *shinkuna neman inda kaku samu magunguna ingantattu sha yanzu magani yanzu*? *Maza kugarzayo MAN'S COLLECTION* *tazomuku da turaruka masu tashin kan megida da kamshinsu munada turaruka kamar haka*