Sashe 91
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tun la'asar ake jiran Maina. Amma babu shi babu labarinsa. Karshe Ammar ya gaya masa sun fita da Layla. Aliyya kan kuka tayi ta saka gwanin ban tausayi........kuyi hakuri bani da lafiya ne ga shi ina fama da rashin lokaci amma biyu naso yi, amma In Sha Allah asabar da lahadi akwai update in sha Allah. Yanzu ina bude data mutane zasu hana ni kashe data abin ka da Yar baiwa da yan baiwa ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500N ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [9/21, 4:59 PM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu __________59 Shiru Malik yayi bai kuma magana ba, saboda yadda Queen Hamidah take fada, samun kanshi yayi da kallon Ummimi. "Bai kuma gaya miki inda zai je ba?" Girgiza kai tayi tana fa in. "Ina ga duk inda zasu tafi ya je ne domin yana bukatar mutsuwa, a kodayaushe ita mace musamman yadda aka mata kishiya yar hakuri ce, idan bata yi hakuri ba zata tafi ta barwa kishiyarta rikon Yaranta da Mijinta. Aliyyah a idan da Allah ya daurawa Maina irin dabi'un Malik da sauransu tow wallahi da baki isa ko d'aga kai, kina kunkuni ba. Yarinyar da kike ihu akanta ko ba a gaya miki ba kin haife ta. Sannan a shekarun da kika yi da Maina ya dace ace kin fita a harabar Masarautar nan kina ihu? Kin zubda mutuncinki a gaban jama'a, kin b'ata mishi suna da darajarsa na magajin garin Baihak. Na fahimci ke da iyayenki baku son zaman lafiya da adalci tow bari na gaya miki ba a haifi macen da zata d'agawa Yarana hankali ba, zaman nan za a kuma yin shi bayan sallah isha sai ki shirya idan zama da Maina Bismillah idan kuma kina da wani abu Bismillah!" Yadda Ummimi ta ware tana bala'i zaka rantse da Allah can masifaffiya ce, yadda Ummimi take fadar yasa Iyayen Aliyyah jikinsu yayi sanyi haka suka tashi taron wanda Abu Ammar ya samu zuwa. Queen Hamidah kuwa masifa take son yi amma ganin yadda aka ki kulata yasa ta ja iyayen Aliyyah tana basu hakuri. Sai da suka dawo wurin su Jasy take had'a kayanta dama basu je da ita ba. Itama bata damu da su je ita ba. "Jasy ina zaki sai gobe ne zamu tafi ai!" "Eh na samu jirgin da zai shiga karfe uku na daren yau zan tafi Yarana suna jirana da kewata?" "A'a don Allah ki bari gobe!" "Wallahi yau xan tafi!" Ta fada tana murmushi. "Anyi miki wani abu ne?" Inji Baban Aliyyah, "kodaya!" Ta fara kokarin kiran line din Maina, ba a dauka ba hakan yasa ta an jirkinta tafiyar. Safa da Marwa Queen Hamidah take. Ta rasa me tayata ha a wannan kullin sai ga Ayrah nan suka shiga kulla sharri amma akan Layla. A can kuwa sai da yayi sallah isha sannan ya zo ya samu tayi barci wayarshi ya kalla ya ga kira babu adadi. Na Ammar ya fara bi ya danna mishi zagi, kafin ya kuma kiran Ummimi da Malik babu wanda ya ce mishi cikanka karshe haka ya kashe wayar. Kafin ya kira Jasy ita ta gaya mishi ana ta niman shi itama tana son komawa gida ne kuma cikin dare jirgin zai tashi. "Ina ga ki gari ku tafi da yammacin gobe mana Please naci wannan alfarman!" "Shi kenan Baban twins na hakura Allah ya kai mu!" "Na gode sosai!" Ya kashe wayar yana murmushi, rike hannunshi tayi tana Kallonshi. "Don girman Ubangijinka kada ka rabu da ni ka ji!" Girgiza mata kai yayi yana fa in. "Ba xan rabu dake ba har abada mutu kara ba sunan aurenmu!" Daga haka ya ja motar suka nufi cikin masarautar. A lokacin da suka isa sako Ammar ya tura mishi. "Ka same mu a bangaren Malik!" Rike hannunta yayi suka nufi bangaren Malik din, lokacin da suka shiga duk aka zuba mata idanun. "Assalamualaikum!" Yayi sallama. "Kaci abinci? Itama taci saboda abin cikinta?" Malik ya mishi wa annan tambayoyin. "Eh taci Malik nima naci!" "A'a baka ci ba, ruwa lemo kawai ka sha fa." Ta fada tana kallonshi. "Ka je ga abincin da Umminku ta kawo ku ci sai ku zo!" Abin ya bawa kowa mamaki, ban da Abu Ammar da yasan tabbas wata rana za azo wannan gabbar wanda yasa daga nan babu wani shinge da za a kara sakawa tsakanin duk su biyun." Tunda suka zauna ya tsaya ta zuba mishi abinci, baki aya Maina idan yana gaban Layla mantawa yake da kome domin matukar abinci zata bashi mantawa suke a inda suke haka ta tsaya a tsaye akanshi sai da yaci abincin sannan ta zauna ya bata, ta rike hannunsa. "Kayi min al awarin zama da ni!" Gyad'a mata kai yayi. "Ka rufa min asiri kada ka rabu da ni!" Ta fada hawaye yana zuba mata. "Ba zan iya rayuwa babu ke ba, nayi miki alkawarin wannan." Daga haka ya ja hannunta suka dawo parlour. "Muhammad!" Malik ya kira sunan shi na gaskiya. "Na'am Abba!" "Meke faruwa ne a gidanka?" Shiru yayi yana rike da hannun Layla da ta makale a jikinshi. "Abin da na sani ina son matana dukkansu biyu, shi yasa ban kasance daga masu bibiyar wasu bayin ba, daga Aliyyah har Layla ina sonsu. Darajata da duniyata Aliyyah ce, ita ce ta saka farin ciki a idanun kasashen kuma ragon maza farin ciki, Abba ina son Aliyyah ba wai a matsayin ta bani kyautar gwala-gwalai ba, a'a ina sonta ne saboda ita ce mace ta biyu a daraja a rayuwata bayan Mahaifiyata. Aliyyah darajata da kimata da duniya ta yana tattare da ita, da zaran babu ita to yasashen duniya ne ni mara amfani da kyau, ina son Matata!" Kallon Maina Aliyyah take idanunta cike da mamaki da kwalla dama yana sonta har haka ne? "Tow Aliyyah kin ji me kike bukata?" "Ya rabu da Layla! Zan kasance kamar baiwa a gare shi." "Muhammad ka ji me tace?" Rike hannun Layla yayi yana kallon kasa fuskarsa dauke da mu murmushi, Layla kuwa kallonshi take jikinta yana rawa. "Abba!" "Na'am Muhammad!" "Idan na gaya maka gaskiya zaka yarda ni!" Gyada kai Malik yayi Maina ya juya ga Layla. "Rayuwata da numfashina sadaukarwa ce ga Layla Jafar!" Ba iya Aliyyah ba hatta Ayrah da take bakin kofar sai da ta antayo parlour. "Sannan duk wanda ya kalubalence ni, zan yake shi har sai na daina numfashi. Idan Aliyyah tana da ra'ayi ta zauna dani idan bata da ra'ayi zata iya yin duk yadda take ba zan iya rabuwa da Layla Aisha ba!" Kuka ne ya kwacewa Aliyyah. "Yanzu kace kana sona! Me yasa ba zaka rabu da ita domin Yaranmu ba, Arniya ce kafirai ce bata da addini sai kafirci, ni uwar Yaranka ce ina cikin jerin matayen da Allah ya kawo cikin Alqur'an a Suratu nisa'i da Suratu Nur! Kada ka bata rayuwarka babu abin da ya kawo ta cikin rayuwarmu sai fansa da ramuwar gayya ita in matsafiya ce Malik ga shaida!" Ta watsawa Layla wani farin abu a fuska, atishawa ta fara kafin ta fashe da kuka, tana rungumar Maina. "Sultan!" "Kada ki damu, babu abin da zai faru." "Me kika aikata?" Murmushi Queen Hamidah tayi tana jin dadin shawarar da Tirsila da Ayrah da Aliyyah suka tsayar na a fitar da Layla a rayuwar Maina dole a bayyana suffar ta. Sai dai kuma kafin su iso a masallaci Maina ya hada Jafar suka gaisa kafin ya ce mishi. "Ka tabbatar ka bata wannan taci no matter how, taci ka tabbatar taci yarinya ce kuma da na ganta a tare da kai nayi imanin zata samu kariya domin kai garkuwa ne a gareta. Ina daga nan xan taimaka muku " cike da Mamaki Maina ya ce mishi. "Dr amma!" "Mahaifinta Jafar Zafir sakona ya isa hannunku!" Jikin Maina ne yayi sanyi wannan zuri'a da ban tsoro suke. "yarinya ce kuma ban san yadda xan dakatar da abin da yake faruwa ba,Yarima ka tabbatar kana tare da ita, kada ka bari wani dalili ya saka ka juya mata baya, kana yin haka wallahi babu wanda zai tsira a cikin Baihak!" "Ban fahimta ba!" "Zaka gane haka, tsorona daya kada ta kasa sarrafa jikinta, kasancewar ba ita aya ba ce. Bana son ta kwace a hannunmu ka saka idanun akanta!" Da wannan suka rabu shi kuma Maina ya tabbatar taci abin da Jafar ya bashi, sai gashi ana zaton zata fara ihu da hauka sai aka ga Lafiya lau barci ne ma ya kwasheta, Bawan Allah ya kwashi Matarshi ya wuce bangaren Ummimi da ita. Ya kwantar da ita ya zauna a gefen gadon. Wannan abin da ya faru yasa Malik cewa. "Tow yanzu hukunci yana hannunki Aliyyah da ke da iyayenki, idan kina son zama da Muhammad dole ki zauna da kishi ko abu Ammar?" "Akwai sarki me adalci ai nan gaba mata biyu za a kara mishi tunda baya bukatar kwarakwara, kin ga wajibi ne a gare shi ya rike mata hudu." "Na hakura da Maina ya bani Yarana da sakina!" "Kaicona! Inji Ummimi. "Kina tsammanin zamu baku yaran ne?" Inji Malik, "Yaranmu basu tafiya ko ina idan muka rabu da iyayensu mata, suna tare da mu ne, sannan masarautar mu bata saki zaki iya tafiya amma bama saki Malik bai tab'a saki ba kuma Maina da yake Sarkin Gobe na xai yi saki ba!" "Abby ba zaka yi magana ba!" "Akan me xan yi magana? Bayan ya nuna mana girma da darajarki, ko daya ba tsoron saki nake miki ba tsoron kewar Yaranki ya ishe ki, tsoron kin haifa masa Yara kin barwa kishiya miji da Yaranki nake tsoron kada ki zama lusara!" "Ummina baki ce kome ba!" "Me zance tunda kin zabi haka shi muje!" Su basu yi niyyar tafiya da Aliyyah ba, kuma abin da ya kara kashe masu jiki yadda tayiwa Layla Abu Amma babu wanda ya mata magana kuma ta ce tana bukatar saki nan ta samu Ansar ta yasa ta jin sanyin jiki. "Idan na cigaba da zama sai na kashe su dukkansu!" "Ba zaki iya ba, na gaya miki tun yarantatta na ga mutuwa kiri-kiri barazanarki ba zai bani tsoro