Sashe 64
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
musamman yadda Auta yake shige mata sai wani hoto yake tare da ita yana wani tab'a kafadarta da riko hannunta, Deenah da tazo wurin ta ga Maina a mota yana latse latse a wayarshi. "Excuse, Layla ana kiranki yanzu zamu dawo!" Mikewa tayi ta bi bayan Deenah sai da suka b'acewa ganin su ta juya tana fa in. "Dalla can ba wani kiran da aka miki, kin wani zauna sai tab'a kafadarki yake yana wani hoto dake, sai kace dan daudu. Ga Papi can zaune yana." Maganar bakinta ne ya tsaya sakamakon hango Maina da tayi, "oya gashi nan sai ki." "Barka da warhaka ranka ya da e!" Murmushin da bai san lokacin da ya sake ba, ya jingina da bango yana fa in. "Barkanki kawarmu!" Wani irin fashewa kanta yayi ta zube kasa tana fa in. "Godiya nake Baihak Crown Prince Mr Hatim!" "Allah ya albarkaci rayuwarki, ki zala Jakadiya na kwarai ga kawarki;" "na gode ranka ya dade, kuma zan yi yadda ka ce, ba zaka tab'a samu da abin da ba haka ba, godiya nake na Barka lafiya." Ta mike tare da barin wurin, ita kan Layla diriricewa tayi tana zare idanu. Shiru yayi can yayi nisa kafin ya ce mata. "Ina ga zan kira Hajja ta gaya miki matsayina har idan nace kada na kara ganin abu kike aikatawa." D'ago kai tayi da sauri ta kalle shi, yadda Idanunshi suka yi jajjur yasa ta sunkuyar da kai. Cizon bakinshi yayi sannan ya cigaba da magana. "Wato ga dan iska!" Ya rasa ta yadda zai balbaleta da fada ya ji sau in abin da yaga Auta na mata. Sai yayi kwafa ya ce mata, "Daga yau zaki bar makarantar ki koma wancan apartment din da zama sai dai aka kawo ki!" Bata ce mishi kome ba, kanta a kasa har zai bar wurin ya ce mata. "Kuma ki saka dogon wando sannan ki ka sake Auta ya kuma rungumarki sai na sab'a miki!" Barin wurin yayi ya wuce office din principle, a can suka sha hiransu kasancewa old friend dinsa ne a jami'a tare suka yi karatu da ita, tasan shi ya santa. Layla da ta koma hostle ta saka wando ta gyara kayanta ta kuma fitowa, a wannan karon gefen Bahi da Sainah ta zauna yadda Auta ba zai dame ta ba, sannan wani abin burgewa yadda Aliyyah ta sake tana mata bayani akan falalar da Allah yayiwa Prince Auta ( abin haushi nama na jan kare) ita kan bata ce kome ba, domin kanta a sunkuye yake haka suka ci gaba da hira. "Didi ina zaki zo mana hutu!" Da wutsiyar idanu ta kalli Aliyyah kafin Aliyyah tayi magana Bahi ta ce mata. "A'a wurina zata zo hutu." Daidai isowar Maina da yace. "Zata wurin Hajja ne ta ga gida!" "Papa zan bita!" Ba tare da ya kalli Nuri darling ba ya ce mata. " Ok Baby zaki bita ai didinki ce ita!" "Papan twins na zata anan zata mana hutu!" Karkad'a key yayi yana fa in. "Can za tafi!" "Bro ni zan kaita." "Tayi maka kama da dan jagora take nima?" "Tow ni dai ta zo min hutu!" "Gidanku da baya rabuwa da kartin maza ne zan tura yar Hajja wurinki!" "Tow Papa ka bar mana ita kawai!" Shafa kan Nuri darling yayi ya ce mata. "Mum dinku vata son bakuwar fuska, zan mai da ita wurin Hajja ne ta ga Mamanta itama!" Sam babu wanda ya fahimci dalilin Maina na raba su da ba, har suka gama mata ziyaran, suka tafi wurin karfe takwas dama principle ta gaya ta hada kayanta zata koma gidanta. Haka ba karamin matsanancin damuwa ya sakata, har da kuka Deenah kuwa ta ce mata kada ta damu zasu na zuwa mata hutu, sannan suka fitar da kayan aka yayyafi suka isa apartment din, drive ya tura ya daukota bata san yana gidan ba, sai da ta kai hannu zata bude kofar ya bude mata kofar. "Welcome to your house!" A hankali ta tura kanta cikin gidan idanunta cike da kwalla tare da takaici. Amsar akwatin yayi ta sake mishi tare da nufar cikin parlour ta zauna tana me fashewa da kuka. Yana jin kukanta amma bai damu ba, haka ya kai kayan da kanshi ya shirya mata, sannan ya dawo parlourn yana ha a mata abinci ya zo ya ajiye mata har lokacin kuka take, yana zama a kusa da ita ta wani ja baya a firgice tana kuka. "Me aka yi miki?" "Ni....ni.... Ni dai kawai a maida ni wurin Hajja bana son zaman nan!" "Da aka yi miki me?" "Kawai bana son zaman nan ne" kallonta yayi sannan ya ce mata. "Ok!" Ya mike tare da nufar daya dakin ya shirya ya fito zao fita. "Ni fa ba zan iya kwana ni daya ba, tsoro nake ji!" Ta fada tana kuka tare fa bubuga kafarta a asa. "Wannan ne kuma baki isa ba, kowacce mace haka take zama a gidanta har ta saba." "Ni dai ba zan zauna ba!" Ta fa a tare da nufar kofar fita daga gidan, wani irin fisgarta yayi ya matse ta da jikin bango. "Don't try me! Ki zauna like I said." A tsora ce ta kalle shi kafin ta fashe mishi da kuka har jikinta yana wani azzaben rawa. Rungumarta yayi yana shafa bayanta. "I with protect you, har karshen rayuwata, ba zan tab'a barin wani abu ya same ki ba. " Ya fa a yana shafa bayanta, lumo tayi tana shashekar kuka. "Ya isa haka! Muje ki ci abinci." A hankali ya wuce da ita dakinta, ya cire mata takalmin kafarta, tana kallonshi. "Kace zaka bani kariya har karshen rayuwarka?" D'ago kai yayi yana kallonta, itama shi take kallo, wayar jikinshi ne yayi kara, ya auka. "Dr Abbas ya me jikinki?" "Am sorry to say, matar nan ta rasu?" Kallon Layla yayi a hankali ya mike tare da barin dakin. "Taya ta rasu?" "Ranka ya da e, ban san yadda aka yi Queen Hamidah ta san da labarin ba, tazo dai kwana biyu da suka wuce yau da safe aka samu gawarta, abin da yasa na gaya maka nima yau da safe na samu sakon blackmailed ta wayata da Office dina, Rayuwata tana cikin hatsari na turo maka iyalina da binciken da na hada na dalilin mutuwarta, idan ka ji labarin mutuwata please iyalina su samu kulawa da tsaro daga gare ka ni kan nasan bai dole na kubuta ba!" "Kada ka damu!" Kashe wayar yayi sannan ya kira Salahudeen ya gaya mishi yaje shiga sojojinsa su dauki Abbas su kai shi bangaren Malik. Sannan ya koma dakin ya ga Layla durkushe tana wani irin kuka, tare da rike kirjinta, - Baihak murmushi Hamidah tayi tana kallon gasar Kalfanah da take kwance a wurin. "Nurse Jalilah kin kyauta, Tirsila duba gawar zata yi kuwa?" A hankali ta nufi kan gawar Kalfanah, ta dafa tare da lumshe idanunta, jini ne ya fara bulbulowa daga hancinta. Ta sake gawar da sauri Falwa da yake bayanta yana fa in "Me?" "Mahaifiyar Layla ce!"sake sandar tsafin shi yayi tare da takowa wurin ya fashe da dariya, ya ce mata. "Lallai zamu yi aiki cikin sa'a da nasara!" Juyawa yayi ya kalli Nurse Jalilah ya ce. "Queen kin san aikinmu bamu yarda da kowa ba!" Kafin Hamidah tayi magana jini ya fantsamu a fuskarta ta da ko ina. "Kiyi hakuri Jalilah aikinmu ne ya biyo kanki, shima Abbas din yana hanya sauka lafiya." Dariya suka fashe da shi domin wannan shine karshen alewa kasa. Daga nan Hamidah ta ce a cigaba da niman gawar Rihanna. Wanda aka tabbatar da cewa matukar tana son Maina ya rabu da soyayya tow dole sai an tashi Rihanna a wani gangan jikin, shine suka bazama niman mara lafiyan da basu da galihu, ta hanyar kai ziyara asibitoci anan ta ci karo da Kalfanah anan ta fahimci babu wanda yasan kome akan Kalfanah sama da Jalilah, don haka aka yi ta mata romon baka tare da zuba mata kudi, ita ta kashe Kalfanah da hannunta, sannan ta shiga blackmailed din Abbas, wannan yasa yake ganin kashe shi zasu yi don ta gaya.musu Maina yana tare da mara lafiyan. Wannan shine abin da ya faru. Bayan sun gama Hamidah ta koma masarauta. Sai da ta leka Malik anan ta ga Dr Abbas yana duba Malik. "Kai waye ya kawo ka nan?" "Muhammad Maina Hatim!" Gabanta ne ya fadi. "Kana nufin ka tsira!" "Rayuwar Malik yana hannunshi!" Inji Salahudeen da ya fito daga ban dakin Malik ya zubar da fitsarin Malik. "Idan kina tunanin zaki kashe abbas tow Baihak kika kashe domin kema baki san me kike ci kike sha, waye ya sani ko gawa tafe............. Jiya nace ku min Referral amma na rasa wanda zai min kuci kanku, Ku sha bakin ruwa [9/2, 9:29 AM] Hafs: _ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu *Alhamdulillahi Na gode sosai da addu'arku Allah ya saka da alkhairi lafiya ta samu ___________39 Tunda ya cillata cikin motar take shashekar kuka, yadda take kukan yana kara yamutsa mishi lissafi. Sai da yayi tafiya me nisa kamar zasu bar garin Washington DC, kafin ya tsaya a wani unguwa me yawan itattuwa da rashin cunkoson mutane, yanayin wurin kana gani zaka fahimci babu wani mutane sosai sai, a hankali ya gangara gefen hanya da ua kai shi wani unguwa da kana ganin kasan gidaje ne da aka yi su da asalin katako masu kyau da inganci, irin gidajen turawan da zaka gani a cikin Film an kawata gidajen sosai. A hankali yake tafiya har wani gida me kyau ga akwai Dawakai a can gefen gidan, sai can kadan da gidan kuma dabbobi ne ana kiwonsu. Wasu kartin maza guda uku ne suka fito dauke da wasu bindigogi suna ganinshi suka sara mishi tare da bude motar. Ganin har lokacin bai fito ba yasa suka watse. Sauke kafar shi yayi daya yana an goge kasa da shi, "Ba zaki min shiru ba?" Ya daka mata tsawa da yasa ta sake wani marayan kuka irin na shageabbabun yara da suke niman rigima. "Ki min shiru nace ko." Ya kalleta ta madubin motar, ganin yadda ta takura kanta yasa shi hasala. "Ya