Sashe 112
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
itacce. Kamar wacce aka d'agata sama, tirsila ya nufi Hamidah wacce itama burinta ne ta soke Layla da wukar tsafi, sai aka yi rashin dace ta sokawa Tirsila itama ta soka mata suka yi juna. Ihu suka yi tare, "Allah ba azzalumin sarki ba ne, yau dubunku ya cika!" Layla ta fada tana komawa bayan Ammar tana murmushi. "Wazir Ammar Halifa. Ga sakon Malik nan a karanta kowa ya ji abin da ta kusan." A hankali magatakardan masarautar ya karanto jawaban Malik da ya rubuta, daga farko hakuri ya bada tare da tabbatar da kuskurenshi sannan ya bukaci a san wacce Hamidah da danta, kafin aka dawo kan Mulki da kuma wanke Maina yadda zai rike masarautar. Daga nan ta juya tana kallon Magatakarda tace. "An sauke wanbai, Chiroma, makama." Da tayi ta zayyano manyan fadar tare da sakawa a fitar dasu ba fada ba zagi su bar Baihak, ita kuwa Hamidah waje aka yi dasu kamar kayan wanki aka watsar da su. Haris ya juya yana kuka ya ce mata. "Allah ya isa min, kuma wallahi a ganki a cikin garin nan sai na kashe ki." "Kuma kai ne dole zaka dauke su ba, aya kasan yadda zaka yi da su." Inji Ammar yana zare mishi idanu, dama can baya kaunar Mutumin. Da Umarnin Layla aka shiga gyara fadar ra ciki da waje bangaren Hamidah aka gyarawa Annah, sannan wurin Ummimi aka gyara fasalin ginen, sai dai tunda ta dawo gida bata da lafiya karfin hali take. Tare da boyewa, Ummimi ta ji sauki sai dai ana gaya mata abin da ya faru take ciwonta ya kuma tashi, dole aka wuce da ita Cairo tare da Maina da Layla sai Yaran. A wannan lokacin Maina ya gana da manyan yan kasuwa ciki da wajen nahiyar Afirka, har da Abdulmajid Mamman Ba'are. Sannan yayi musu alkawarin idan ya samu lokaci zai ziyarce shi. Rashin lafiyar Ummimi wasa wasa Sai da ya kwashi wata takwas, domin A lokacin Aliyyah har ta haihu, sai kiran Maina take amma yayi biris da ita. Haka yanayin ya cigaba da tafiya akwai dad'i da rashinsa. A can Baihak Salahudeen yake rike da garin da gidan da ake ta aikin gyaranshi. Ba karamin kashe kudi ake ba, Auta yana cikin masu zaman fada don ma Allah ya taimaka yana da ilmin addini sosai, shi yake lura da abin da ya shafi addini. Ba atab'a samun karnin da aka samu matasa a matsayin Sarakuna ba sai a wannan karnin, iyayen fada suka kama.kansu tare da tsayawa da Shawara a matsayinsu na iyaye marasa suka kame kanshi a matsayinsu na yan koyo. A wannan lokacin Salahudeen kamar yayi hauka domin ya fahimci Maina cikawa bujenshi iska yayi baya kaunar sarauta. Malik da Malika sun zama abin kauna ga kowa, ga me kula dasu tana ji dasu. Don ma Uwarsu tsoron haihuwa ne da ita, mahaifinta Jafar ya bata address din dangin Mamanta a Kuwait, ta kuma nimo su anan ta samu itama Mamanta yar babban gida ce ta fada soyayyar Jafar, irin kaunar da suka nuna mata yasa ta kasa boye farin cikinta. Kwana biyar kenan da barin garin a tunaninta zasu tafi gida ne nan yake ce mata. "Haeda zata wuce Baihak da Yara. Muje ki raka ni Nijar!" "Ummimi fa?" "Wai tsohon labari ai ta warke sun koma Baihak." "Ban yaye Yarana ba!" "Ni na yaye su zan cigaba da shan nonon har ki yaye ni!" "Papa wannan son kai ne fa!" "I har da son kafa duk daya ne!" "Gaskiya ba a musu adalci ba!" "Haka na yanke!" Daga haka ya wuce daki tasan fushi yayi don haka ta shige dakin suka fada shagali, washi gari Ya saka Haeda a jirgi sannan ya rike hannun yar kwailarshi suka tafi yawon bude idanu. Yasan matukar ya koma Baihak yadda ake jiranshi zai yi wahala su kara barin shi ya fita wata asa. Kwanansu biyu suka wuce Nijar, anan ta hadu da Zahra Majid lokacin tana cikin ta kama aikin mijinta, kwanakin da suka yi Zahra ta tausayawa Uwargidan Maina domin wannan yarinyar me kirji kamar na bera zata iya kome. *** Da karfe daya na rana suka isa Baihak, sai murna ake sun dawo ana ta shagali. A gajiye suka shiga Masarautar sai biki ake na murnan dawowarsu, tunda suka shigo gidan basu kuma haduwa ba, sai dare ita tana tare dasu Ummimi da kuma Yaranta baki aya, wato Sanah da Sainah, Nuri darling da Banafsha, sai Malik da yake cinyar Nuri darling don Bai da Uwa da ta wuce ta, itama son shi take kamar tayi yayya. Har ana musu dariya. Kallon Sainah Layla take tana kara sake baki. "Hmm Mami ai dating take da wani ban san waye ba!" Ware idanu Layla tayi tace mata. "Saurayi?" Wayar faduwa tayi kasa tana me bin wayar. "Bani waye kika samu?" "Inji Maina da ya shigo. Ajiye wayar tayi ta kwasa da gudu. A hankali ya duba. "Kan Uba!" Ya furta da karfi tare da nufar waje da sauri. Ya same shi a inda ya barshi yana makale da jikin bango kamar kadangare. "Idan ban ci Ubanka ba, me zaka yi da Sainah da kace baka so!" "Kasan dai Ubana ya mutu, sannan a matsayinka na surukin zamani wallahi zan iya ware wando muci uban juna dan iska kawai uban waye yace ka haifa mana kyawawan Yan mata." "Dan iska karuwan namiji!" "Tsohon banza tsohon najadu! Ina kai nan kayi ta rawan.kafa akan yarinyar da bata da kome don nayi chat da yarinyar da ta isa mace laifi ne! Amma Maganar gaskiya ina son Sainah da aure!" Wani ha e rai Maina yayi yana fa in. "Ba zan baka yata ba, bayan ka gama.cin mutuncina!" "Yo ai kaima kaci mutuncina fa!" Abin kamar wasan Yara daga arshe dai an rabu Maina ya ce ba zai bawa wanda baya girmama shi auren yarshi ba, shi kuma Ammar da baki.yace wallahi ko mutuwa yayi sai ya auri yarsa rigima dai sai gashi har parlourn Annah. Wacce ta rasa yadda zata yi da su don dariya tarasa yadda zata yi dasu tace musu. "Yanzu ku dawo gobe a tattauna sai muga waye zai hakura a cikinku!" "Anna ina son yarinyar nan itama tana sona meye laifina da uban banza zai hanani aurenta" "Kut Anna kina jinshi ai yana zagina naga wanda ya isa ya baka Sainah!" "Allah zai bani ita don Ubanka an zage kai sai me kai din banza kai din wofi wallahi sai na aureta." ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500 ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [10/16, 10:12 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________79 "Tow kai Ammar ka daina zaginshi mana!" Inji Anna, "tow na daina!" "Kai kuma Maina kayi hakuri a bar maganar nan gobe ayi " a fusace ya bar parlour ya nufi gidanshi. Layla tana tsaye gaban Mirror ta ganshi ya shigo ajiye turaren tayi tana fa in. "Kai da waye?" Ta karasa gabanshi tana me rungumarshi. Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi. "Ammar ne yake son Sainah!" "Wow abin yayi kyau!" "Sai dai ni ba zan bawa wanda ya rena ni auren yata ba!" "Hala Yarka gwal ce da ba zaka bashi ba, malam ni da ka aura ne yasa Babana bai ki ba, Aure fa an gama yin shi sai ka bashi ita!" "Ba zan bada ba naki!" Tura shi gado tayi tana fa in. "Zaka bashi ko ba zaka bashi ba?" "Layla kada ki shiga rigimar nan!" Ai kuwa ta shiga bashi sakon da da kanshi ya fara rawan jiki daga yarinyar nan ta saka shi a lungu tayi ta more dan Ummimi. Da kanshi ya ce ya bada auren Sainah a ruwan sanyi. Washi gari Ummimi ta turo Auta ya zo tana son ganinsu har da Sainah. Sai hararanta yake idan Layla ta ga abinda yake mintsininshi take sai ya dawo hanya, haka suka hadu a parlour Ummimi. Bayan an karya suka fara magana, "Husainah kina son Ammar!" Gyara zaman madubinta tayi tana satar kallon Maina. "Addar Malika kada ki kalle shi kalli Ummimi da take miki magana, kin ji yar albarka." Kamar yayi kuka haka Maina yake kallon Layla da ta kasa ta tsare ta kuma ce mishi ya sake yayi magana wallahi sai ta gamu da shi. Ta wasa da kayanta tunda ta kalli Ummimi ta sunkuyar da kai tana murmushi, "Tow Masha Allah, kai Maina meye matsalarka?" "Auren ce ban amince da shi ba, wannan ba soyayya ba ne wayo yake son yayi mata." Dariya abun ya basu Layla ta ce mishi. "Ba wani wayo ka samu me son Yarka zaka fara rikici hala tsofa ka fara." "Ni dai ba zan bashi ita ba." "Ummimi me zaki ce da wannan lamarin ke da Baban Khalid!" "Allah ya sanya alkhairi!" "Uncle Auta da Uncle Ibrahim fa!" "Allah yasa ayi a sa'a shi kuma sabon Sarki Allah ya taya shi riko!" Baki aya suka hade kai, wani irin abu yake ji ganin yadda yarinyar ta gudu daga cikinsu, shima ya fita yana me bin bayanta, garden ta nufa ta zauna tana ta kuka da dariya. Zama yayi a kusa da ita. "Kina cikin farin ciki ko?" Kwantar da kanta tayi a gefen kafadarshi. "Am sorry Papa!" Ta fada tana jan kuka. "Hey I'm gald da kike son Ammar domin ko baki amince ba, zan so ba bashi dayanku. Ammar ya cancanci na bashi duk wani abu me daraja a gare ni. Har da ku kuna cikin abu me daraja a gare ni." D'ago kai tayi tana fa in. "Me yasa kayi ta fada tow?" "Saboda ina son na ga how he love you! Nasan jiya ko barcin kirki bayi ba, kaf duniya bani da abokin sirri irinsa. Kiyi hakuri da shi amma mutumin kirki ne, yana da amana da nagarta sannan mutum ne da yasan darajar mutane da mace baya wulakanta mace, ki mishi biyayya sosai shi Uba ne a gare ki ba miji ba, Ni kuma aminina ne." Gyaran murya Ammar yayi yana fa in. "Zagina ake?" Ita kan sunkuyar da kai tayi. "Cewa nake idan kayi mata iskanci ta gaya min naci mutuncinka!" "Hmm! Yarinya Wai haka ne?" Da gudu ta