← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 115

Sashe 7

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maza kiyi min rawan baya." Yadda tayi maganar yasa Tirsi bata san lokacin da ta kama rawan baya ba, sai tayi gaba sai tayi baya. "Yawwa juyawa kuka had'awa da tashi sama kamar tsintsaye Wagaduwada tana sanya muku albarka, lallai ku mutanen kirki ne;" "Malamin majami'a ba haka ake rawan ba, kayi min rawan tumbi, yawwa rawan tumbi rawan tumbi." Ta mike tana tura cikinta, shima ya kama. "Wakilin birni, kaga kanka kamar bayan tasa. Maza kayi min rawan maciji maza Uwargijiya tana saka muku albarka " Kallon yara tayi ta ce musu, "Yawwa yara, a girgiza a juya a taka!" Kuma duk wannan iskancin babu kida kawai rawan zaku yi ta yi. "kada ku tsaya domin ladanku yana sauka ne daidai da rawanku, maza a cigaba." Can ta ce musu. "Ya isa!" Tsayawa suka yi ta koma gaban gunkin Wagaduwada, ta kai gaisuwa tare da fashewa da kuka ta juya ta ce musu. "Maza mu fashe da kuka, amma kukan jarirai bata manya ba." Ta saka su suka yi ta rasa kuka, juyawa tayi ta ce. "Kaka Jami ya ba i hawaye maza kuyi kuka sosai har da hawaye, ina hango Uwargijiya tana kukan jarirai." Aikuwa suka yi ta rusa kukan jarirai,domin kuwa Uwargijiya tana kallonsu, can ta juya tare da cewa. "Ya isa haka. Tow uwar gijiya ta ce ku fashe da dariya, hahhahhahha!" Ta koma gaban gunkin tayi ta Kyalkyalkyalkya, tana rike cikinta tana dariya har da dungure da faduwa, ganin haka suma suka shiga dungure da faduwa.......... Ranakun posting. Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday In sha Allah, wannan pagen na Friday ne da ban karasa ba sai yau, don haka kada a ga babu Layla gobe ayi ta raba idanu. #Mai_Dambu [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu FREE BOOK _________________3 Dariya suke tare da rike ciki sai da suka yi me isarsu sannan, ta d'aga musu hannu tana had'e rai ta ce. "Ya isa haka." Ta zuba idanu tana kallonsu daya bayan daya, murmushi tayi tana fa in. "Kowa ya rufe Idanunshi domin tunawa da ranar da aka kawowa wagadu hari. Kuma duk abinda za aji na motsi ko giftawa kada a bude idanu don kada a fa a fushin abin Uwargijiya." Shiru suka yi, kafin maza suka rufe idanunsu. Fitowa Yu'isan da Ambi suka yi, tare da Tata suka shiga kwashe kayan mutane, babu wanda yayi yunkurin motsi domin kuwa tsoro yake kada fushin Uwargijiya ya fa a kanshi. Sai da suka yashe kowa, sannan ta gyara murya ta ce musu. "Kafin a bude idanu yana da kyau a yarda da cewa Uwargijiya tayi muku wani abin mamaki, wanda take son ku yarda ni yar aikenta ce. Kubude idanu a bisa umarnin Uwargijiyar." Bude idanu suka yi tare da zuba mata, "kafin nan ina son ku fara duba kayanku!" Ai kuwa suka mike da sauri. "Eh ai babu kayanmu," "mai gida sarkata!" "Mama yan kunne na." "Yaku Jama'an Wagaduwada! Ku tafi izuwa majami'a Uwargijiya ta mai da muku da kayanku kamar yadda ta dauka, jin jina ga Uwargijiya!" Ta mike ya fara rawa da tsalle-tsalle, wasu daga cikin mutanen suka shiga rawa da ihu, yayinda Malamin majami'a ya tura daya daga cikin dalibansa zuwa majami'a sai ga tulin kayansu har da wasu karin sulallar zinari. Da gudu suka dawo aka fadawa mutane, lallai fa Layla alkhairi ce kuma yar aiken Wagaduwada ce, ba makawa. Ai kuwa take mutane suka shiga zubewa a gabanta suna kwasar tabaraki. Wannan abin ya saka Tirsi confusing domin ta kasa yadda cewa Layla ce take wannan iyayin ta kuma kasa yarda ba ita ba ce, haka dai tayi ta kallon Layla din, so take ta gano wani abu amma ta kasa. Kallon Kaka Jami tayi cikin yanayinta, bayan ta sauko daga gaban gunkin Wagaduwada, tazo tana washe baki. "Kaka na kyauta?" Rike kunnenta tayi, tana fa in. "Sam Uwargijiya bata ji dadin abin da kika aikata ba, Habawa Layla wannan uban wahalar da kika bawa mutane da sunan ibada me haka yake nufi!" Tura baki tayi tana fa in. "Yar aiken Wagaduwada kika rikewa kunne fa." "Da ban tsinke kunnen ba." "Wannan cin amanar da me yayi kama Jamimah? Abin da kuka aikata laifi ne da ya sabawa tsarin bautar Uwargijiya." "Tirsi me kike nufi?" "Ina nufin kin saka Layla ta sab'awa abin Uwargijiya!" "Ni kuma da kaina?" "Eh mana, ke idan ba ke ba waye? Bayan da saninki ta aikata kuskure. Wanda haka hukunci ne babba!" "Tirsila kada ki kawo wani zance anan taya , Shugaba zata aikata haka?" "Malamin majami'a, abu na farko ka tambayi Jamimah sati biyu da suka wuce ta shiga kebabben fada ko bata shiga ba? Abu na biyu Jamimah ta bawa Layla sarkanta na kariya, yadda Layla ba zata kara musharaka da uwar gijiya ba, abin da na kasa fahimta shi ne me Jamimah take nufi da hana Layla fitowa a matsayin Uwargijiya." Zubawa Jamimah idanu kowa yayi, a hankali ta sauke ajiyar zuciya. "Sarkan kariya na saka mata ne domin jikinta ba zai iya daukar musharaka ba, idan kuma kuna son haka ya faru tow bari na nuna muku abin mamaki." Rike hannunta Sanaya tayi tare da cewa. "Jikin Layla babu karfin da zata iya daukar musharaka, idan kuma kika bari ta aikata haka rayuwarta ne zai zama abin farauta." Cike da takaici Tirsila ta buge hannun Sanaya. "Waye ya ce ki saka baki a zancen manya? Waye ya aike ki.?" "Kaka tirsi idan ma kika yi hakuri zaki samu yadda kike so, domin ita zanen addara ba a goge don a rubuce take." In Layla, juyawa tayi ta kalli Malamin majami'a ta ce mishi. "Malamin majami'a, kan ka zai yi kyau da kidan gangan sannan kayi min rawan tumbi ko na maciji!" Sai da ta fadi haka ta kalli mutanen gari ta ce. "Oho na saka su aikin wahala sun min rawa.." ta kwasa a guje, bin bayanta suka yi da idanun, Sanaya ta ce . "Kaka tirsi kalli saman kan Layla!" Wani bakin hayaki yake binta. "Da kin cire wancan hayakin ya shigeta ba iya mu ba, hatta ilahirin majami'an sai ya girgiza! Kaka Jamimah a san yadda za ayi a kare Layla daga bakar inuwa!" Murmushi kaka Jami tayi tana kallon Sanaya, sannan ta ce mata. "Tana dauke da sarkan kariya." Wannan abin ya bakanta ran Tirsila, duk yadda aka yi akwai wani boyayyen al'amarin da Sanaya ta sani take boye mata, kuma abin da bata gane ba shine yarinyar ko ta banka mata tsafi, sai tayi kamar ta biyu kwana biyu zata warware. Duk yadda ta kai da kintsa mata mugun nufi sai ta ga Sanaya ta watsar koda ta dauka. Kwafa tayi tare da barin wurin, ta nufi gidanta. Jamimah tana kallonsu, cikin takaici sallamar mutane tayi da suke kananun magana, akan abinda Layla tayi musu. Yo dama ya lafiyar kura. Fin Era estate.. Tun lokacin da yaji labarin zuwan Court lady, hankalin shi baya jikinshi. Kaf-kaf yake da cikin Aliyah. Wannan shine karo na uku tun bayan dawowansu Baihak Aliyah take samun matsala idan ta samu ciki zai zube, tun bayan haihuwar Nuriyya, ya fahimci haka, yanzu sati kusan biyu kenan. Babu abinda ya faru. *Witch woman* ya bayyana akan wayar shi, daidai shigowar Aliyah sanye da doguwar rigar barci me tsantsi light pink hannunta dauke da tiren green tea. Yana zaune a restchair, yana dan gaba da baya, ajiye tiren tayi ta bude kofin ta tsiyaya mishi tea din, ta bude kwalin brown sugar ta dauki kwaya daya ta jefa mishi, ta saka cokali tana juyawa a hankali. "Na gama" Wayar ce tayi ara, ya bude idanu ya kalli screen din, ya janye idanun shi akai yana me daukar kofin tea din. Yana kurban shanyin a hankali yana lumshe idanunshi. Aliyah tana durkushe a gabansa, warware rigar barcin tayi, gaban rigar ya bayyana wanda na cikin karamin riga ne iya Cibiyarta, shima pink din ne set na kayan baki aya, sai gajeren wando shima duk na kayan. Sau daya ya kalleta sannan ya mai da idanushi kan wayarshi. *First Love* ya gani a hankali ya kalli Aliyan, tare da mata alamar ta dauka. Da sauri ta dauka tare da sakawa a handfree. "Son kazo Mother tana son ganinka! Don Allah." "Yana jinki Ummimi!" "Thank you daughter! Don Allah ya zo kin ji!" Kashewa wayar tayi, ya gyara rike kofinshi yana sha tea din a nutse kamar me ciwon baki. Wayarshi ce ta kuma ara ya zubawa wayar idanu. A ranshi ya ja tsaki ta ce. "Me Hamidah take nufi da ni ne?" "My Lord na d'aga kiran ne!" D'aga mata kafada yayi . Yana kallon yadda take kome cikin sanyi sanyi da dari-dari. "Assalamu alaikum! Gran Ma!" "Ke bana ce ki daina amsa wayar Maina sai dai idan ni na kiraki ba? Baki aya ba ki da wata amfani sai na haihuwar Y'aya mata, har kin isa ki dauki kiran da nayiwa Jikana?" Maganar Queen Dowager ya mata ciwo, amma sai ta sauke kai tare da cewa. "afwa ba zan kuma ba." "Bashi wyaar kuma ki bamu wuri, domin zan yi magana da shi ne akan haihuwar da namiji. Tunda ke Allah bai miki gindin haihuwar maza ba. Sa....." Kashe wayar yayi ya cillata can gefe, ganin yadda Aliyah take zubda hawayen, ajiye kofin hannun shi yayi yana kallon yadda take shashekar kuka, abin yana tab'a ran shi amma kuma bai da yadda zai yi da ita, saboda shi dai bai ga dalilin damuwa tinda bata da ikon bawa kanta haihuwar Yara maza sai abin da Allah ya nufa. Cikin yanayinshi kamar kullum a yadda ta san shi mutum mara damuwa da kome, sosai ya ce mata. "Idan dai Dowager Hamidah ce, baki fara kuka ba." Ya fada yana mikewa ya nufi ban dakinshi cikin ruwan dumi ya shiga ya zauna, tare da rufe idanunshi. Bai cika cire kaya ba, don shi mutum ne mai matukar kunya, shi yasa sau daya yake kallon Aliyah idan ta biyo shi turaka, sannan yana da wata dabi'a shi baya bin mace, ita zata motsa mishi sha'awarshi ayi sha'ani, daga shi har ita farkon aurensu, an sha fama domin kuwa sai da aka yi da gaske yake
Chapter 7 · 0% Book details