← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 115

Sashe 114

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bikin saura sati guda, Maina suka samu matsala da Aliyyah wanda sai da manya suka shiga maganar, ita kan Layla rufe kanta tayi tana kuka, a daren ranar tayi mafarkin ga wani abu yazo yana hadiye daya daga cikin Yaran, farkawa tayi ta nufi dakin yan matan, nan ta samu sainah ce suke dambe da maciji. "kaiiiii!" Ta daka mishi tsawa, juyawa yayi a fusace ta dakatar da shi da hannunta cikin fushi ya juya ya sari Sainah a kafa, ta kwala ara, ita kuwa Layla daskrar dashi tayi tare da nufar Sainah. Rungumeta tayi tare da aukarta suka fito zuwa bangaren Maina tana kiran sunanshi. Cikin tashin hankali ya fito yana kallonsu.."Layla!" "Asibiti maciji ne!" Haka ya juya zuwa daki ya dauki key suka fita adaren. Dira Kalya tayi gaban Macijin ta shake shi sai da ya mutu sannan ta kwashe Yaran zuwa dakin Layla ta rufe tana me zaga gidan macizai.aka sake na bala'in fitar hankali, kiran dakarunsu tayi aka kwashe macizan. Aka fitar da su, har inda aka aiko su Tirsila ce a jikin katangar Masarautar tana ta fama.da siddabaru.kamata tayi ta saka aka daure ta aka saka ta a tsohon rijiya da macizan. A can asibitin kuwa duk iya arinsu akan Sainah sai da wanda ya basu ya amshi abinsa bayan ta bukaci ganin Babanta da Layla. Tayi ta rokonsu kada suyi fushi da Aliyyah, sannan ya cewa Uncle Ammar tana sonshi sosai. Su gayawa Mamanta tayi hakuri da Rayuwa. Tashin hankalin da Maina ya shiga ba iya fada, a daren ya kira Ammar ya gaya mishi bai yarda ba sai da ya zo asibitin yankar jiki yayi ya fadi sumamme, yana son Sainah ana fama da Ammar suka dawo gida kafin gari ya waye gidan ya cika fam har wannan lokacin Aliyyah tana dakinta taki budewa saboda abin da ya faru sai da Ubanta ya kirata ya mata ta'aziyar Sainah ta fito tana me fa in. "Karya ne wallahi bata mutu ba jiya ta shigo min daki fa!" Rike Hannunta Nuri darling tayi har parlour Layla ga gawar Yarta kwance wani irin kuka take tana fa in. "Wallahi ni na kashe ta, Ni ce na ce ta zab'a ko ni ko layla." Ta sake rushewa da kuka tana fa in. "Tace min Mum da akan na zabi dayanku gara na zabi mutuwa domin ita ce zata raba gardama a tsakaninku don Allah ya gani ina sonku baki aya iyayena ne ku, ko bayan na tafi ki rike Mami ita bata rike ki da kome ba, please Mum!" Kukan da take yi ba karamin karya zuciyar Layla yayi ba. Wacce kanta yake sunkuye sai kuka take a hankali, tana son Sainah yarinyar ta so ta from beginning. "Kin gama mata addu'a Layla?" Maina ya tambaye ta, "Eh saura Mum!" "No need!" Ya fita ya kira yan uwanshi suka dauki gawar aka fita da ita. A lokacin Aliyyah ta bi bayansu da gudu, ya juya tare da daka mata tsawa. "Kada ki saka fushina ya kwace, ki koma dakinki kada na kara ganin fuskarki!" Mikewa tai ta juya haka ta tafi dakinta ta zauna Kamar yadda ya umarce ta, Yaranta ma haushinta suke ji domin sun ji yadda yayi ta yiwa Sainah. Ashe ba aurenta zai dawo da ita ba mutuwarta zai dawo da ita baki aya suka ji sun tsani Mamansu, Ammar yana farkawa ya fito zuwa Baihak ana ganinshi aka.dakatar da sallah sai da yayi sallah asuba sannan ya fito aka yi jana'izar Sainah yayi kuka yayi kukan da ko mutuwar Mahaifinsa bai yi ba, har aka watsa bai bar makabarta ba, yana zaune gaban kabarinta. "Uncle Ammar ina sonka, ina son ganin fadarku da Papa yana nishadar da ni, kafin a samu abokai irinku sai an tona, zan so nayi nisan kwana domin na ga yadda zaku yi ta fada idan akace ga Yaranmu da kai ina son naga fuskar Papa!" Ta fada tana murmushi, hawaye ne ya zubo mishi. Dafa kafadarshi Maina yayi tare da riko hannunshi ya mike yana fa in. "Maina ina sonta!" "I know!" "Maina me yasa zata min haka?" "Haka Ubangiji ya nufa!" "Maina ka tuna kai ka bani ita?" "Yes na sani!" "Maina wallahi ina sonta!" Ya fada yana kuka, har motar su ya saka shi, shima Maina yana tuna yadda tayi ta binshi tana tambayar shi abin da ya bashi mamaki ya kore ta. "Papa Uncle Ammar bai da first love ba ne?" "Ke ban sani ba shi bai gaya miki namamajo bane shi." Wani bata rai tayi tana fa in"Papa!" "Ke shi fa bai da wata first love domin duk yan matan makaranta babu wacce bai so ba" "Papa ina jin haushin labarin nan!" "Sorry My love, kece first love dinsa domin akanki ta zama kwarkwar ya kuma zama shashsha, sannan ya zama maloho amma yana sonki domin bai tab'a min karya ba akanki ya fara soyayya!" Rungume shi tayi tana fa in. "Thank you Papa, kai ne mutumin da zaka bada shaidan shi har gaban Allah!" Hawaye ne ya zubo mishi ya tare. Yadda Ammar yake surutu sai ya baka tausayi. Mutumin da bai taba soyayya ba akan ta ya fara soyayya kuka yake har aka kaishi gida mahaifiyarshi ta yi kuka domin yasan yana son Sainan haka ma Matarshi da Yaranshi sun tausaya mishi domin sun san yana sonta. Matarshi ta samu Maina da Mamanshi. "Mama ina ga idan da hali kada a ad'aga bikin nan a barshi yadda aka tsara sai a bashi biyunta Sanah itama zata iya cike mishi gurbin Sainah!" "Allah ya miki albarka ya baki abinda kike nima duniya da lahira lallai kinyi kyan kai. Kuma kin nuna mace ce ke gaba da baya!" Da haka aka ajiye batun har aka yi kwana uku ruwa ake daura mishi duk wannan abin Maina yana tare da shi, "Malam ka tashi ka ware, kai namiji ne akwai abubuwa dayawa a gabanka ba Sainah ba ce a gabanka kadai matarka ma tana bukatar ka ita da Yara Please ya isa haka ." Ire-iren wa annan kalaman Maina yayi ta amfani da shi har ya same shi ta sauko amma ya sauya sosai. Ranar da aka cika kwana bakwai aka daura mishi auren Sanah tare da nadin Sarautar Maina. Har wannan ranar Maina bai saka Aliyyah a idanunshi ba, baki aya baya son ganinta amma haka ya daure ranar bakwai ya kai mata goron daurin auren ya gaya mata. Cikin shashekar kuka ta ce. "Ka kaiwa Layla ita ce tafi dacewa da zama Uwarsu ni na rasa wannan martaban, wallahi na yafe kome ka kai mata ita ce uwar da ta dace dasu." Har cikin ranta ta hakura da kome tarasa yard a take mata biyayya take jin maganarta me kuka zata yi. Haka ya fito bai kula ta ba, sai da aka saka wata uku domin mutuwar ta fita a jikinsu ayi sha'anin biki, tun bayan nadin sarautar Layla take rashin lafiya, sun dauka ciki ne da ita sai daga baya aka gane ba ciki bane, zaman da Aljanu suke yi ta yi a jikinta ne ya haifar mata da wani irin ciwo, haka tayi ya fama har, Lokacin bikin yazo a lokacin Zahra Bukar tazo bikin, sun tattauna sosai kafin ta bar garin. Sau dayawa Layla kallon mutuwa takewa kanta, sai da aka mata hanya tazo Nigeria ta ganin Dr Hayat Mijin Ummu Rooman (Na cikin jini yafi ruwa kauri) har da Maina suka zo wanda ya sauka a fadar sarkin Gombe. Satinsu uku kafin Layla ta samu lafiya, sosai kamar ba ita ba. Sannan Dr Hayat ya ce mata. "Kina da baiwa da ba zan iya rufe miki ba, don haka ki cigaba da azkar Allah zai iya rufe miki ko kuma ya bar miki kayanki shine janibinki!" Sannan ya samu Maina ya gaya mishi kome akanta, wanda murmushi Maina yayi ya ce mishi. "Allah yasaka da alkhairi, na sani." Kwana biyu a tsakanin suka dawo Baihak. Tunda suka dawo take magani da addu'a ga wani abin burgewa Layla akwai ibada. Bayan wata takwas, tana barci tunda tayi sallah azhar ta kwanta barci take sosai. Mafarki ne me dad'i da bata so a tashe ta ba, wai gata ga Sainah ga Mamanta, ana.ta hira sai murna take taga Sainah ta kara girma tayi kyau, har da cewa zata gayawa Papa yazo ya ganta. Murmushi tayi tana fa in. "Mami ki cewa Sanah kada tayi raki fa Allah yana tare da ita." "Mami!" Malik ya kwala mata kira a firgice ta farka tana kallonshi. Kamar zata yi kuka ta ce mishi. "Meye?" "Aunty Sanah bata da lafiya tana asibiti inji Mum Wai na gaya miki!" Shigowar Aliyyah parlour tana dariya. "Allah ya maka albarka Ubana, jeka wasanka." Ta fada Layla ta tura baki tana fa in. "Na rantse na kama ka sai akuyar cikinka yayi kuka. Fisabiilillahi mafarki nake da My Sainah Yaron nan da murya kamar babanin akuya ya tashe ni!" "Allah ya baki hakuri wai an kai auntynsu asibiti ne!" Mikewa tayi tana nufar dakinta tana me sauya kaya ta fito tana fa in " Ki kira Mijinki ki gaya mishi ba zama na wuce asibiti yau zanyi sabon miji!" Murmushi Aliyyah tayi wani lokacin kana raye amma sadaukarwa ba sai ka mutu ba, ta rungume mata Yara baki aya ta maida su nata kuma tana tsaye akan Yaran. A farkon auren Sanah da Ammar yarinyar bata ji dadi ba, Layla ta hana Maina magana ya zuba idanu. Haka tayi ta hawa da sauka har Allah ya daidaita zaman, yana sonta sosai amma yana gaya mata mace daya yazo ita ce Sainah Uwargida Sanah tana da mutunci sosai haka yasa Ammar bai yi wani rawan kai akan Sanah ba, sai ma gidan ya zama home of happiness. Zaman lafiya da kwanciyar hankali ana samu. Yanzu ma haihuwa ce ta kama su suka gayawa Ammar shi kuma ya tattara babban rigarshi ya wuce asibiti yo ko kallon Maina yayi ne balle ya samu damar mishi bayani. Baba Galadima daruyarsu yake yadda suke rikici kuma su dawo su shirya. Maina ya kira Aliyyah ya gaya mata domin baya son Layla ta je don yana zargin wannan karon yayi amfani da kujerana mulkinsa ya buga mata gundumar sarautarshi shine take yawan barci. Koda
Chapter 114 · 0% Book details