← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 115

Sashe 3

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shekaru uku ba'a yi ba, yanzu ya sake kirkiro zuwa wani wurin ita km ba zata ko ina ba,wallahi gara ya sake ta zata huta. Tana wannan tunanin barci ya auke ta, sai wurin Asuba ciwon mara ha e da tsinkewa jini ya tashe ta lokacin Maina ya tafi masallaci. Ita daya tayi ta birgima sai wurin 6:45 ya shigo lokacin da ya shigo ta suma. Farar Jallabiyar jikinshi da ya je sallah da ita bai ko cire ba, ya d'auketa a stairscase ya hadu da Amra da Kukun dinsu cikin yanayi mara dadi ya ce musu. "Ku saka idanu akan Yaran!" Ya wuce da ita, tun kafin ya fita Amra da Kukun sun isa bakin kofar suka bude mishi kofar, security din gida da kullum suke jiran ko ta kwana suka bude mishi motar da take gaban gidan, ya sakata ya shiga gaban, drivan ya figi motar a haukace, don ko Maina bai furta mishi kome ba, yasan kan aikinshi a zamanshi da su na tsawon shekaru. Koda suka isa asibitin, karban gaggawa aka musu kasancewar Asibitin na royal family ne, ba na kowa da kowa ba ne, kafin wani lokaci doctors biyu da nurse biyar ne akanta, kamar wasa sai da gari yayi haske har wurin 9:26am, mota Ammar Wazir da Salahudeen, "Maina wani b'arin ne?" Murmushi yayi me ciwo domin dai yana wani daki ne na daban, haka yasa suka shigo. "Na je security suke gaya min kana nan." Inji Ammar, shaf ya manta da wayarshi, hannu ya saka cikin aljuhun rigarshi ya ce. "Muje Palace!" "A haka?".inji Salahudeen. Ha e rai yayi tare da nufar hanyar waje, da sassarfa Ammar ya bi bayanshi. "Look Maina." Yadda yayi wani kicin-kicin da fuska yasa Ammar Wazir ya ce mishi. "Ina tare da duk abinda xaka zartas" "Ban gane ba" "Muje!" Ammar ya tura Salahudeen. "Kai ban fahimci kome ba" "Muje dai!" Ammar ya kara gaya mishi. "Na gaji!" "Kayi min shiru ka biyo ni" Maina ya daka mishi tsawa, yadda yayi tsawan yasa hatta likitoci da nurse da wasu marasa lafiya, kamewa domin kaf Baihak ba a tab'a jin yayi fa a ba, yana daga cikin manya mutane da suke da daraja Baihak kuma ake ganin girmansu, haka yasa baka jin ko motsin kowa domin tsawar da ya dakawa Salahudeen, shugaban rundunar sojojin tsaron fadar da kasar, yasa aka kashe tvs da takaita zirga-zirga, sannan wadanda suke tsaye suka zube kasa, tare da sunkuyar da kansu. Wannan tsawar tasa Salahudeen ji kamar zai mutu. Maina ya kunyata shi a gaban jama'a. Suna fita suka bude mishi mota, ya shiga tare da jingina kanshi a jikin motar, haka suka nufi Palace, duk da babu wanda ya kawo Maina zai shigo masarautar da karfe goma na safe haka, sun san karfe tara yake shiga sannan zai fita karfe tara da rabi, duk yawan maganar da zai yi yana bata minti ashirin ne zalla. Kai tsaye bangaren Queen Dowager Hamidah ya nufa, tana can tana shiri tasan sai ya gama yawo a cikin masarautar, tara da minti ashirin da daya ya shigo mata, idan yazo har ya gama zamaninshi babu maganar arziki sai gayawa juna magana masu zafi. Tana tsaye tana gyara zaman hularta na lu'ulu'u da aka mata tun daga kasar India, a jikin hular har da duwatsun lu'ulu'u mai daraja na khoinoor. A kofar apartment dinta Ammar ya tsaya, cikin gaggawa ya fita ko tsayawa bai yi ba, a kashe motar ya nufi cikin apartment inta bakinshi dauke da addu'a, kasancewar an san shi an kuma san waye shi, amma sun yi mamakin zuwan shi a karfe goma, ita kanta a can dakin adonta, mamakin me ya hana shi zuwa ko ya fasa zuwa ne. Shiga falon gidan yayi, bayi maza da mata sai zubewa suke ana gaishe su. Amma bai amsa ba Ammar ne ya samu zarafin amsawa, amma daga Salahudeen da Maina babu wanda ya iya amsawa, a babbar kofar da zasu shiga bahira ta tsaya tare da gaishe su. "Ku jira zata." Hankadeta Saraki yayi suka shige falon da zai had'a su da ita. Ba tare da b'ata lokaci ba suka shige akinta. Ta madubin ta hango su, gabanta ne ya fadi a rud'e ta juya amma ta dake. "Lafiya kuka shigo min har uwar daki?" Janyo kujeran da yake gaban madubinta Saraki yayi ya ajiye mishi, ai kuwa ya zauna tare da daura kafa daya akan daya. "Me kuke bukata a bangarena?" Bani wanda ya ce mata cikanki, kallonta Maina yake daga sama har kasa, irin kallon nan me tattare da bakinciki takaici, b'acin rai. Yadda take hango fushi da b'acin rai akan fuskar shi. Yasata niman duk wani matakin da zata dauka ta rasa, ta diririce kamar zata fasa ihu. "Ke Bahira kira min Mutallab, wannan ai rashin lafiya ne azo a saka ka a gaba sai kace maita." Ta shiga taburman kunya, ganin Maina ko gizau yasa ta soma ja fa baya, domin Saraki ya fita ya tawo da Bahiran ya wurgata gaban Queen Dowager Hamidah, sai jikinsu ya dauki rawa. Akwai wani irin kallon da idanun mutumin da baya magana yayi maka, kallo ne me tattare da zaka ci gidanku. Kallo ne da babu kamar shi domin kuwa sai ka fi sha'awar duka da zanewa sama da kallon, kasa kasa yake bin ta da kallon kamar ya rufe ta da duka. "Wai meye haka zaku saka ni gaba kamar mayya." Mikewa yayi cikin takun Kasaita, ya isa gabanta yana bin round na fuskarta da idanu. "Idan kina yi ne tow ki cigaba!" Ya fa a yana murmushi ganin yadda ta razana har sai da ta zube a kasa, ya bita kasar tare da dan tsugunawa. "Wannan shine last warning, a tsakaninmu." Yadda yayi maganar yana zaro golden eyes din shi, yasata ja da baya a zaune. "Kada ki daina ki cigaba, wannan tsoron da na gani a idanunki, is okay for me kada ki kara idan na dawo ba zan yi dogon shiru da wondering yadda xan yi dake ba." Daga haka ya mike, yes Maina ya gama cusa mata tsoron shi, idan akwai abin da ya rage ta shiga dakinta ta kashe kanta da bakinciki, tsananin tashin hankalin yadda ta tozartatta yafi kome mata ciwo, a hankali ya juya ya kalleta yadda take zufa. "Zan bar muku kasarku da aikin da kuka kakkaba min, ina da aikina kika sa aka dawo dani, be careful with me." Ta fahimci sako yake bata, amma kuma Allah ya isa tsakaninta da Maina, domin yadda ya fusata bata san ta sake fitsari ba, sai bayan fitarsu wani azabeben kunya ya rufeta, duk cikin jikokinta babu dan iska kamar Maina, babu lalatace kamar shi. "Allah ya isa min!" Ta fa a tare da wurgi da crown dinta, tana me fasa ihu. "Wayyo Allah na!" Ta fa a da mugun karfi, cikin fushi da b'acin rai ta cewa Bahira. "Ki ra min Mutallab right now!" Da gudu Bahira t fita, ta nufi can Mansion na King AbdulMutallab. Ganin Bahira ta fita ta fashe da kuka, sosai domin babu wanda ya tab'a bata tsoro haka sai Maina, ba iya tsoro ba, ya gigita mata lissafinta tunda take bata tab'a ganin guguwar b'rai haka ba, don haka take kuka kamar ranta zai fita. Kafin su iso ta mike ta gyara jikinshi, abin kunya ne a ce Maina ya mata haka, sannan abin mamaki ne ya biyo ta har turakanta ya muzanta mata, kawai ta fashe da kuka kuka wiwi. Sai da ta gyara jikinta har ta sauya kayanta. A can kuwa ganin Bahira babbar hadimar Queen Hamidah yasa aka bata kofar shiga, daidai King AbdulMutallab zai fita fada, ta zube a gabanshi tana fa in. "Allah ya kara maka lafiya, Allah ya kara maka nisan kwana, Allah ya baka ikon aukar Baihak a bisa kafadarka, Queen tana cikin tashin hankali." "Long live king AbdulMutallab." Shiru yayi kafin ya kalli security inshi. "Zan je ganin Umma." "Allah ya baka nasara, karfe sha daya ne ganawa da bakin da suke son bude kamfanin nan kum...." "Ita mahaifiyata ce,idan ta saka min albarka zan ga daidai su kuma niman duniya ta ce, idan na samu matsala juya min baya zasu yi." Daga haka ya karkatar akalar tafiyarshi zuwa wurin Queen Hamidah, tana zaune a inda Bahira ta barta, sai kaya da ta sauya. "Umma lafiya?" Watsa mishi kallon banza tayi, ta wuce. "Umma wani abu aka miki!" "My Lord, Maina da Saraki da Ammar suka zo suka ci mutuncinta." "Maina!" Ya fa a da karfi, domin bai kawo a ranshi zai zo cikin masarautar ba, ya dauke shi shekara daya rabon da ya saka Maina a cikin idanun shi amma duk wani cigaba na nahiyar da masarautar Maina ne akan shi. "Me ya faru!" Cikin tsoron munafunci, tayi kasa da kai kukan Queen Hamidah ya ji, "kada ki gaya mishi yadda Maina ya tozarta ni, shi din d'ana ne bana son ya fusata ka je kawai, Allah na gode da ba iya Maina nake dasu a masarautar nan, akwai Haisam da Braham. Amma na cire Maina da Saraki a cikin jikokina,ba zasu kashe ni ba da bakinciki ba." "Umma don Allah kiyi hakuri, wallahi ban san kome ba,bari na samu Khamilah." Ya fita a fusace, bai tsaya wani tunani ba. Har ya isa part din Princess Khamilah da take sallah walaha, ya shiga har cikin akinta. Tana ganin shi tayi sallama ko dogon addu'a bata yi ba, cikin tsannanin biyayya ta mike. "Welcome my Malik, me za aka kawo maka!." "Da saninki Yaranki suka ci mutuncin Mahaifiyata?" A rud'e ta ce mishi. "Wa kenan? Su waye?" "Maina da Saraki!" Gabanta ne yayi mummunar faduwa, ta zube akan gwiwarta. "Lallai sun yi kuskure, wallahi ban san sun zo cikin Baihak ba,na rantse da Allah ban sani ba." "Ki tashi muje ki bawa mahaifiyata hakuri sannan ki kira shi ya bata hakuri ko na zare shi cikin Yarana, Maina ya masifar rena ni haka zai shigo masarautar lokacin da ya gadama ya fita lokacin da yaso me Maina ya mai dani? Maina bai dauke ni a matsayin Uba ba, ban sani ba ko mun raba gonar..." "Mutallab;" ta kira sunanshi da karfi, tana girgiza kai. "Kai sheda ne, ban fito a gidan da tarbiyya
Chapter 3 · 0% Book details