← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 115

Sashe 39

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*Duffur black humra*
*sandal humra*
*white humra*
*body milk*
*misik humra*
*soulmateng humra*
*creem kulecca*
*basilin kulecca*
*makhmariyya kulecca*
*turaran wunana*
*farce*
*Hawi*
*halud*
*sandal oud*
*oud flaxs*
*Sandal flaxs*
*oud kajiji*
*Gabgab*
*sandal coconut*
*oud Al'arab*
*sandal balls*
*kindi kayi*
*and more.....*
*gamasu siyan daya ko sari kunemeni ta Wannan lambar*
09018535968
*muna maraba dakowa saikinzo*
______________________
Tunda suka shigar da Layla da Nuri dakin kula da majinyata, yarinyar nan taki yarda ta rabu da Layla, shafa bayanta take tana bata hakuri, tare da hure karfin sihirin take yarinyar ta shiga sauke ajiyar zuciya, sannan Layla ta samu ta raba ta da jikinta. Aka shiga duba yarinyar da jikinta, ita kan fitowa tayi tana kara jin b'acin ranta yana bun
asa shirinta na daukar fansa daban, wannan aikin daban. Kurawa kasa idanu tayi tana jin wani sabon takaici. Su yara kamar waliyya suke ba a cutar dasu, domin bata manta shekarar da aka yi wani fari ruwan kogi ya kafe, babu al'amar za a samu ruwa, haka yasa manoma shi halin ni y'asu, Kaka Jami da Malaman Majami'a suka tafi taro bayan an hada kan kowa, aka kira Yara har da Layla a cikinsu. Malaman Majami'a suka tambayi kaka Jami da cewa. "Shugaba meye hikimar hada yara a rokon Uwargijiya ta bamu ruwa?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Su din kamar waliyayye ne, kusancinsu ga Uwargijiya zata sssauta mana ta bamu ruwa, kaunar da jinkanta zai saka ta tausayawa yaran nan, su din kamar abu ne mai daraja da ake boyewa don kada a cutar da su, Yara abin kyautatawa ne." Jin haka yasa duk suka amince aka tattaro su Layla sai dai ita dake ba zuwa rokon ruwan ba ne a gabanta, wani garin Ciyawa me yauki ta dibo ta kwab'a, sai da suka yi ta rokon ruwan ta sulalle zuwa kofar malamin majami'a ta watsa mishi. Sannan ta koma wurin rokon ruwan ai kuwa can sai ga ruwa da karfi aka shiga yayyafi da gudu Malamin majami'a ya fito tare da wasu ba bin bayanshi, yana zuwa ya taka yaukin nan tuni ya fara gangarawa daga matakalar majami'an, sai da ya diro gabansu. Kunshe dariya tayi ita daman damuwarta taga yadda zai gunguro da katon ciki kamar na kwado, budar bakinta ta ce mishi. "Lallai Malamin majami'a zaka yi albarka irin wannan godiya ga Uwargijiya." Duk da ya bugu dai gashi ya cigaba da juyi a cikin ruwan sama, ai kuwa ta shiga rera waka da muryanta me zak'i. _Ruwa ruwa caccaya! Malamin majami'a caccaya! Kayi juyi caccaya!_ yara suna taya ta, kai karshe Layla da wulakanci sai ta tasa Malamin Majami'a taka rawa, ai kuwa daga karshe aka kora yara zuwa gida, Layla kan kin wucewa tayi ta bi Malamin Majami'a zuwa
akinsu ana duba buguwar da yayi. "Yarinya nan an yi munafuka, Ravi na bugu fa amma kaga yadda munafukar yarinyar nan ta mai dani abin wasa a gaban jama'a" kawai ya fashe da kuka. Ravi yana bashi hakuri lekowa tayi ta tagar ta ce mishi. "La Malam kuka kake?" Fashewa yayi da dariya yana fa
in. "Yar albarka ina xan yi kuka bayan na gama, yiwa Uwargijiya rawa." "Atow na ga dai kai babba da kai kayi kuka ai akwai matsala tow ni dai na wuce!" Ta fita da gudu tana dariya, tana barin dakin ta fashe da kuka wiwi, Ravi yana bashi hakuri.... Hawaye ne ya zubo mata, ta koma gefen Bahiyyah tana shashekar kuka. "Kukan ya isa haka!" Kuma wani abu
aya kukan da take yi ba kukan kome ba ne, tuna wasu abubuwan da suka wuce na farinciki a rayuwarta ne, da gatarta da kome ita kanta renonta ake kamar jaririya, a hankali ta sulale ta koma can wajen asibitin, ta samu kasar bishiya ta zauna, idan ta tuna da Abokanta Tata Yu'isan Ambi, wani irin kuka take jin yana zuwa mata. Ta rasa kowa nata bata da uwa bata da uba, babu dangin iya bata da abokai. Yana tsaye ciki da mamaki bayan abin da tayi yanzu ta koma waje cikin sanyi tana kuka, haka kawai yaje akwai abin da yake damunta don ya lura bata rena abin kuka kuma bata rena damuwa zata ware kanta tayi ta kuka. Wannan shine karo na biyu da yake ganinta tana kuka haka. Daga nesa Prince Auta ya hango ta cikin sanyi, da sauri ya nufeta. "Layla!" D'ago kai tayi tana share hawayen da yake zuba mata. "Ya isa jikin Nuri darling da sauki tashi haka kika fito babu sweater!" Ya fa
a yana kallon yadda take goge fuskarta. "Mr gashi ance a bata!" Mika mata jakar takarda aka yi ta amsa tana son tambaya amma ta kasa, amsar jakar yayi ya ciro mata rigar sanyin har gwiwarta, sai hula da yar mayafin da ake nadewa a wuya, domin Scotland tana cikin kasashen da basu rabuwa da sanyi, mika mata yayi yana kallonta kasa kasa. "Nagode!" "Bani na saya miki ba." Kallon shi tayi da manyan idanunta tana son tambayarshi wayarshi tayi
ara, ya mika mata safar hannu ta saka sannan ta ga ya juya bin shi tayi. Tana shiga rike da mayafin, Bahiyyah ta amsa ta daura mata. "Kinyi kyau!" Ta fada tana kallon yadda Layla taki yarda su hada idanu. "Hala na zama in-law dinki ce ko?" Zuwansu Ummimi da Aliyyah yasa suke ta jajjantawa juna abin da ya faru. "Ina ita Nuriyyar?"Inji Ummimi "Tana ciki!" Layla ta nuna mata dakin, kallon Layla Aliyah tayi ta ce mata. "Kina ina haka ya faru?" Muryanta na rawa ta ce mata. "Nur din ce tace na duba mata!" "Fisabilillahi sai ki barta ita
aya? Me yasa baki tafi da ita ba? Yanzu idan ta mutu me zaki ce min? Saboda na yarda da ke da kuma yadda take kaunarki aka barki fa ban ga amfanin zamanki ba." Zubewa tayi a kasa tana fa
in.. "Na cancanci mutuwa, ranki shi da
e. Tabbas sakaci na ya janyo haka tuba nake ayi min hukuncin da ya dace da ni!" "Tashi!" Suka ji muryan shi a bayansu. Sannan ya nufi Aliyyah ya riko hannunta, suka fita mota ya nuna mata ta shiga. Shima ya shiga, shiru yayi tare da kifa kanshi a jikin steering motar. Kawai tashin motar yayi suka nufi gida, babu jima ya ajiyeta. "At least kin ji kunyar Ummimi!" Daga haka ya dauke kai, cikin masifa ta ce. "Taya zan ji kunyarta? Kashe min Y'a za ayi kace kada nayi maganar? Anya kuwa Papan twins akwai adalci a ranka?" Idan ya bude baki maganar da zai fito bakinshi mara da
i ne da zafi, "fita!" Ya fa
a mata, ba musu ta fita tana mita, kuma wallahi babu wanda ya isa ya hanata masifa. Karya ne ma a ce Ayrah ta rankwasheta sai dai ita ce zata yi rankwashin ba zata yi kafara ba Layla ce tunda ga Ayrah bata san yadda kanta yake ba. Baki
aya sai Layla ta rasa sukuni, haka yasa take ganin laifinta ne, har yamma sannan su ka dawo gida Nuriyya tana manne da ita,, suna shiga cikin gidan Aliyyah tana amsar Yarta, ai kuwa Nur ta fashe da kuka tana fa
in. "Ni wurin Didi zan tafi!" Bahiyyah da takaici ya isheta ta riko hannun suka wuce
akinsu. Ita bata son abin rashin mutunci da rashin fahimta, ai tasan yadda Ayra take kishi da ita Aliyyah amma take wani blaming Layla da babu ruwanta ba don tana son Layla ba da ta kira Sultanah Dilshah Khatoon tazo ta dauki yar mutane.
A can Asibiti Ummimi ce kan Ayrah wacce har lokacin bata farka ba, dole suka kira Malik aka gaya mishi, a can kuwa Baihak. Cin duniyarsu sa tsinke Queen Hamidah take, amma har yau Falwa yana gaya mata, lallai a nimo Layla domin mulkin Baihak zai ji ma a hannun Malik, don haka akayi ta nimanta, ba dare ba rana. A cikin wannan yanayin aka kira Malik da ya tare da sabuwar Kwarkwaran shi Sohana, wacce ta maye gurbin Lady Ayrah. Aka gaya masa halin da take ciki, bai wani damu can ba ya tafi ya gayawa Queen Hamidah, sai da tayi tsamma kafin ta ce mishi. "Lokacin da kake da shi yana da muhimmanci, bari ni na tafi naga halin da take ciki." Gyada kai yayi yana fa
in. "Shi kenan!" Haka kuwa aka yi a tsakanin kwanaki uku ta bar Baihak. Lokacin da ta isa Auta ya daukota zuwa gidan Maina. Ba karamin kulawa ta samu a wurin Aliyyah da take ganin kamar dole ce ta bata kulawar. Sai dai jin kukan Nuri yasata kallon Aliyyah. "Me ya same ta?" "Ranki shi da
e, wai zata wurin nanny ce ni kuma ban yarda da Nannyn ba ce." Wani irin dadi Queen Hamidah taji ta samu hanyar da zata lakume Banafsha. "ina Nannyn take?" Cikin sanyin jiki ta fita tare da kiran Layla. Dama tasan da zuwan Queen Hamidah Sainah ta gaya mata, wani irin tsana da kiyyayar Hamida ta isa gabanta. "Gani ranki shi da
e." "Ita ce!" "Eh!" "Tashi ki bani wuri, sannan ki turo Nur
in!" "An gama!" Ta fita can sai ga Nur da Sanah, tana ganin Queen Hamidah ta zube a kasa. "Welcome My Queen Mother of great kingdom Baihak." Wani
asaitacciyar murmushi Hamida take yi tana gyada kai da ace Sanah namiji ne da ita ce makamin da zata yi amfani da shi wurin janyo Maina cikinsu. "Allah ya miki albarka!" Nuri na ganin Layla ta fa
a jikinta. "Didina!" Ta fa
a tana kara shiga jikinta "i miss You!" Ta fa
a tana kuka. Fincikota Sanah tayi yarinyar ta fashe da kuka. "My Princess kyaleta kinji!" Inji Queen Hamidah tana kallon yadda Layla take kara rungumar Nur
in. "My princess ki tafi daki akwai wani box ki dauka muku naku ne!" "Thank you My Queen!" Ta shige dakin can ya fito da akwatin tana ja da kyar. "Nanny ko? Tayata daukar akwatin" dama hankalinta a tashe yake, amma jin zata tayata ta mike tare da Nur suka fita tana rike da akwatin, da take jin motsin abu a cikinshi, har dakinsu fakar idanu Sanah tayi ta yiwa akwatin aiki yadda duk abin da za ayi ba zai bude ba. Sannan ta koma wurin Hamidah. "Ya sunanki!" "Layla!" Da sauri Hamidah ta kalleta. Sai kuma ta wayance ta ce mata. "Daga ina kike?" "Daga wurin Sultanah Dilshah Khatoon." "Ai tare da Hajja kike?" "Eh!" "Me kike yi anan?" "Ina kula da Yara ne!" "Amma kin san Mamarsu bata son kulawar da kike basu?" Kasa tayi tana fa
in"rashin fahimta ne amma nasan zata sauko!" "Idan kin amince zaki min aiki. Kanta a sunkuye ta ce mata. "Ranki shi da
e, meye amfanina idan ban yi muku aiki ba?" "Good girl, je ki zan nime miki sannan ki cigaba da kula da Nur din zan mata magana!" Haka kuwa ta bar Hamidah da farincikinta zata janyo maina Baihak, sannan zata yi ta tilawa Layla dukiya domin tayi ta mata aiki, sannan zata saka a karo wata baiwar da zasu yi biyu yadda kome zai tafi mata smootly. Sai yamma can suka tafi asibitin da Aliyya da ta kai Abinci, har kawo lokacin Ayrah bata san inda take ba, kudi ake kashewa akanta ga hannun sai kara hawa yake, har zuwa kafadarta ya cika bam. Abin da ya tsorata kowa kenan, Maina haka kawai yaje jin matsalar Ayrah Layla ce maganinsa, amma taya zai mata magana? Don haka a cikin kwanaki biyar da faruwan al'amarin aka fara maganar za a yanke hannu, don haka ya saka auta ya kwaso su, aka yi ta maganar idan bata farka ba, yanke hannun za ayi idan ta farka. Zazzare idanu take tana kallon yadda Ayrah take kwance har kanta suka isa yana halkance da ita ta shafa hannun da sauri. *Ashe ba Muguwa ba ce* juyawa tayi taga babu me kallonta, ita kuma tana niman waye yayi zancen zuci har taji, ganin babu wanda ya lura da ita yasa ta koma gefe tana zare idanu. Motsin da Ayrah ta fara yasa Maina kara tabbatar da zarginsa ita ce ta kwantar da Ayrah amma me yasa bata iya cutar da kowa sai Ayrah wannan shine karo na biyu, amma kuma a firgice Ayrah ta farka tana ihu. "Ke tafi can, sakarya randar waje wacce aka ajiye ta duk wankar tsarki ba don sha ba.........Mu hadu next episode
[9/2, 9:29
AM]
Hafs: *_
LAST EMPRESS
Historical fiction hot romance story
_Mai_Dambu_
Wattpad:Mai_Dambu
Arewabooks:Mai_Dambu41
Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu
MASU BU
ATA DAGA FARKO DON ALLAH SU SHIGA LINK ABUBUWA SUNA MIN YAWA GA CIWON IDO GASKIYA BA ZAN IYA BADAWA DAGA FARKO BA TA PRIVET KO GROUP LINK CHANNEL GASHI NAN IDAN KA SHIGA ZAKA SAMU DAGA FARKO PLEASE joining Last Empress
https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s
_________________
*MAN'S COLLECTION*
*gidan Kamshi da gyaran jiki da maganin mata*
*Ina uwargida da amarya da masu shirin gyara,shunkuna neman inda zaki samu ingantattun turaruka masu kama jiki da gida Wanda tundaga get za'a fara jiyo kamshin gidanki?*
*shinkuna neman inda kaku samu magunguna ingantattu sha yanzu magani yanzu*?
*Maza kugarzayo MAN'S COLLECTION* *tazomuku da turaruka masu tashin kan megida da kamshinsu munada turaruka kamar haka*
Chapter 39 · 0% Book details