← Book details Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 115

Sashe 2

Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wagaduwada idan na sace kayan k'awan uwar gijiya. Tow uwar gijiya ta tashi da kanta tayi bayani." Sake buga sandar tsafinta tayi zai da Layla ta zube akan gwiwarta. Tana kallon Malamin majami'a ta ce mishi. "Da na rufa maka asiri shine ni, zaka tonawa ina cewa duk madaran da ake kaiwa don wanke Uwargijiya kai ne kake sayarwa." "Yaushe zaki daina saka mutane magana? Ke fa mai tsarki ce domin karramarki babba ce." Inji tsuhuwa Jamimah. Zare idanu take tana zubura baki, ta ce mata. "Idan Ni mai tsarki ce, tow muje gaban Uwar gijiya ta fa a da bakinta ban yi mata sata ba.!" Ta fada tana kunkuni. "Ranki shi da e, ba yau Layla take sace mana yan abubuwan ba, ba iya gwala-gwalai ba hatta." Taren numfashinsa tayi bata bari ya kai aya ba, ta ce mishi. "Malamin majami'a, kasan na kama maka sau biyu kana sayar da tukwanon madaran uwar gijiya ga Haris?" Ta fada tana kallon yadda kunya ta kama shi cikin diriricewa, tow Ina tsoron uwar gijiya ta la'anance ki na tafi." Ya juya zai tafi ta sha gabanshi tana fadin muje gaban Uwar gijiyar ta gaya min ni ne na ke zuwa mata sata." Duk yadda yaso kaucewa ya kasa sharrin Layla tafi ta shashi, wato macijiyar da take kare Uwar gijiya. "Gaskiya muje gaban Uwargijiya a fadi gaskiya." Inji wani dattijon. Ai kuwa wurin ya dauki aje aje kawai. Kasa magana Kaka Jami tayi domin bawa mutanenta muhimmanci bata iya saka baki idan suka ce ayi abu,nata na shugaba ce. Don haka ta ce musu. "Malamin majami'a aje kawai." Ta fadi haka ne don bawa kowa damar kare kanshi, sauran mutanen da Layla ta musu sane ta ce musu. " Za a biyanku hakkinku, ku kula har yau Layla yarinya ce da kuruciya akanta, ina fatan zaku yafe mata." "Mun yafe mata!" Juyawa tayi wurin wata dattijuwa Tirsi, ita ce hannun damar Kaka Jami, sai dai kallonta Kaka Jami tayi tana fa in. "Tirsi ki sallame su." "Tow." Ta fa a a shake, asalin wannan abin yana mata ciwo, shigowar Layla rayuwar Jami yasa ta mike kafa tana mata bauta, amadadin ita da zuri'ata ya dace Jami ta kula dasu, a'a sai ta koma kula da jikar dan uwanta da suka ci amanar Uwargijiya. Tirsi tana da jikar sa'ar Layla ce kai da kai, sannan asalima ita ce ta dace da sunan Layla. Don darajar sunan amma aka sawa wancan bakar addaran. Cikin gida Kaka Jami ta wuce don ba zata iya zuwa majami'a ba, kuma duk abinda xai faru za a kawo mata labarin har gida. A majami'an kuwa tsaye Layla tayi a gaban Uwargijiya, tana zare idanu kai zaka rantse da Allah wani abu take yi nan kuwa rufe idanu tayi tana kallon gunkin Wagaduwada ta ce mata. "Uwargijiya Wada nasan nayi miki barna amma kuma a matsayinki na gumki me zaki yi da kayan kwalliya? Kawai al'ummar da suke bauta miki fa na bawa, don Allah zancen gaskiya kada ki bani kunya ki bawa malamin majami'a kunya!" Ta d'aga gira daya, tana kallon Uwargijiya da take zaune juyawa tayi ta ce musu."yawwa idan har ina sace kayan Uwargijiya Wada, Shashi macijiyar Uwargijiya zata farmake ni idan kuma sharri aka min akan idanunku Shashi macijiyar Uwargijiya zata farmake ko waye da yake min sharri." "Laaaaaa!"mutanen cikin Majami'an suka fada baki aya, sakamakon hasken da ya haskaka ilahirin majami'an, juyawa tayi ta ga hasken har bata iya ganin gabanta. "Kin roki Uwargijiya bayan kin san duk abinda kika bukata zata miki, don haka babu wanda ya isa kada ke a gaban Uwargijiya." Hasken ne ya dauke kamar anyi ruwan sama an auke cak. Sai atuwar macijiyar Uwargijiya da ta fasa kai a gefenta. A hankali take ganin mutane bibiyu kafin ta zube a wurin, bata kuma sanin wanda yake kanta ba. A hankali take bude idanunta, ganinta a cikin turakar Kaka Jami yasa ta zare idanu, rabonta da dakin ai ta jima bata shigo ba. Kasancewar Kaka Jami ta juya baya ne, a hankali ta sauka a gadon, ta fara sand'a kamar mage, zata fita ta ce mata. "yau ya zama karo na karshe da zaki yi magana da Uwargijiya kin ji ko baki ji ba." "Kaka amma ai." "Na gaya miki ai!" Shiru tayi tare da ja da baya, kaka bata tab'a tsawa ba. Yau tayi mata don haka cikin fushi ta fice daga gidan lokacin yamma tayi, ta nufi can dutsen wagadu, tana mita. A can saman dutsen akwai inda ruwa yake zuba, har yana shigowa gari. Yan mata sukan tafi wurin diban ruwa ko wanka, ita kuma a lokacin take jin ta juya siffar maza taje niman tsokana. Don haka ta gama mitarta kawai ta wuce wurin dutsen, kwashe kayan yan mata tayi ta haura saman bishiya, ta zauna sai da ta ga garin ya fara duhu ta leka tana gyaran murya. "Yawwa kuzo kuga mata zigidir!" Ai kuwa mata suka fara ihu tare da boye jikinsu. Murmushi tayi ta musu tana fa in. "Yau na sha kallo" "Wayyo namiji ne! Ka bamu kayan mu" "Bani badawa! Sai kun min rawa babu kid'a." Aikuwa kuwa suka shiga rawa, suna juyi tana dariya. "Gaskiya wannan rawan bai min ba." Ta fa a haka suka yi ta rawan tana fa in a sauya mata, har sai da garin yayi duhu ta cilla musu kayansu, ta bar wurin tana ihu da dariya, koda ta iso gidansu gari yayi duhu, a dan gaban gidansu akwai wasu masoya kullum dare sai sun zo hiran soyayyarsu. Ita Layla gani take kamar gulmarta suke, don haka da tazo wucewa ta tsaya tana kallonsu, kwafa tayi tana fa in. "Munafukai, Uwargijiya ta tsine muku daidai gwargwado." Ta wuce, ita ta san me zata musu. Don Allah ta shige cikin gidansu. Tana shiga ta samu Sanaya, tana cin abincin dare. "Saniya!" Ta fa a tana wucewa. "Eh ai gara saniya bata kai jaka jakunta ba" dariya tayi tana tafiya. "Ai shi jaki kullum aiki yake badawa, kin tab'a jin an bawa Jaki aiki? Aikin shi daya ne kuma idan yayi kowa sai ya ji a jikinshi." "Mahaukaciya!" "Ke da kika kula ni kin fini hauka!" Ta wuce ta dauko abincinta, sai da ta zauna ta fara ci Tirsi ta fito dakin Jamimah, tana kallonsu. Idanunta ne ya kai kan Layla da take kallon abincin kamar tana son gano wani abu. "Ke meye haka?" Inji Kaka Jami da ta fito, "Kaka dama bayan wannan duniyar tamu akwai wata duniya ce? Kin ga har da wani abu me motsi!" Ta nuna mata cikin kwanon abincin." Lekawa tayi tayi shiru, "babu wata duniya da na gani." Ta fa a tare da komawa akinta, bin ta akinta Tirsi tayi tana fa in. "Ganawarta da Wada ko?" Inji Tirsi. "Hmm!" Inji Kaka Jami. "Me zamu yi yanzu?" "Rufe mata kai a cire rauhaniyar da take tare da ita, wannan shine adalci." Daga Tirsi har Jami kwana suka yi suna aiki akan Layla, kuma a daren suka da ce aka rufe mata kanta da rauhaniyar aka barta fanko. Da safe ta tashi tas babu kome, a kanta ta manta da kome sai masoyan jiya da abin da ya faru na al awarin da tayi, don haka tana karyawa zata fita aka hanata fita, kamar tayi hauka vata samu fita da sai can yamma likis, shima da amincewar ba zata kara zuwa majami'a ta'adi ba. Abokanta Tata, Yu'isan, Ambi,.suka tafi daji suka dibo arara, suka bi inda masoya suke zaman nan suka watsa, sannan suka watse ita kan komawa kofar gidan tayi ta zauna, tana kallon abinda zai faru. Can kuwa masoya suka zo aka fara soyayya kafin kace me, sun fara sosa. "Susa min nan, abar kaunata." "Susa min nan masoyana!" Dariya take tana fa in. "Soyayya min masoyata, Susa min nan abar kaunata,". Ai take masoya kowa ya kama gabanshi, a madadin ta koma cikin gidan, a'a sai cewa tayi. "bari na je na shafa naji yadda kowa yake ji." Nufar wurin tayi ta saka hannunta, ai tuni kamar iska ya mamaye mata jiki tana ihu tana yage kayan jikinta, ta isa cikin gidan tayi dungure ya kai sau uku, kafin ta shiga. "Wayyo Kaka Jami ki sosa min, wayyo ni na shiga uku na lalace, kaikayi ne ku cire min shi a jikina.... #Hothotlove #Wagaduwa #Baihak #Teenage #Marriage #Betray #Layla #Sanaya #Maina [9/2, 9:29 AM] Hafs: *_ LAST EMPRESS Historical fiction hot romance story _Mai_Dambu_ Wattpad:Mai_Dambu Arewabooks:Mai_Dambu41 Facebook: Ramlat Manga Mai_Dambu The journey of a miles is begins with a single step..... https://whatsapp.com/channel/0029VadYczJLY6d8BbzsbY0s *MASU NIMA DAGA FARKO DON ALLAH GA LINK NAN SU SHIGA ZASU SAMU* ______________4 Sosai dare ya raba, yayinda barci barawo yayi gaba da kowa. A bangaren Maina wani irin wahalallen barci yake me cike da tashin hankalin, domin kuwa kamar a mafarki kamar a zahiri yake ganin wani irin halitta yana kaiwa Aliyah hari, amma bai same ta ba, shi kuma yana rike da wani irin bulala da zaran abin ya kawo mata cafka zai zuba mishi duka. Kad'a fukafiko abin yayi tare da girgiza Maina ya zube can, tsalle abin yayi tare da dirka akan cikin Aliyah. Ihun da tayi yasa duk suka farka, sai a lokacin ya shiga karanto Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, yana yi yana nanatawa, d'ago ta yayi yana kallon fuskarta da take zufa kamar ana gasata. "Aliyah?" Ya kira sunanta tare da d'agota, bude idanu tayi tana kallonshi. "Papan twins lafiya?" Ta fa a tana kallonshi. Ganin babu wani abu a tare da ita yasa shi sauke ajiyar zuciya, ya zare ta a jikinshi yana tab'e baki. Kamar bai damu ba nan kuwa damuwa ce cikin ranshi. "Zuwa gobe ku tattara, Haisam zai kai wuce daku Scotland." "But why?" Juyawa yayi cikin duhu, ya zuba mata idanu. So yake ya tambayeta yaushe ta fara mishi musu, amma sai ya cije lips inshi ya mike tare da shiga ban daki, yayi alola sannan ya dawo ya kwanta a dogon kujeran dakin, ya tsani musu da taurin kai, shi yasa basa shiri da Bahi domin ta cika taurin kai. Juya mata baya yayi abin shi. Kwanciya tayi tana ji a ranta ba zata bar garin nan ba, ta gaji da yawo da ita da Maina yake, ko
Chapter 2 · 0% Book details