Sashe 93
Last Empress Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zan bika!" Tayi wani fari da idanu. Baki aya ya rasa me zai ce mata. "Tow akwai maza a wurin ne!" Yayi shiru yana kallonta kafin ya cigaba da cewa. "Zasu ta kallonki Please ki zauna da Bahiyya!" "Shi kenan ai shi kenan, tunda ba zaka da ni ba. Zan zauna to. Kuma idan kayi tunani na zan biyoka." Ta fada tana murmushi. Waye idanun yayi tare da fa in. "Me yasa ba zaki fahimce ni ba?" "Tow shi kenan ka dawo lafiya Babynbaby!" Kura mata idanu yayi kome nata na musamman ne. "Yanzu zan dawo!" Ya juya zai tafi ta ce mishi. "Sultan kada kayi tunani na fa! Domin da gasken gaske xan biyoka!" Jin haka ya sa shi fita da sauri ya nufi bangaren Queen Hamidah yana fatan kada ya tunota ta fado ranshi. Yasan matukar ta je azabtar da Hamida zata yi, don haka ya isa bangaren yana sauke ajiyar zuciya. Ya samu an zagaye ta, baki a karkace tana nuna Maina. "Ka fita tunda bata son ganinka." Inji Ayrah, watsa mata kallon banza yayi ya nufi inda take ta zauna yana sunkuyar da kanshi kasa. "Sannu ya kika ji da jikin?" "Ka fita!" Ta fada da kyar. "Malik ka ce ya fita Mother bata son ganinshi." "Mai zai hana ki fitar da shi tunda kina da lafiya da karfi!" Inji Abraham, ita wallahi tsoron dan jagaliyan nan take. Don haka tayi shiru tana son tayi kukan munafunci. "Yanzu me za ayi mata?" "Me kuwa da ya wuce a kaita asibiti!" "Ai ciwon ba na asibiti ba ne, akwai masu magani zasu zo yanzu!" Suna zaune Falwa da Tirsila suka iso, akayi ta abu daya daga karshe aka cimma lallai Maina ya sake Layla idan ba haka ba, Queen zata tabbata a nad'e. "Babu wani mafita ne? Sai wannan." Inji Abu Ammar, "ranka ya dade wazir wannan shine mafitar." "Muhammad!" "Allah ya bata lafiya, amma ko mutuwa zata yi ba zan sake matata ba!" Ya fada yana me nufar waje. "Wannan ma renin hankali ne taya za ace sai ya sake matar shi zata samu lafiya Allah ta kyauta!"inji Salahudeen, "Ni abin haushi na rasa me yarinyar ta tsare musu kowa damuwarshi ya sake ta mtseew!" Inji Abraham. A hankali aka fara watsewa a dakin ya rage Malik da Ummimi da Abu Ammar,ga Ayrah da tayi bake-bake. "Allah ya baki lafiya Mother!" Inji Ummimi, ta bar dakin. Auta shima da tsarin bai mishi ba, ya fita yana fa in Allah ya sawwaka. A hankali aka watse a dakin. Sai Ayrah itama daga karshe ta fece. Falwa da Tirsila sun yi sunyi aljana Shuki ta bar jikin Queen Hamidah Amma fir taki ta ce musu. "Ina barinta mutuwa xan yi umarnin Uwargijiya Tal ce." Haka suka yi ta fama har tsawon wunin ranar kafin Layla ta samu damar zuwa gaida ta. Tun daga parlour kayan dakin da bangaren yake wani girgiza, har ta shiga cikin dakin kafin ta nime wuri ta zauna kujeran dakin Queen Hamidah sun kawo kansu, zama tayi tare da murmushi. Kujeran ya tashi da ita sama. "Lokacinki ya fara sona na miki kwaf daya amma sai na fahimci ba zaki san yadda ake ji ba, na fison kiyi ta rokona mutuwa ina kauce miki. Tirsila!" Ya fadi sunan a izgilance. Nuna mata yatsa tayi sai ga wani dark black hayaki ya nad'e wuyar Tirsila. Yayi sama da ita, "Nace ki gudu ko? Na ce ko gudu fa kiyi ta gudu kada ki tsaya domin bana son na ga mutuwarki na fison a zo min da lamarin yadda kika mutu a wulakance!" Ta juya ga Falwa da yake kokarin gudu, ya nad'e shi sama, tayi ta gana musu azaba da wajigasu, tana yi tana kyalkyalwa da dariya, saboda ba karamin nishadi take ji ba, Maina a bangaren Ummimi ya shigo ya samu bata nan, duk inda yake tsammanin ganinta bata wurin tuna incident din da ya faru yau yasa shi falfalawa da gudu yana me zubda abin hannunshi lokacin da ya isa ya samu tana ta juya gadon Queen Hamidah ne a iska sai ihu suke amma babu me jinsu. "Aisha!" Ya daka mata tsawa, juyawa tayi ta kalle shi kafin ya kwashe da dariya. "Zauna ga kujera kaima just have fun!" Ta cigaba da da juya su son ranta. Tirsila sau uku tana yunkurin guduwa Layla tana kamata. A karshe dai dole ta hakura da ukubar Layla. "Nace ki kyale su!" "Wannan kuma ba huruminka ba ne Sultan dina!" "Layla!" "An iya albarkantansu da Ni'imata kana da U ubata!" Ta fyad'a Falwa da bango ta ce mishi. "B'ace min!" Bata rufe baki ba ya b'ace sannan ta kalli Tirsila ta ce mata.."Kada na kara ganinki nan! Wuce!" Itama b'acewa tayi. A hankali ta sauke gadon Hamidah ta nufe ta. "Bafa abin ya kare bane, kin ci darajar Sultan dina ne!" Ta daki gadon sai da yayi wani irin juyi sai bakwai kafin Queen Hamidah ta mike zubur. "Maina kana ganinta matsafiya ce." "Eh mana na sani, matsafiya ce sai aka yi yaya?" Ya tambaye ta a hasale kafin ya cigaba da cewa. "Kada ki sake ki fusata ni muje!" Ya riko hannun Layla. Kallonshi kawai Layla take da dukkan Mamakinta. "Me yasa baka min fada ba?" "Har marinki zan yi idan kika cigaba da min rashin kirki." Ya fada yana tsare ta da idanu. Tura baki tayi tana fa in. "Tow kayi hakuri! Ba zan kuma ba!" "Tow meye ribar kayi laifi ka bada hakuri? Gashi nan kin kara bude sabon rigimar da ban san yadda zan dakatar da shi ba, wallahi baki jin magana." "Kayi hakuri ba zan kuma ba!" "Shi kenan!" Ya janyo ta yana me fa in. "Bana son fada ko tashin hankali, ni ba a cikin masarautar nan na rayu ba, na rayu ne a wurin Sultanah dilsha khatoon, kin ga ai basu da tashin hankali please ayi hakuri da rayuwa. Ina sonki sosai ina son kowa nawa amma kada ki ce zaki rama abinda aka miki!" Ya gaskiyar shi yake fa a, don haka ta saka hankali tana jin shi. Bayansu kwanaki al'amarin kamar ya wuce, amma ina kasa kasa Tirsila suke takalar Layla da tashin hankalin da ya wuce saninsu. Wata ranar Laraba da dare, haka kawai Queen Hamidah ta turo a kira Layla bayan sun tare a gidansu. Maina baya gida. Aliyyah tana parlour tana jin wurin Layla aka zo ta bar parlour. Haka Layla ta shirya a daren wurin karfe takwas da wani abu, tun kafin ta isa bangaren Queen Hamidah aka dauke wuta a dukkan masarautar baki aya. Haka ta cigaba da tafiya har ta isa corridon da zai kai ka parlour Hamidah kawai ta ga wasu irin halittu kwance suka ganinta suka suna gurnani. "Ku B'ace!" Ta fada tare da wucewa, haka suka b'ace tun kafin ta isa cikin parlour ta tafa hannunta sai ga wani irin haske light blue ta d'ago kai tana kallonsu. "Da alamu kashedin da nayi bai ishe ku ba, shine kuka gayyato ni." Ta fada tana murmushin mugunta. "Tirsila kiyi min rawan kwad'o kai kuma ka kwanta kayi rawan alade a cikin tabu, ke kam Hamidah kike, ki fita kiyi ta zaga masarautar nan a guje tare da kukan jaki domin bana son nayi muku yadda kowa zai fahimci ainihin abinda ya faru na fison kiyi haka tuburan. Kafin na san yadda zan yi dake sai da safenku kuyi idan gari yayi haske ku sake sabon shiri. " daga haka ta barsu nan suka fara aikin da basu san lokacin bari ba, ke Queen Hamidah da ta bazama a guje..... Gani nan biyo ki ```ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI ALLAH YA BADA LADA, NA GODE (GAMU SU BUKATAR SHIGA WAIT-LIST FAKA-FAKA OOOO 500N ne a tab'a ni ta wannan number 08130269641 )``` [9/24, 10:06 AM] Ramlat Manga Abdulrahman: LAST EMPRESS Mai_Dambu ____________62 Koda Aliyyah ta koma daki, kiran Maina tayi cikin sanyin murya ta ce mishi. "Papa kasan da fitar Layla ne?" "Ban gane ba?" Ya jifa mata tambayar shima. "Yanzu na ga tafita kuma bata gaya min ga inda zata ba, sai dai naji tana fa in iftaz ko oho!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Ok gani nan ma a parlour Ummimi zan zo!" Kashe wayar tayi tana murmushin mugunta, dole ki fita min a gida, daga haka ta koma parlour ta zauna. Bai ko cika minti biyar ba ya shigo gidan ya zuba mata idanun, kafin ya ce mata. "Har yanzu bata dawo ba?" "Eh tow ban sani ba dake na shiga na duba Yara, ko ta dawo..!" Bude kofar da aka yi yasa shi juywa yana kallonta. "Sultan dina!" Kura mata idanu yayi kafin ya ce . "Daga ina kike?" Juyawa tayi cikin kara maida kanta yarinya ta ce mishi. "Baby kwadayi nake ji, na fita niman soyayyen kifi fa!" Kallonta yayi cikin lullubi. "Ina kifin?" Ciro ledar tayi cikin lullubin ta nuna mishi. "Me yasa baki gaya min na kawo miki ba?" Ya kuma tambayarta yana kai hannu ya amshi ledar yaji da zafinsa sosai. Bubuga kafa tayi hatta kirjinta da suka fara girma sai da suka girgiza, tuni ya dauke wuta. "Tow ni taya xan iya kiranka bayan kai ma naka uzurinka fa, ai bai dace na kiraka na ce ka kawo min kifi ba, please bani kifina zanci da noodle ne!" Ta fauce tare da zurawa da gudu. "Layla be careful, ba ke daya ba ce." "Tow me kayan dadina mu nawa ne?" Ta fa a tana dariya, dafe goshinsa yayi yarinyar nan mahaukaciya ce. Ran Aliyyah yayi mugun b'aci. Mikewa tayi ta koma bangarenta. Shima bangarensa ya wuce. Yau girkin Aliyyah ne, kuma baya son yayi wani da zai janyo rigima shi, abun da yake damunshi yadda tasa lallai sai dai yayi kwana aya aya. Sannan ranar girkin Layla tayi ta niman rigima kenan, yasan idan yayi mata magana zata ce ya nuna mata yafi kaunar Layla gara ta mutu ya samu damar son Layla. Haka ya sa shi kiyaye duk abin da zai saka shi rigima da dukkansu biyu. Kiran wayarta yayi amma taki dauka, yana daga cikin abin da yake mishi zafi. Tura mata sako yayi. *Maybe kin manta da hakkina ne ko? Idan kika wuce minti uku zan tafi inda